GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin bata falo yasa shi aje mata akan dinning ya juya zai fita k’asa-k’asa ya jiyo maganar ta daga bedroom, gaban sa ne yayi muguwar fad’uwa, a hankali ya nufi bedroom d’in nata, yasa hannu akan handle din zai shiga yaji tana magana ” kai ma ka fiya naci wallahi kai wanne irin jarabben mutum ne haka, na fad’a maka miji na ya saka min ido da matakan tsaro dan ya fara gano ni, dan haka had’uwa dakai yanzu bata yi koyaushe ba,amma idan dare ya raba kazo gida na zan bud’e maka k’ofa ta baya idan yaso sai na d’an lasa maka koyaya ne, na sammaka.

Da k’arfi ya banka k’ofar d’akin ya shiga tana ganin shi ta saki wayar, sosai ranshi ya b’aci zuciyar sa ta shiga tafasa tana yi masa tiriri, k’irjinsa ya fara yi masa zafin k’ona a fusace ya nufeta, da sauri ta goce tayi bathroom tasa key, da sauri ta kira police station tana kuka taji an d’aga tace ” dan girman Allah ku taimake daga d’ayan b’angaren aka ce wacece ke? sunana Fatima amma anfi kira na da Teemah nice matar Zaid Muhammad Bature duk acikin firgice had’i da mummunan tashin hankali take maganar, muryarta sai rawa tace daga ji kasan tana cikin mummunan tashin hankali taci gaba” miji nane zai! zai!!! zai!!! kasa k’arasawa tayi saboda banko k’ofar da Zaid yayi da k’arfi ‘yan sandan na cewa ” hello muna jinki ci gaba! gashin kanta Zaid ya damk’a aiko ta saki gigitacciyar k’ara.

A falo yayi cilli da ita, ya hau duka sosai Teemah ke ihu tana neman ceto, wani irin mugun bak’in ciki ne ya turnuk’e Zaid ya tafi luuuuuuuu, wajen 5:00am sama-sama yaji ana tashin sa a hankali ya fara bud’e idonsa dishi-dishi ya fara gani kafin idonsa ya washe ya dawo normal a hankali ya mik’e zaune dakyar, police ya gani zagaye da shi sama da guda 20, babban cikin su ya kalle shi yace ” Zaid Muhammad Bature ko? da sauri Zaid yace” eh, police d’in yace “ok you are under arrest, cikin firgici Zaid ya zaro ido yace ” what! da k’arfi, ” yes! U are criminal Zaid and u gv us surprise, cikin tashin hankali yace” ban gane ba?

Murmushi police d’in yayi had’i da nuna masa gawar Teemah dake kwance shame-shame cikin jini, ga wuk’a nan cake a gefen cikin ta da sauri Zaid ya mik’e ya nufi inda Teemah take cikin mummunan tashin hankali da firgici……..

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:13] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

27

Da k’arfi ya rungume ta a k’irjinsa tare da sakin mahaukacin kuka mai rikitar da ma’abocin sauraro, ” i love you Teemah, wallahi ina mugun sanki duk abinda kika ga ina yi miki ina yi ne dan ki gyaru, ke ce rayuwata wallahi koda zan mutu bazan tab’a barin wanda ya kashe ki ya rayu cikin farin cikin rayuwa da walwala ba, ya k’arasa maganar yana k’ara sakin mahaucin kuka, zama police d’in yayi ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana kallonsa tare da sakin gutun murmushi, yakai 10mnt a haka sannan ya kalli Zaid yace ” I arrest you for killing ur wife a razane Zaid ya d’ago kai yana kallon sa, ya kalli yaran sa yace ” oya arrest him, da sauri suka nufi Zaid dake rungume da Teemah yana sakin kuka, dakyar suka b’anb’are shi daga jikinta suka saka mishi ankwa tare da tusa k’eyarsa zuwa harabar gidan inda suka yi parking motocinsu, police d’in ya kuma bada umarnin a fito da gawar Teemah harabar gidan.

