GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Shoki goga Abraham duk ya samu kansa da neman hanyar da zai kawai dai Zaid da Mukhtar babban burinsa a duniya bai wuce yaga Zaid da Mukhtar basa raye ba safa da marma ya shiga yi a d’akin hannunsa sak’ale a bayan say yana ta sak’a da warwara yayi nisa cikin tunanin hanyar da zaibi dan ganin ya had’a musu GADDAR ZARE, makeken gadonsa ya fad’a yana dariyar mugun dan samun mafita…….

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:13] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

22

Sannu a hankali wata irin muguwar shak’uwa ta rink’a shiga tsakanin Teemah da Zaid, sosai suka saba ta saki jiki dashi, ta yadda kowannen su baya jin dad’i idan baya tare da junansu, har yawo suke zuwa tare, sune shan ice cream, kallon films zuwa garden ko park, sosai suka shak’u da junan su fiye da tunanin mai karatu, shi dai ya kasa fitowa ya fadawaTeemah yana santa.

Zaid kwance akan gado sai juyi yake yana waya da Teemah hankali kwance, Mukhtar yana gefe ya zuba masa ido yana kallon ikon Allah har Zaid ya gama wayar, a hankali Mukhtar ya kalle shi yace ” why not bazaka fito ka sanar da ita kana santa ba? “shiru Zaid yayi ya kasa cewa komai, “kasan dai hausawa na cewa abari ya huce shike kawo rabon wani ko? murmushi Zaid yayi yace ” babu ma rabon wani anan sai nawa, “murmushi Mukhtar yayi yace ” Allah yasa friend koni ina fatan haka, amma wanne aiki take? “she is jobless cewar Zaid “ok to yanzu wanne plans ne dakai akanta?

“I employed her as my secretary, “what! yaushe? “gobe ma zan tabbatar da ita a office, sosai Mukhtar yayi murna da aikin da Zaid ya bawa Teemah dan koba komai yayi taimako, washe gari around 9:00am Zaid ya gabatar da Teemah a company dinmu a matsayin secretary d’insa, a hankali ya dafa kafad’ar Mukhtar yace ” and dis is my dear friend and our company’s legal advisor Mukhtar, he is my best friend, murmushi Teemah da Mukhtar sukayi ma junansu tace ” sannu abokin mu “yawwa amaryar mu, tun daga ranar Teemah ta fara aiki a company din Zaid, a office d’in ta same shi tana yi masa maganar akan office da kasuwanci sanye take da doguwar riyar materials mai shegen kyau ya kuma karb’i jikinta d’as, tana zaune akan kujerar dake fuskantar shi kanta yana kallon system ta shiga yi mishi bayani.

” Thought our marketing plan, we are planning toto set up a central customer service cell, to help support investor who sell their products thought us, we will also have a customer service support website, ok and ta d’ago taga mai yake dan jin baice komai ba, duk maganar da take Zaid bai fahimtar komai dan gaba d’aya bai ma san inda kansa yake ba, ya zabga tagumi hannu biyu ya k’ura mata ido sai sakin murmushi yake, kallansa tayi cike da mamaki tace ” sir! sir!! shiru bai ma san tana yi ba idonsa na kanta ya kafe ta dasu, table d’in dake gabansu ta d’an buga a hankali ta kuma cewa ” sir firgigit Zaid yayi ya dawo daga duniyar tunani ya sauke ajiyar zuciya da k’arfi ya fara kame-kame ” uhn ummm marketing plans d estimated demand 4 higher paper…

Kanta da sunkuyar k’asa tana kanne dariyar dake shirin kufce mata, a hankali ta mik’e tace ” mayi magana latter bata jira amsar saba tafita, yabi bayanta da kallo, bayan antashi daga office wajen 8:00pm ya shigo office d’inta ya iske ta zaune sai faman aiki take kallon ta yayi yace “you still there? kai ta d’ago ta kalle shi tana murmushi dan bama tasan ya shigo ba tace ” you haven’t either sir, murmushi yayi yace ” for me home & office mean d same thing, ido kawai ta zuba masa bata ce komai ba yaci gaba ” a home is where someone wait 4 u, murmushi tayi tace ” I don’t hv anyone waiting 4 me either, sir, murmushi ya kuma yi mata yace ” tashi mu tafi ko? ba musu ta mik’e suka jera.

