
Zaid yana komawa gida Ammi ta tada falli bata son Teemah wai ta waye da yawa kuma bata da tarbiyya, kayi ta lallashen amma fir tak’i babu yadda Mukhtar da Abba da Zaid basu ba amma ta rufe idonta tace ” ya daina nemo wata amma banda Teemah akayi ta abu kusan wata d’aya amma tak’i yarda Zaid duk ya rame ya shiga damuwa da takura amma Ammi ko a kanta da ta kafe ta k’ek’ashe k’asa akan ita bata son Teemah, dakyar Abba ya shawo kanta ta yarda akan tana da sharad’i, Abba yace ” bakomai sunji sun yarda, da safe Abba ya kira Mukhtar da Zaid duk suka zauna bayan sun gaida iyayen nasu, a hankali Ammi ta k’arewa Zaid kallo taga mugun ramar da yayi take tausayinsa ya shige ta, a hankali ta kalle shi ta kira sunansa “Zaid! cikin nutsuwa ya d’ago kai yana kallon ta had’i da amsawa, “na yarda ka auri yarinyar nan Teem…. ai kafin ta k’arasa ya nufe ta ya rungume ta “thank you, Ammi you so much, a hankali ta zame jikinta ta b’ata fuska tace bisa sharad’in d’aya gaban Zaid ne yayi muguwar fad’uwa k’irjinsa ya shiga bugawa dan yasan tunda Ammi ta had’e rai maganar babba ce, maganar sa na cracking yace ” wanne irin sharad’i Ammi………….!
MOMYN ZARAH
[21/01, 04:13] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
23
Fuska ta k’ara b’atawa dan ya d’au maganar ta da mahimmanci tace ” so nake ka auri mata biyu a lokaci d’aya a firgice Zaid ya mik’e yace ” what Ammi? Mukhtar ma a firgice ya d’ago kai yana duban Ammi wacce tayi kamar ba itace tayi maganar ba taci gaba ” zan barka ne ka auri zab’in ranka matuk’ar nima zaka karb’i nawa zab’in idan kuwa ba haka ba sai dai ka hak’ura da Teemah, a hankali ya durk’usa a gabanta ya shiga bata hak’uri akan tayi kyale shi, shi bashi da burin mata biyu amma sam Ammi tak’i, daga k’arshe ma mik’ewa tayi tace ” idan ka shirya kayi min magana, da sauri ya rik’o k’afafunta dan ganin yana niyyar yin biyu babu, yace ” na yarda Ammi, amma ban san inda zan k’ara nemo wata ba wannan d’in ma da kyar na samo ta, ” ok to shikenan ni zan samo maka, ” to please Ammi ki bari na fara auren Teemah tukunna, in yaso bayan wata uku sai na auri zab’in naki.
” ko kuma ka auran zab’in nawa in yaso daga baya saika auri naka zab’in, “please Amm…. da sauri ta d’aga masa hannunta tace” nifa ba matsa maka nayi ba, zab’i na baka, ganin damar kane kabi zab’in ko kuma ka hak’ura, shiru Zaid yayi kansa a sunkuye ya kasa cewa komai, ganin haka yasa Abba cewa tashi kaje kayi tunani tukunna, idan ka gama shawara sai ka dawo, a hankali ya d’ago kai yana kallon iyayen nasa, cikin sanyin murya yace ” bakomai Abba na amince, murmushi Abban yayi yace ” Masha Allah ka sanar da ita nan da wata d’aya za’a d’aura muku auren dukkan ku, kai ya k’ara risinawa yace ” nagode, ” tashi kuje Allah yayi muku albarka, ” Amin ya Allah suka ce suna barin parlor’n.
Zaid na shiga ya fad’a gado ya rufe idonsa ya fara tunanin ta ina zai fara sanarwa da Teemah wannan maganar, a hanlaki Mukhtar ya dafa shi ” friend kayi hak’uri kaji, in sha komai zaizo mana da sauki, ni dai ina mai baka shawara da kayiwa Ammi da Abba biyya, a hankali Zaid ya bud’e idonsa had’i da sauke ajiyar zuciya, ” to yanzu Friend ta ina zan fara tunkarar Teemah da wannan maganar?
“Koma dai yaya ne ya zama dole ka sanar da ita, idan kuma har soyayyar da take maka gaskiya ne zata amince maka ta kuma k’ara maka k’arfin gwiwa akan kayiwa iyayenka biyayya, “haka ne in sha zan sanar da ita yau din nan ma, “ok Allah ya taimaka, kaga nima idan naga Ammi ta iya zab’e sai na mak’ale ta zab’o min ya fad’a yana dariya, ganin Mukhtar na niyyar yi masa shak’iyanci ne yasa shi yi masa banza.
