
Ganin yadda yake ta faman sauri da rawar jiki yasa Ammi mamaki, ” kai kuma ina zaka haka naga sai rawar jiki kake, kai ya shafa sannan yace ” meeting ne dani, dariya Mukhtar ya tuntsure da ita har yana k’ok’arin kwarewa gaba d’aya suka kalli Mukhtar, Ammi tace ” kai lafiyar ka kuwa?
Dariya yayi yace ” bakomai Ammi yakai dubansa kan Zaid dake ta faman raba idanu dan yasan abinda Mukhtar ke shirin yi masa, kuma kallon Zaid Ammi tayi tace ” ga abinci can kaci sannan ka fita, kai ya langwab’ar yace ” please Ammi ana jira na, ban san na b’ata musu lokaci idan na dawo sai naci, kallonsa Abba dake gefe yayi yace ” wanne meeting ne dakai around 5:00pm yanzu ya fad’a yana kallon agogon hannunsa, shiru Zaid yayi ya rasa abincewa dariya Mukhtar ya kuma yi yace ” a dai rink’a fad’ar gaskiya.
Abba da Ammi suka kalli Mukhtar suka ce “to da magana kenan? da sauri Zaid ya kalli Mukhtar ya k’ifta masa ido ya girgiza masa alamar karya fad’a aiko karaf akan idon Abba, dariya yayi yace ” meye kake k’ifta masa ido, ” Abba ba ido na k’ifta masa ba wani abu ne ya fad’a min a idon, murmushi Mukhtar yayi yace ” kyale shi Abba ba ido zai kanne min ba idan ma hanci ne sai na fad’i, aiko da gudu Zaid ya nufe shi, shima Mukhtar mik’ewa yayi aiko suka shiga zaga parlor’n, Abba da Ammi dai sun kasa fahimtar komai da ido kawai suke binsu, cikin zafin nama Zaid ya rik’o Mukhtar yasa duka hannunsa ya rufe masa baki, yayi ta k’ok’arin kwacewa amma ya kasa.
Cikin dabara Mukhtar ya samu ya gantsarawa Zaid cizo a hannun aiko da sauri ya sake shi yana yarfa hannun, da sauri Mukhtar yace ” zance zashi, da sauri Ammi da Abba suka had’a baki “zance!!!? “Eh wallahi Ammi ai an samo muku suruka, sunanta Fatima amma ana kiranta da Teemah, zama Zaid yayi akan kujerar yasa hannunsa duka biyun ya rufe fuakarsa alamar jin kunya, “oh! wato shine kake ta rawar jiki ko, kuma ko ka bamu labarin ta, Ammi ta fad’a tana zama kusa dashi, Abba kusa dashi ya zauna ya dafa kafad’arsa yace ” bamu labarin ta, hannu Ammi tasa ta cire masa hannuwansa daya rufe fuskarsa yace ” who is she?
Murmushi yayi yana mik’ewa yace ” she is beautiful, intelligent, loving, caring & she had walked into my life, she had everything, she’s just kinda different Ammi,I really love her, ” uhnnn Zaid manyan gari duk wannan bayani haka, so who is her parent cewar Abba, fuskarsa ya langwab’e da alamar tausayi yace ” I think they are poor, but I don’t know, ” u wat, u mean u don’t knew her parents, ” yes Ammi, ” ok to ina kuke zance?
Shiru yayi kamar bazaiyi magana sai yace ” babu yadda banyi da ita akan ta kaini gidan su ba amma tak’i, kullum sai dai mu rink’a had’uwa a park “what! Ammi tace a fusace irin wannan matar kake shirin aure irin wannan uwar zaka zab’awa yaranka? to bari kaji wannan shirmen badai a family mu ba, wannan ai zance banza ne daga ji wannan ba ‘yar mutunci bace “no haba Ammi meyasa zaki yankewa ‘yar mutane hukunci tun kafin ki ganta, kamata yayi kisa shi ya kawo miki kiga tarbiyya da nutsuwa sannan ki yanke hukunci, cewar Abba a hankali Zaid ya sauke ajiyar zuciya dan ji yayi kamar Ammi na watsa masa ruwan zafi, a hankali Abba ya kalli Zaid da hankalinsa yakai k’ololuwar tashi yace ” gobe ka kawu ta, kanshi a k’asa yace ” ok Abba in sha Allah, tashi kaje, a hankali ya mik’e ya kalli Ammi yayi murmushi yace ” Ammi zan tafi ya fad’a yana yi mata kiss a kumatu murmushi tayi tace ” ka gaida ta wani irin sanyin dad’i yaji ya ratsa shi dukda dama yasan Ammi mai sauk’i hali ce, ” ok zata ji, ya juya inda Mukhtar ke tsaye yace ” adayyi zuciya dan ni na kusa wuce gorin Ammi ya fad’a sigar tsokana, dariya shima yayi yace ” oho dai ka sani ma kona riga ka angoncewar “ah ai banga alamar hakan ba ya fad’a yana k’ok’arin barin parlor ” ok shine kokace nazo na raka ka?