A gida kowa Zaid zaune gaban Mukhtar suna magana akan Teemah Zaid yace ” I decided to spend all m life with Teemah & I wanted 2 start dis new life as soon as possible, murmushi Mukhtar yayi yace ” gaskiya to ya kamata kaje ka tunkare ta ka fad’a mata kana santa kawai ka cire tsoro da fargabar komai, nan dai Mukhtar yayi ta k’ara masa k’arfin gwiwa, harya yarda akan gobe zai sanar da ita.

Washe gari ta kasance ranar Saturday dan haka babu aiki kasancewar duk ranar weekend Zaid da Teemah suna tare a wajejen shak’atawa, yau ma haka ce ta kasance, zaune suke a wani garden mai kyau sai kamshen flowers ke tashi, kallonta Zaid yayi a hankali ya kira sunanta “Teemah yanayin yadda ya kira sunan nata da wata irin kasalalliyar murya kuma ya kafe ta da ido ne yasa ta kasa amsawa sai ido kawai data zuba masa, sun kai wajen 30 minutes a haka amma ya kasa cewa komai kuma ya kasa d’auke idonsa daga kanta itace data gaji da kallon ta sunkuyar da kanta k’asa.

Jikinta ne ya kuma bata ana kallonta dan haka ta kuma k’ara d’ago kai ta kalle shi aiko suka had’a ido murmushi suka sakarwa juna a lokaci d’aya a hankali Teemah tace ” you’ve been practicing about 4 d last 1:30 hrs , will u say something now? ” what do I say Teemah? 4 d first tym I’ve fallen in love, 4 d first tym I’m meeting someone lyk dis, 4 d first tym I’ve done shopping 4 someone & sai kuma yayi shiru ya kuma sauke ajiyar zuciya, kallansa tayi cikin rashin fahimta tace ” what!? what are you talking, murmushi ya kuma yace ” 4d first time I set my eyes on you I fall in love with you Teemah you come into my life and make it meaningful ” kaga ni fa ban gane abinda kake nufi ba dan haka I don’t follow a thing , stay here i may go ta fad’a tana k’ok’arin barin wurin mik’ewa da sauri Zaid yayi ya rik’ota dan yasan yau ne kawai damarsa a hankali shima ya mik’e tsaye ya fuskance ta yadda kowanne su yana iya jiyo numfashin juna yayi gaf da ita sosai yace ” I want 2 say something Teemah, I’m businessman as u already know , honestly Teemah I’m in love with u, pls accept my loving hands Teemah, ya fada cikin wata irin kasalalliyar muryar.

K’ara matso ta yayi sosai ya k’ura mata ido, itama shi take kallo dan haka idonsu cikin na juna yake kallanta fuskarsa d’auke da kwantaccen murmushi yace ” My heart, my life, my everything I gv u, in fact Teemah you’re my everything !! idonta ta lumshe tana murmushi dan ta dad’e da kamuwa da mugun son Zaid, a hankali ta bud’e idonta ta sauke su akan na Zaid, kallansa kawai take ta kasa da furta kalma d’aya, ya kuma cewa ” will u belong 2 me in dis lifetime & all d lifetime? Murmushi kawai Teemah keyi ta kasa cewa komai, hakan ne ya tabbatarwa da Zaid ya karb’u

Sannu a hankali soyayya mai k’arfi ta rink’a shiga tsakanin Teemah da Zaid, kusan kullum suna tare da dare kuwa kusan kwana suke suna waya, sosai Teemah ta gama shiga jikin Zaid haka ma Zaid ya gama mamaye every part na Teemah, amma tunda Zaid yake bai tab’a zuwa gidan su Teemah ba, yayi juyin duniya amma tak’i kai shi koda unguwar su balle gidan su, yauma kamar kullum ya gama shirin tsaf dan sunyi zasu had’u a wani park, yana sauri ya shiga b’angaren su Ammi a zaune ya iske Ammi da Abba sai Mukhtar dake zaune gefe, har k’asa ya durk’usa ya gaida iyayen nasa, da fara’a suka amsa masa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button