
Cikin rawar jiki nayi wanka na wanke kai na tasa aka gyara min kai na aka zana min lalle k’afa da hannu ta bani sabon kaya na saka ta kawo min abinci mai rai da lafiya da drinks naci, tunda naci abincin nan ban sake sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi na ganni a gidan MB cikin jini da mugun zafi da k’asa na keyi min, anan gidan MB ya kulle tun daga ranar ya mayar dani kamar matarsa ta k’arashe maganar tana fashewa da matsanancin kuka, sosai jikin Zaid yayi sanyi yaji zafin da zuciyar sa keyi masa ya d’an sassauta, cikin sanyin murya yace ” daga nan sai akayi yaya?
Cikin muryar kuka tace shine ya tafi dani turai (k’asar waje) ya lallab’a ni yayi man wayo har na yarda dashi na saki jiki sosai dashi kasancewar ban kowa a k’asar ba sai shi ya mayar dani matars…….. “Stop! Zaid ya fad’a cikin rawar murya ” please Teemah ya isa haka, yanzu ina Hajiya da MB? ” duk sunanan amma basu san nayi aure ba, “zaki iya kaini inda suke “da sauri tace ” eh tausayinta ne ya kama Zaid sosai, har bai san sanda ya jawo ta jikinsa ya rungume ta ba, yana sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya mik’e da ita a jikinsa ya nufi bed da ita, sosai ya rungumeta yana k’ara jin mugun sonta na raatsa shi, har bacci yayi awon gaba dashi, kiran sallar asuba ne ya farkar dashi a hankali ya zame jikinsa daga nata yayi bathroom, wanka yayi had’i da d’auro alwala ya zira jallabiya ya nufi masallaci, yana shigowa gidan ya nufi b’angaren Lubnab domin tashinta daga bacci, tun daga steep yake jiyo zazzak’ar muryarta tana karatun suratul baqrah, ido ya lumshe yana murd’a k’ofar d’akin da sallama, a bakin gado ya zauna yana jiranta, bata amsa ba sai da takai aya sannan ta rufe Qur’an ta jiyo ta amsa masa sallamar durk’usawa tayi har k’asa ta gaida shi, ji yayi kirjinsa na bugawa da sauri da sauri cikin rawar muryar ya amsa jim dukansu sukayi sannan ya mik’e ya fita, yadda yabar Teemah haka ya dawo ya iske ta, yayi tashin duniya amma taki tashi, kwanciya shima yayi a kusa da ita ya fad’a tunani har bacci yayi awon gaba dashi.
Basu farka ba sai wajen 11:00am shine ya fara farkawa sakamon wata muguwar yunwa dayaji kamar me, direct bathroom ya nufa yayi wanka, harya shirya Teemah ko motsi batayi ba, a hankali yasa hannu yana bubbuga k’afarta, mik’a tayi gami da mik’ewa idonta a kanshi ta sakar masa da murmushi shima murmushin ya sakar mata yace “a tashi ayi wanka ko?
Fuska ta ya mutsa tace” sweetie yunwa nake ji, “nima haka jiki wankan sai ki zo mu naimi abinci “no wallahi ban iya wankan saina fara cin abinci, da mamaki ya kalle ta yace “wankan tsarki da sallah fa? “zanyi amma saina ci abinci ta fada tana saukowa daga gadon taja hannunsa suka fita suka nufi part d’insa, aiko tunda parlor suka ji wani mugun k’anshi na sakkowa daga part din Lubnah kallanshi tayi tace “please muje wajen Lubnah naji kamar tayi abinci ba musu suka yi sama, wani sihirtaccen k’amshi ne ya bugi hancinsu gidan fes an gyara ko’ina tas ga kamshin Air freshener da turarurkan wutan dake tashi ya gauraye da sanyin AC take gidan ya rikid’e da wani irin rikitaccen kamshin dad’i.
D’auke da food flask ta fito a sannan tana bin karatun Qur’an dake tashi a hankali a TV, sanye take da wandon jean crazy da riga marar hannu ba ko bra a jikinta fuskarta d’auke da make up, suman tsaye Zaid da Teemah suka yi dan ita kanta mace ta koka kyan da dirin Lubnah, shiko Zaid ya kasa koda motsi ya kafe ta da ido, ita bama tasan suna tsaye ba, duk sanda tayi tako 1 sai duk ilahirin jikinta ya motsa yayinda da duk takunta yake saka bugun zuciyar Zaid karuwa, jin taci karo da wani abu ne yasa ta yin baya da sauri zata fad’i aiko cikin zafin nama ya taro ta ta fad’a k’irjin sa, duk suka kafe juna da ido Zaid ko k’iftawa bayayi take zuciyar sa ta shiga bugawa da k’arfi.
