GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ranar Saturday wajen k’arfe 8:00pm babban hall din kuma tsadadje cike yake da jama’a had’add’u ‘yan gayu kuma ‘yan book kai gani kasan naira ta zauna da gindinta a wajen, don kuwa ka gani kasan yaci ya tada da ita, yayinda duk jama’ar dake wajen maza da mata fuskokin su cike da fara’a da sanyayyan murmushi Zaid take tsaye ya hango wani abokinsa sosai da tunda suka gama karatu bai ganshi ba, shima abokin nasa idonsa ne suka sauka akan Zaid aiko cikin zumud’i fuskarsa d’auke da wadataccen murmushi ya nufo Zaid shiko Zaid tsayawa yayi yana kallonsa shima yana mayar masa da martanin murmushin suna gaf da had’uwa ne aka kashe wutar wajen.

Hankalin Zaid kwance ya k’arasa nufar abokin nasa ya rungume gam cike da farin ciki ” I miss you so much frien…… maganar tasace ta sark’e masa a mak’ogwaro sanda aka maido da wutar hall d’in, ya sandare a tsaye yana kallon yarinyar daya rungume a tunaninsa abokin nasa ne, sakinta yayi da sauri yayi baya durk’ushewa tayi a wajen d’an kwallin kanta ya fad’i gashin kanta daya sha gyara ya zubo mata a fuska ya rufe mata face, cikin b’acin rai ta mik’e tasa hannu ta kawar da gashin daya zubo mata, baki Zaid ya bud’e yace ” am sor…. kasa k’arasa maganar yayi sakamakon kyau da had’uwar yarinyar daya firgita shi, take nutsuwarsa ta d’auke ya k’ura mata ido baya ko kiftawa, itama cikin tsiwa ta bud’e baki tace “Would take your hand off, please, tana sauke idonta a kansa gabanta yayi mummunar fad’uwa, shida baima ma san har a lokacin hannunsa na kanta ta yayi saurin d’auke hannunsa amma idonsa na kanta fuskarta ba yabo ba fallasa tace ” what are you staring at?, never seen a girl before? ta fad’a tana barin wajen, murmushi Zaid yayi yabi bayanta da kallo yace “I have but not a girl who entered my heart, at first sight.

Duk inda yarinyar tayi idonsa yana kansa, ya kasa daina kallonta, tana sane dashi amma tayi kamar bana tasan tana yi ba, haka har aka gama taro, Mukhtar yace ” muje ko? ” kaje kawai ni ba yanzu zan tafi ba, cikin mamaki yace ” me zakayi, ina zaka biya? “kaje kawai zamu had’u a gida cewar Zaid yana barin wajen, da ido Mukhtar ya bishi kawai, duk yadda Zaid yaso yayi magana da yarinyar amma taki bashi dama, har taron ya watse, cike da matsanancin bak’in ciki yake tuk’in motar yayinda yake cizon d’an yatsansa, danja ce ta tsaida shi dole ya tsaya badan yaso ba, wasu samari ya gani cike da mota suna bin wata motar a guje, da gudu motar da ake bin ta bigi wani gani dake gefe ganin haka yasa samarin barin wajen a guje, da sauri Zaid ya fito ya nufi motar da k’arfi ya b’elle k’ofar motar, tsaywa yayi cak dan ganin yarinyar ce acikin motar amma ta suma, gabansa ne yayi muguwar fad’uwa, da sauri ya d’auke ta yasa a cikin motarsa yayi aaibiti da ita.

Bayan Doctor ya gama duba ta ya fito yana yiwa Zaid bayani “her blood pressure is low, but everything is okay otherwise, not a serious wound, I think she has lost consciousness because of fear, I have administered the injection she’ll be fine by morning, murmushi Zaid yayi yace thank you doctor, you are welcome Doctor ya fad’a yana barin wajen, a d’akin da aka kwantar da ita anan Zaid ya kwanta kan doguwar kujera, tun asuba daya farka yayi sallah bai koma bacci ba, zama yayi a kusa da ita ya k’ura mata ido yana ganin tsantsar kyau ya hankali yace ” da gani ba baushiya bace dan tafi kama da turawa, sai wajen 8:00am ta farka bakin ta d’auke da salati hannunta ta saka duka biyun ta dafe kanta da sauri Zaid ya nufe ta, a hankali ta tashi zaune ta fara ware idonta tana bin ko ina da kallo, idonta ne sauka akan Zaid da sauri ta k’ara zaro ido tana kallon sa tace “you agai?

