GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Dariya Khamal da Abdul sukayi sosai har da dan buga kafafunsu suka ce ” suwaye manyan?

Dariya Naseer yayi yace “Real madrid cluv 1 keylo navers 3 cavejal 3 marcelo 4 sergio ramos 5 rafeal varen 6 casmiro 7 Asensio 8 tony krooss 9 karim benzema 10 luca modric 11 grez bell.

Abdul yace “ai gara kace ma Manchester City, suma suka saka masa dariya, hade ranshi yayi sosai yana cin magani kana yace ” wallahi tafi duk sauran yan wasan kwallon da kuke.
dan itama tana da manyan ‘yan wasa km kwararu da suka shahara acikin duniya Manchester city cluv 1 ederson 2 neuclas otemendi 3, kyle walker 4 fabian delp 5 ilkey gundigon 6 fernsndinho 7 bernado silver 8 rahem sterling 9 sergio aguero 10 leory sane 11 lapote,

Nan fa musu me karfi ya shiga tsakaninsu kowanne yana kokarin kawo hujoji da cewa nashi ne babba, har sanda aka tashi daga wasan, har waje suka fito tare suna wasa da dariya, tare da exchanging din numbers junansu suka yi, sannan kowa ya nufi gida.

Washe gari tun wajen k’arfe 12:00pm Naseer ya fita wajen motsa jiki, tun baiyi nisa ba yaji ana kwala masa kira, cak ya tsaya ya juyo, dariya yayi yace ” Khamal ka fito kenan?

” eh na fito, tare suka ci gaba da tafiya, Khamal ya kalli Nasser yace ” halan kaima anan kake ba nisa?

“Eh daga can baya gida na yake, number 12,dariya Naseer yayi yace ” kace bamu da nisa, ni ina layin baya number 27,ina nan da matata d’aya da yara 4 mata 2 maza 2, Khamal yace ” nima da iyalina mata ta 1 yara 3 biyu maza 1 mace,

Suna hira har suka k’arasa wajen, Abdul suka hango ya dage yana ta motsa jiki, dariya sukayi suka nufeshi, cikin dariya Khamal yace ” an dage ana ta faman aiki, halan madam ce bata san k’iba, sai a lokacin ya kula dasu.

Dariya yayi yace ” ni Madam d’ita babu ruwan ta, kudai da naku suka koro ku, tunda safe, dariya sukayi gaba d’aya, sai wajen 4:00pm sukayi sallama, har zasu rabu, Khamal ya kalli Abdul yace ” a ina gidan ka yake?

” a Jon crescent house number 35,dariya sukayi suka ce” lahh dukkan mu ashe unguwar mu d’aya,batare mun sani ba .
nan suma suka fad’a masa inda gidan su yake, murmushi yayi yace ” nima ina da mata 1 da yara biyu mace da namiji.

Sallama sukayiwa juna suka rabu, wajen k’arfe 8:00pm Abdul ya fita kallan wasan Cricket, yana zuwa ya iske Naseer zaune gaba d’aya hankalinsa ya tafi wajen wasan.

Murmushi Abdul yayi yace ” tabb kaga sarkin kallo, ajiyar zuciya Naseer yayi .
ya kalli Abdul dake tsaye hannuwasa duka zube cikin aljihun wandonsa yace ” oh kai ma kana kallan wasan Cricket?

“Sosai ma, Khamal suka hango can gefe yana ta waya, mik’ewa sukayi gaba d’aya suka nufe shi, yana ganin su ya ajiye wayar ya mik’a musu hannu yana dariya yace ” kaga manya a she nan ma kuna lel’owa?

” Sosai ma kuwa inji Naseer dake murmushi,zama sukayi suka maida hankalin su ga wajen wasan

Ba’a tashi ba sai wajen 11:pm, tare suka fito, sallama sukayiwa juna, kowa ya nufi gida.

Ranar asabar da wuri Khamal ya tafi kallon wasan Poly, yana zama saiga Naseer, shima bai dad’e ba saiga Abdul, kallonsu Abdul yayi yace ” wai ku ko’ina kuna nan kmr wasu mayyu ?

“Dariya suka kwashe dashi suka ce ” ko kuma muce kai ko’ina kana nan kmr wani magnet?

Gabadaya suka kwashe dariya wannan karon tare da tsansar murna sake ganin junansu da hk kawai kowanensu ke jin dan’uwansa ‘cikin zuciyarsa .km a duk sanda zasu hadu suna tsintar kanshi ‘cikin farinciki.
Bayan an gama wasan Khamal yace ” gaskiya ya kamata musan juna fiyye da haka tunda duk Muna tare da matan mu yakama har su mu had’asu domin zumucinmu ya daure .