Wajen 8:30pm yayiwa Teemah yace ” su had’u inda suka saba had’uwa ba musu tace gatanan dan taji yanayin muryarsa cike take da damuwa, k’arfe 8:30pm acan tayi mata, bata fi 5mnt ba saiga shi, yanayin yadda ta ganshi ne yasa gabanta dukan uku-uku, a hankali tace ” lafiya kuwa sweetheart duk na ganka a birkice? Murmushin yake yayi mata yayinda da acan k’ark’ashen zuciyarsa tsoro da fargaba suka dirar masa, ido ya k’ura na mata na wani d’an lokaci sannan yace” kina so na? cikin rashin fahimta tace ” me, wannan wacce irin magana ce kake yi ne? bangane ba fa, ” tambayar ki kawai yi, so just answer me, ” ok ina jinka.
“Kina so na? ” eh, “zaki iya aure a wanne irin nanayi? shiru tad’anyi “Zaid why all dis? “I said just answer me yes or no, cikin sanyin jiki tace “yes dear, “Alhamdulillah ya fad’a yana sauke ajiyar zuciya, “ok please ki taya ni yiwa iyaye na biyayya please my life ya fad’a yana rik’o duka hannuwanta cikin nashi, muryarta na cracking tace ” what is going on dear? a hankali ya sanar da ita abinda ke faruwa amma bai fito fili ya sanar da ita Ammi bata santa ba.
Cikin sanyin jiki da rawar murya tace ” bakomai dear Allah ya nuna mana lokacin Ammi da Abba iyayen mu ne nasan bazasu tab’a had’a mu da abinda zai cutar damu ba balle har su aikata mana abu mara kyau ba, Allah ya bamu ikon yi musu biyayya ya kuma had’e maka kan mu, ta k’arashe maganar hawaye na zubo mata, a hankali ya lumshe idonsa yana jin wani sanyin dad’i yana ratsa shi tun daga kasa har k’afarsa, a hankali ya bud’e idonsa ya sauke su a kanta, take ya k’arayin wutar santa na k’ara ruruwa a zuciyar sa, bai san sanda ya jawo ta jikinsa ya rungume tsam a k’irjinsa ba, a hankali yace ” thank you so much my life, cikin muryar kuka tace ” I can do anything to make you happy my dear, kanta ya shiga shafa mata yana bubbuga bayanta alamar rarrashi, cikin nutsuwa ya shiga kwantar mata da hankali.
Bayan sati d’aya Ammi ta umarce shi daya je yaga LUBNAH, ‘yar k’awarta ce ta yarda da tarbiyyar yarinyar, sannan ta yaba da hankali da nutsuwar ta, “a’a Ammi ba sai naje ba indai tayi miki nima nima tayi min ba saina ganta, “ok badamuwa cewar Ammi, Abraham ya fito daga d’aki ya samu su Ammi zaune suna hira, a hankali ya zauna kusa da ita, yana murmushi abinda ya bawa kowa mamaki kenan, Zaid yace ” Ab ya kake?
Fuskarsa a sake ya amsa ” lafiya lau ango ya shirye-shiryen biki? Zaid kasa amsawa yayi ido kawai ya zuba masa yana kallonsa baki bud’e shiko Abraham bai sake bi ta kansa ba ya kalli Ammi ya langwab’ar kai “Ammi yunwa nake ji da abince?, Murmushin jin dad’i Ammi tayi tace ” akwai kuma ur favorite food, murmushi yayi yace ” best mother of d world, ya mik’e ya nufi dining.
Kallon Ammi Zaid yayi yace ” kai Ammi abin harda san kai yanzu fa da mu ne bazaki bamu ba sai kinyi mana gori, murmushi tayi sannan tace ” shima sammasa zanyi kafin na koraka gidan matanka suma na tada musu, dariya Abraham yayi yace ” ah nifa ba aure a agenda ta yanzu, tunda dai ga k’anina nan zayyi ai shikenan yayi mana, ni can ma zan koma.
“K’aninka kodai yayanka cewar Zaid dayake dama sun sama da wannan drama tun suna yara kowa yace shine babba, dariya Ammi tayi tace ” zaku fara halinku ko? yanzu kun girma dan kwanan na zaku zama Baba, “Baba kuma? “tab ai sai dai Dad & Uncle cewar Abraham, haka dai sukayi ta hirar su cike da wasa da dariya.