Murmushi yayi hannunwasa had’e a k’irjinsa ” yes, yaci gaba da cewa ” can’t help it, you run into my life, without even knocking, murmushi tayi tace ” thanks for last night, ido ya k’ura mata, alama tayi masa da idon sa na wannan kallan fa a hankali ya shiga furta ” looking at you, I think the astrologer’s words might come true, cikin rashin fahimta yace ” astrologer? ” you see.. , yaci gaba da cewa ” in the last twelve hours, this is our third meeting, did some trait of catch your eye back at d party?

Murmushi tayi kawai tace ” i’ll leave now, ta fad’a tana saukowa daga kan gadon, a hankali ta fara takawa dan barin d’akin karaf taji yace ” strange! you vanish to meet again, & u meet only to vanish again, u may leave, but won’t u tell me whom I ought to thank, a hankali ta juyo tana fuskantarsa tace ” pardon me? ” I mean, who was dat person, who made u take 2 ur heels, if not 4 dat soul, neither would u hv collapsed, nt would I hv brought u here, & all my life, I would’ve felt sorry 4 nt asking ur name, b4 u vanish again, hurry up and tell me ur name, murmushi tayi dan ta fahimci ya zata bata jin hausa dan haka ta kalle tace ” sunana Fatima amma amfi kira na da TEEMAH, ido ya zaro yace ” kina jin hausa?

“Gashi kuwa na tabbatar maka, ni cikekkiyar bahaushiya ce, ni bani da wani yare sai hausa dan ban taso a gidan mu naga ana yin wani yare bayan hausa ba, murmushi yayi yace ” masha Allah, ni sunana Zaid Muhammad Bature, gabanta ne ya fad’i dan duk Nigeria baby wanda baisan Alhaji Bature ba, da sauri ta d’ago kai ta kalle shi tace ” kai d’an Alhaji Baturen dana sani ne?

Murmushi ya kuma yace ” when tym has come u know, babu yadda Zaid bayi ba yakai Teemah gida amma fir taki yarda, sai exchanging numbers da sukayi a junansu, Zaid na zuwa gida direct d’aki ya wuce, yana zuwa ya fad’a gado yana sakin murmushi yace ” nisa tazo kusa an kusa daina yi min gorin aure, Mukhtar dake toilet ya fito, idonsa ya sauke akan aminin nasa daya dad’e da fad’awa duniyar tunani kai ya girgiza ya jingina da bango yana kallonsa dan yasa tunanin dayake a hankali yace “haba Friend ka daina matsawa kanka akan maganar auren nan by God grace a beautiful and charming girl will walk into your life for ever, mik’ewa zaune Zaid yayi yana murmushi yace ” she already walk into my life, I pray to stay with me for ever, cikin mamaki Mukhtar yake kallansa alamar tambaya yayi masa da idon sa, Zaid yace ” yes I told you d true, hankali Mukhtar ya tako inda Zaid yake ya zauna a kusa dashi his face with smile yace ” are serious friend?

Dariya Zaid yayi har fafaren hak’oransa suka bayyana yace ” yes nan ya shiga bashi labarin Teemah, ” Alhamdulillah masha Allah, yau aboki na ya samu soulmate d’insa, toya take? “Kai dai bari ai duk yadda nake mafarkin samun mace Teemah ta wuce haka, yarinyar ta had’u fa, ” to ya ka gani a b’angaren tarbiyya d’a addininta? “Eh to ai bamu zauna ba balle na fahinci hakan, ” ok badamuwa friend in sha yadda ka sameta a zahiri haka zaka sameta a bad’iri, ” Amin ya Allah, ni dai na kusa na wuce gorin Ammi, na kusa zama mai gida gaba kad’an kuma na zama Dady, wasu ko oho.

Duka Mukhtar yakai masa yana cewa ” nima ai ba haka zan zauna ba, kai zan ma k’ok’ari na samu Matar aure dan bazan bari ka riga ba, dan idan na bari ka rigani na shiga uku, ” oho dai gwara ma dai mutum yayi zuciya ya d’au himma danbazan rink’a barin k’atti suna shigar min gida pillow ya d’auka ya jefa mishi “au nine ma k’aton banzan, shima Zaid pillow ya jefa masa yana dariya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button