Murmushi Abdul yayi yace ” gaskiya dai ya kamata, Naseer yace ” to yanzu tunda unguwar mu d’aya, kamata yayi kowa yaje yaga gidan kowa, inyaso gobe sai mu had’u a gida na, shawarar Naseer aka bi.

Washe gari Abdul da Khamal kowa yazo gidan Naseer da Matar sa da yaran sa, cikin fara’a Zarah ta tari Fateeha da Yasmeen, wanda daman tasan da zuwa agurin mijinta hira sukayi sosai, tamkar sun jima da sanin juna sannan aka zauna a dinning aka ci abinci,yayinda yaran su ‘cikin farinciki suke wasa da juna wanda hkn ya faranta ran iyayen .

Tun daga wannan ranar wata irin kwakkywar shak’uwa ma k’arfi ta shiga tsakanin Khamal, Abdul, Naseer haka matayensu da yaran su, sun saba sosai, dan bazaka tab’a tantance yaran su ba, d’an kowa na kowa ne.

Har school d’aya suka maida yaransu domin inganta zumuncinsu kyakykyawar fahimta ce mai k’arfi a tsakanin su, kowa bai da get a gidan kowa.

Khamal ya kalli dubbun manya ‘yan jaridan da ‘yan gidan TV da sauran masu d’aukar labarai, yace ” to kunji farkon yadda muka fara had’uwa, da junanmu har Allah ya dai-daita tsakanin mu, har yau Allah baisa mun tab’a samun sab’ani ko rashin fahimta a tsakanin mu ba, haka ma yaran mu, da matan su.

D’aya daga cikin ‘yan jaridan ne yace ” Sir to yaakayi kuka had’u da Ammar, Fahad, Zaid?

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:11] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)

      ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

4

Murmushi Khamal yayi ,sannan ya kalli Ammar yace ” to Bissimillah,shima murmushi yayi yace “ok sannan ya fara

” misalin k’arfe 11:00pm na dare a garin Holland, muna tafiya ni da Matata Basma a mota .
ana tsuga matsanancin ruwan sama, Basma tace ” Dear kamar hannu naga ana d’aga mana ko?

Ido sosai na k’ara bud’ewa dan ganin ko gaskiya ne, ” eh my love kuma kamar mace, ” eh macece Basma ta fad’a a dai-dai lokacin da muka k’arasa wajen, mace na gani da tsohon ciki, ga motarta a gaban ta ga dukkan alamu motar ce ta lalace, muna tsayawa Basma ta fito da sautunta ta kama wannan matar dake takawa da kyar ta shigar da ita ‘cikin mota, ta rufe ta zaga ta shiga gaba, da kyar matar ta iya bud’e baki tace “motatace tayi faci.
sai a lokacin na lura yarinyar ce wacce bazata wuce sa’ar Basma ba.

” a hankali tace ” sunana YASMEEN, “oh Basma tace, sannan tace ni kuma Basma, yanzu ina zamu kaiki ko mu wuce gida dake kawai?

“A’a please ku kaini hospital saboda ina d’an jin ciwo, “ok Basma tace, ta kalli Ammar, gira ya d’aga mata yana murmushi , direct a hospital mafi kusa muka wuce, sai da muka kai 1:00am sannan aka sallame mu Dr ya tabbatar mana da babu wata matsala, daga nan muka wuce gidan mu, da taimakon Basma Yasmeen tayi wanka, ta bata abinci, dai da Yasmeen ta dawo hayyacinta sannan ta fara laliben jakarta.

Kallon ta Basma tayi tace “me kike nema, murmushi tayi tace “jakata, Basma tace ” aiko ina tunanin kin barta a mota, ” please kozan iya samu aran waya na kira miji na na sanar dashi, inda nake .
dan nasan hankalin sa nacan a matukar tashe, “ok tace had’i da mik’o mata wayarta, kiran Abdul Yasmeen tayi ta shaida masa abinda ya faru, hankalinsa yayi mugun tashi yace ” a bashi mai gidan.

Basma ta karb’i wayar ta kaiwa Ammar, da sallama Ammar ya fara magana, cikin tashin hankali Abdul yace ” please a wace unguwa kuke? ina son nazo yanzu.

Murmushi Ammar yayi yace ” mu muna liver fool stress, amma idan ba damuwa ka fad’a mana inda gidan yake sai mu kawota, dan naga kamar baka cikin nutsuwa, “ok ina gida,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button