Gyaran murya Teemah da sauri Lubnah ta kwace jikinta cikin jin kunya ta jiya ta nufi bedroom da sauri yace ” ke zo ki bamu abinci, cak ta tsaya had’i da juyowa a hankali ta fara taku har zuwa dinning, lumshe ido Zaid ya k’ara yana k’isma abubuwa da dama a ransa, duk inda tayi idon Teemah da Zaid na kanta ita mamakin kyanta take yi, yayinda shi ya rasa mai yasa ya kasa d’auke ido daga kanta, tana bud’e food flask din wani fitinannan k’amshi ya dake su, service d’in su ta fara yi farfesun kayan ciki da doya da kwarai ta zuba musu sannan ta zuba musu samosa da spring gr ta zuba musu gunun gyad’a itama ta zubawa kanta cin abincin suke babu wanda yake magana har suka gama.
Bayan sun gama Lubnah ta mik’e ta kwashe kayan ta gyara wajen ta wanke kwanokan, Teemah tuni ta tafi shiko yana hakince akan sofa yana binta da kallo duk inda tayi, a hankali ya mik’e yace ” ya sunanki murmushi har dimples dinta suka lotsa kyanta ya k’ara bayyana, cikin zazzak’ar murya tace ” LUBNAH, bai san sanda yace ” wow nice name ba, murmushi tayi tace ” thank u, sai a lokacin yasan me ya fad’a a hankali tace ” kai fa? Murmushi yayi mata a karo na farko yace ” ZAID, “masha Allah kawai tace kafeta ya sakeyi da ido yana ganin tsantsar kyau babu abinda yafi burge Zaid kamar Addininta da tsafta ga masifar iya girki dan zai iya cewa bai tab’a cin abinci mai dad’in nata ba, ajikinta Kim dimples dinta d’an k’aramin bakinta had’i da idonta, a hankali yace ” gida zani kina da sak’o ne?
Murmushi ta kuma yi masa wanda yashi suman tsaye tace ” a’a ka gaida Ammi da Abba please, sai kadawo Allah ya tsare, “Amin nagode yace yana fita, direct part din Teemah ya kola, wanka ya iske ta shiga a bakin kofar bathroom din ya tsaya yace ” zani gida! “Ok kawai tace,, harya isa gida yana mamakin hankali da nutsuwar Lubnah had’i ingantacciyar tarbiyyar data samo, haka kuma ya shiga halayen Teemah tsaki yayi yace ” akwai gyara sosai a al’amarin Teemah.
A parlor ya iske su Ammi duk sunyi jigum-jigum da sauri ya k’asa falon” Ammi lafiya? ” cikin rawar murya tace Abbanku ne ba lafiya yana cikin mawuyacin hali, cikin firgice yace ” mai ya same shi, ” tun daren jiya yake fama da matsanancin ciwon ciki, yanzu ma yace a kira ku kai da Abraham yana san magana daku, suna cikin haka Abraham suka shigo tare da family Doctor su, da sauri ya k’arasa yace ” Ammi ya Abba? bata iya bashi amsa na tayi gaba gaba duk suka bita a baya, a kwance suka iske shi sai faman haki yake yana ganin su ya fara mik’a musu hannu da sauri Zaid da Abraham suka nufe shi rungume su yayi sosai a k’irjinsa yana zubar da hawaye a hankali ya zame jikinsa daga nasu dakyar ya bud’e yace ” dan Allah ku had’e kanku, ku daina rashin jituwar nan rai na baya so daurewa kawai nake, please ku zama tsintsiya mad’aurin ku d’aya, baku ganin idan tsintsiya na d’aure ba’a iya karya su amma da zarar an zari d’aya cikin sauk’i za’a iya karya ta, idan kanku na a ware cikin sauki za’a iya cutar daku, amma idan kuka had’e kanku in sha Allah sai kun sama murucin kan dutse, dan Allah kuyi min alk’awarin ko bayan bana raye zaku had’e kanku zaku rink’a komai tare, idan d’aya daga cikin ku yayi abu ba tare da shawarar d’an uwansa ba ban yafe muku ba, duk abinda zakuyi ya mana kowa ya Sani, haka idan na mutu duk wanda ya raba min gado ban yafe ba, ku had’e dukiyar waje 1 kuci gaba da juyawa tare kuna raba ribar amma duk wanda ya taso da magaar gado bayan bana raye ban yace ba.