
Duk duniya bani da aboki sama da mukhtar, he is my best friend, yasan komai nawa nima nasan sirrin sa, duk inda zama tare muke zuwa ko kaya kala d’aya muke sawa, komai namu tare sai ya zama na kamar shine Hassan d’in nawa ba Abraham ba, muka ware Abraham gefe babu ruwanmu dashi daga ni sai aboki na Mukhtar muke sabgar mu,babu yadda Abba da Ammi basuyi dan ganin rayuwar Abraham ta gyaru ba amma ina yayi nisa, iyayen mu sun sha kukan bak’in cikin Abraham amma a banza dan ko a kansa, duk abinda Abraham yakeyi su Abba basu tab’a kyamar sa ba, basu tab’a nuna masa wasu alamo ba, sai ma jan sa da suke yi a jikinsu, kozai gyaru, ganin mun girman mun gama karatun mu mun zama cikakkun mutane ne yasa Abba da Ammi suka matsa mana akan maganar aure, kowa ya fara kame-kame dan daga ni har Mukhtar babu mai budurwa dan bama mu tab’a tsayar da mace ba balle soyayya, shiko Abraham babu ma mai saka shi a lissafi.
Abba ya samarwa Mukhtar aiki a federal government, shiko Abraham Abba niyya yayi ya gina masa asibiti nashi na kansa, ganin rayuwar da ya zab’a yasa shi yi masa banza, haka ganin Business na karanta yasa Abba mik’a min gaba d’aya ragamar kasuwancin sa tun daga nan gida Nigeria har zuwa na k’asashen waje, komai ya dawo hannuna, Abba ya mayar da sunan duk wani company sa da sunana da kuma signing d’ina haka ma duk wasu kadarorunsa da account dinsa na bank ya zama nawa, Abba ya mik’a komai gare ni, ya kuma sanarwa da Abraham cewa saboda shi ya kauce hanya, kak’i nutsuwa kasan ka girma ya sashi yin haka dan bazai mutu yabar duniyar daya sha wahala da gwagwaryar duniya wajen tara ta watse ba dan haka ya mik’awa Zaid komai, ya kuma k’ara da cewa duk ranar daya nutsu ya dawo dai-dai yabi hanya ta gaskiya shima zai raba komai da kansa ya bashi.
To fa! wannan abu ya shi ya lalata komai, shine mafarin komai, shi tarwatsa komai ya kuma yi sanadin faruwar duk abinda ya faru, ya rora wutar tsana da k’iyayyata a zuciyar Abraham, harta kai kwata-kwata baya son gani na, ya tsane ni ko magana nayi masa baya amsawa sosai ya fara tunanin hanyar da zaibi dan ganin ya kawar da ni…………
MOMYN ZARAH
[21/01, 04:13] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
21
Zaid kwance bisa makeken gadonsa mai kirar royal bed, yana tunanin ta inda zai fara neman matar aure don Abba ya matsa musu da maganar aure kusan kullum sai yayi musu maganar, shi gashi ko a cikin friends d’in su shi ba mai yawan magana bane, he is so silent & hand sum guy, dan Zaid yana matuk’ar kyau daga na fuska harna halitta, tunani yake amma ya rasa ta inda zai b’ullowa al’amarin, yana cikin wannan hali Mukhtar ya shigo d’akin d’auke da sallama.
Ganin Zaid baima san ya shigo ba balle ya amsa masa sallamar ba, ya sashi tsayawa a kansa yana k’are masa kallo yana murmushi , dan yasan tunanin me yake, a kusa dashi Mukhtar ya zauna amma har a lokacin bai ma san ya shigo ba, a hankali Mukhtar yasa hannu ya shiga jijjiga shi, aiko firgit ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, ya kalli Mukhtar fuskarsa cike da murmushi yace ” Friend yaushe ka shigo?
Dariya Mukhtar yayi yace ” tun d’azu mana, “kai haba amma ban san ka shigo ba, ” toya za’ayi kasan na shigo bayan ka tsunduma duniyar tunani, murmushi Zaid yayi a karo na biyu ya shafa kwantacciyar sumar kansa yace ” hmmmmm dan bai da san mai zai cewa Mukhtar ba, shima murmushi yayi dan yasan halin Zaid da muskilancin tsiya, ya kalle shi yace ” kaji Class mate d’in mu sun had’a party ko?
D’ago kansa yayi yana kallansa daga bisali kuma yace ” a’a ban sani ba wanne daga ciki?
” wad’anda mukayi karatun Mastrs dasu a Dubai, shiru Zaid yayi yana kallon Mukhtar, “ko bazaka je bane? cewar Mukhtar, ” eh to gani nan idan ina da time zanje wacce rana ce?