“Ka raka ni ina, tab sha zamanka bana gayya, Teemah tafi 1hr zaune a park tana jiran Zaid, dan haka koda yazo bak’aramin rarrashi ba kafin ya shawo kanta asha love, nan ya shayda mata maganar iyayensa suna san ganin ta dan haka ta shirya gobe zai kaita.
Washe gari wajen 5:00pm Zaid yakai Teemah gidan su, a falo ya ajiye ta yace ” ina zuwa tunda Teemah ta shigo gidan su Zaid kanta ya buga dan ganin girma da kuma tsaruwar gidan, aranta tace “Allah kad’ai yasan mak’udan kud’in da aka kashe wajen tsara gidan, tana cikin wannan tunanin taji Zaid yace ” Teemah meet my parents, ya fad’a yana nuna mata Ammi da Abba, a hankali ta d’ago kai ta kalli Ammi da Abba ganin mutumin da take gani a gidajen TV tsaya a gabanta yasa k’irjinta bugawa da k’arfi, murmushi tayi tana gaida Ammi da Abba tana daga zaunen akan kujera faran-faran Ammi ta amsa bata nuna mata alamar komai ba, ta karb’e ta hannu bibbiyu, Ammi ta umarci ‘yan aiki dasu kawo mata kayan motsa baki aiko aka cika mata gabanta da kayan ciye-ciye fal, wani abun ma bata tab’a ganin sa a rayuwarta ba, babu kunyar komai cike da wayewa taci ta k’oshi ta cika cikinta fam, a hankali Ammi ta kalli Zaid da Abba, shi kanshi Zaid sai da yaji baiji dad’in abinda Teemah tayi ba, murmushi Ammi tayi tace ” ya sunanki? kai tsaye tace ” Teemah, “ok Teemah a wacce unguwa kike sannan suwaye iyayen ki? da k’arfi gaban Teemah ya buga zuciyar ta ta shiga lugude gami da harbawa, kafin ta gama nutsuwa taji Abba yace ” ke ‘yar asalin wanne gari ce?
Kasa magana tayi ta shiga in’ina sake kallon Zaid da Abba Ammi ta kuma a karo na biyu tayi murmushi, cikin rawar murya Teemah tace ” ni mareniyya ce ni kai na ban san iyaye na ko garin ba, a gidan marayu na taso, ta fad’a tana share kwallar dake zubo mata, take tausayin Teemah ya cika zuciyar Zaid da Abba amma Ammi murmushi tayi irin nasu na manya tace ” ikon Allah wanne gidan marayu kenan, cikin rawar baki Teemah ta fad’a musu gidan marayun data taso, daga Abba har Ammi sai da gaban su ya fad’i dan gidan marayun da aka d’auko Abraham ne, cikin rawar baki Abba yace ” ok badamuwa, zamu bincika,sai bayan magrib Teemah tabar gidan su Zaid cike da kayayyaki da kud’i da Ammi da Abba suka bata.
A motar Zaid da Teemah zaune babu mai yiwa wani magana kowa da abinda yake sak’awa a ransa, ajiyar zuciya Zaid ya sauke a hankali ya kalli Teemah yace ” mai yasa baki tab’a gayamin ke marainiyya bace, a hankali tasa hannu tana goge hawayen fuskarta tace ” ina gudun karna rasa kane, ina mugun sanka Zaid idan ka barni wallahi mutuwa zanyi murmushi Zaid yayi yace ” ke! ya kike irin wannan maganar ne, waya ce miki ni zan iya rabuwa dake? “Ni dai please ta fad’a tana rik’o hannunsa gam cikin nata yayin da hawaye ke zubo mata, wani mugun shocking Zaid yaji kasancewar yau ne rana ta farko da mace ta tab’a shi, taci gaba da cewa ” dan naga kamar iyayenka bazasu karb’e ni ba, ” saboda ya tambaye ta? “alama na gani kuma kaga ku masu arzik…… hannu ya d’aga mata yace ” ni iyaye na ba haka suke ba, ba irin masu kud’in yanzu bane dan suna da fahimta da kuma adalci, abinda kikayi ne kawai bai kamata ba, ” kasan ni ban san komai akan rayuwa ba, dan ban san gatan iyaye ba dole wani abun sai ana yin min uziri tunda kaga ba’a hannun kiyaye na ta taso ba basu suka yi min tarbiyya ba, jikin Zaid yayi sanyi, a hankali ya shiga kwantar mata da hankali, harya kaita ya ajiye.