” this coming weekend ne, Saturday, ” ok zaka je? Zaid ya tambayi Mukhtar, murmushi Mukhtar yayi yace ” idan zaka je amma idan baka zuwa nima babu inda zani,” hmmmmm gadukkanin alamu dai kana son zuwa, ” eh mana ko ba komai ai a sada zumunci kuma ma ai munyi missing juna cewar Mukhtar, ” ok badamuwa Allah ya kaimu, “Amin Mukhtar yace yana mik’ewa kallonsa Zaid yayi yace ” sai ina kuma?
“Baka ji an kira sallah bane? ” banji ba wallahi ya fad’a yana duba agogon hannunsa, ganin lokaci yayi ne yasa shi saurin mik’ewa, yayi toilet, bayan sun idar da sallar direct cikin gida suka wuce a parlor suka samu Ammi zaune tana kallon Aljazira English, har k’asa suka duk’a suka gaida ita, fuskarta cike da fara’a ta amsa, kusa da ita suka zauna gaba d’aya, Mukhtar yace “Ammi da abinci kuwa?
Ban sani ba! kullum kuzo ku dame da neman abinci ance kuyi aure kunk’i sai kuzo ku rink’a cinye min abincin gida acici kawai ta fad’a tana dariya da sigar tsokana, dariya sukayi gaba d’ayan su Mukhtar ya langwab’ar da kai cikin shagwab’a yace ” kai Ammi idan bamu ci naki ba nawa kike son muci? “Na matan ku mana, ni fa lokaci na baku idan kuma ya cika ko gida na bazan bari ku rink’a shigo min ba, ni ban tab’a ganin yara irin ku ba kwata-kwata basa san maganar aure balle auren ma, “dariya suka kuma yi Zaid yace ” da Abban mu nan daya shigar mana a… “Aiko wannan karon bazan shigar muku ba bayan matata ni ma zanbi cewar Abba dake shigowa cikin parlor d’auke da fara’a Mukhtar yace ” kai Abba harda kai kuma yau? ” eh harda ni nazan yarda kullum a rink’a damarmin mata da maganar abinci ba ana zuwa ana hana ta baccin dare da hira murmushi Zaid yayi yace ” kyale su Friend idan muka tashi mu full tank zamuyi dan sai munyi 4 dariya Abba yayi yace ” idan kunji haushi kuyi 1000 yau ma.
Haka dai suka ci abincin cike da fara da barkwanci dan daga Abba har Ammi sun kasance mutane masu fara’a da wasa da dariya da iyalan su, suna cikin haka Abraham ya shigo da sallamarsa fuskarsa d’auke da murmushi ya nufi wajen Ammi da Abba, burki yaci dan ganin wad’anda yafi tsana a duniya take ya murtuke fuska ya had’e rai yadda kasan anyi masa sammacin mutuwa.
Cikin fara’a Abba yace ” yawwa babban d’a k’araso fuska ya k’ara b’atawa yace ” no Abba badamuwa bari naje waanka zanyi, murmushi Ammi tayi sannan tace ” haba d’ana zo kaci abinci kaji, murmushi yayi mata yace ” ok Ammi but not now, Abba ya kalli su Zaid yace ” baku ga Yayan ku bane? “Ai da muka ga kuna magana ne, a tare suka had’a baki Yaya ina wuni? ko kallan inda suke bayyi ba a ciki ya amsa da lafiya, hakan ma dan agaban idan su Abba ne, ya wuce abinsa, gaba d’aya suka bishi da ido ita ko Ammi ajiyar zuciya ta sauke tana mai matuk’ar bak’in cikin halin da Abraham yasa kansa, ganin gaba d’aya yanayin Ammi ya canja yasa Zaid da Mukhtar tare da Abba kwantar mata da hankali da bata hak’uri.
Abraham na shiga d’aki ya banko k’ofar d’akin, yana ta faman huci kamar maciji, kayan jikinsa ya cire ya shiga cilli da dasu, zama yayi a bakin gadinsa yana furzar da iskar bakinsa, da sauri ya mik’e ya d’auko sigarinsa ya hau busawa sai da yasha mai isarsa sannan ya shiga bathroom ya sakarwa kansa shower, yakai kusan 30 minutes sannan ya fito ya fad’a kan gadonsa yayi rigingine kansa yana kallon sama ya shiga tunanin ta inda zai b’ullowa Zaid, sai da ya b’ata lokaci sosai sannan ya samu mafita, mik’ewa yayi zaune yana murmushi gefen baki dan ya samu hanyar dazai k’ullawa Zaida GADAR ZARE.