Jin magana k’asa-k’asa yasa Lubnah surar zumbulelen hijabinta tayi waje turus Lubnah tayi dan ganin dandazon ‘yan sanda a hankali takai idonta inda mijinta ke zaune hannayensa sanye da ankwa yana kuka, cikin sanyi idonta ya sauka akan gawar Teemah dake rufe da farin yadi, da sauri ta k’ara wajen ta durk’usa agaban gawar Teemah tana kuka marar sauti hannunta na rawa tasa bud’e fuskar Teemah da sauri ta kawar da kanta gefe, cikin dakewar zuciya ta mik’e ta nufi inda Zaid yake ta tsaya a gabansa tana kallonshi ido cikin ido cikin kuka ta fara magana ” yanzu duk irin hak’urin da muka baka ni da ma’aikatan gidan nan ashe daman baka hak’ura ba.

“sai da ka kashe ta Zaid wacce irin zuciya Allah yayi maka kai wanne irin mutum ne marar yafiya, mai yasa ka kasance mai taurin kan tsira, da k’arfi taci kwalar rigarsa ” haba Zaid mai yasa zaka aikata laifin da kai kanka kasan makomarka wallahi nayi danasanin aurenka nayi nadamar kasancewa ta matarka kai mugu ne azzalumi, mai tayi maka haka dazaka kashe ta a hankali ta sake shi ta zube a gaban k’afafuwansa tana ci gaba da kukan ta “mai yasa Zaid mai yasa kayi haka mai yasa bakayi tunanin halin da Ammi da Abba zasu shiga ba, kasan halin da Abba fa yake ci ta k’asara maganar tana fashe da mahaukacin kuka, cikin rashin fahimta Zaid yake kallan Lubnah ya bud’e baki zayyi magana yaga Baba mai gadi ya rugu da gudu yana salati da sauri Baba mai gadi yace ” ya kashe ta ko?

Baba mai aiki ma ta fita daga d’akinta had’i da d’ora hannu aka ta fasa kuka had’i kallon Zaid ” kai yanzu yaron nan duk rok’onka da mukayi amma sai da ka kashe ta, Baba mai gadi ya share hawayen dake zubo masa yace ” wallahi dama sai da tace bazata koma cikin gidan ba idan ta koma kashe ta zayyi, har nan waje na ta gudu Ya biyo ta wuk’a, sai da muka rok’oshi muka bashi hak’uri ya nuna ya kyale ta, ashe kwanton b’auna yayi, shiru police d’in yayi yana binsu da kallo fuskarshi d’auke da murmushi, Zaid ko komawa yayi kamar mutum mutumi binsu kawai yake da kallo yayinda da mamaki ya gama ciki masa rai da zuciyar sa take yaji tsoro da fargaba sunyi masa dirar mikiya, nan take yaji ya fara zargin kansa, ya shiga tunanin bayan baya biyo Teemah daga d’aki mai ya faru amma ya kasa tunawa, yana cikin wannan mummunan hali yaji police sunce ” kai shiga mota had’i da hankad’a shi cikin motar.

A babban division d’in su sukayi parking, suka fito dashi, a wani babban d’aki mai cike da na’urori suka suka saka shi a d’akiyar d’akin akwai table had’i da kujerun zama babban jami’in da kes d’in ke hannu shi ne zaune a d’ayan daga cikin kujerun had’i da wasu ‘yan sanda 5 sai Zaid shima dake zaune akan kujera, babban jami’in ya kalle Zaid fuskarsa d’auke da murmushi yace ” ni sunana DSP Lawan Hassan ko zan iya sanin sunanka ” sunana Zaharaddeen Muhammad Bature, murmushi DSP yayi yace ” Muhammad Bature, sannan yace ” kasan zargin da akeyi maka? “Eh nasani ” ok wanne kenan cewar DSP, ” kuna zargin ni ne na kashe matata Fatima wacce akafi sani da Teemah, ” good to ya abin yake ko zamu iya sanin gaskiyar al’amari? shiru Zaid yayi yana tunani ” ka taimaki sharia ka fad’a mana gaskiya ta yadda sharia ma zata taimake ka, a hankali Zaid ya d’ago kai yace ” na kasa tuna komai ne, “what! DSP ya fad’a a zafafe sai kuma ya taso yaje kusa da Zaid yayi k’asa-k’asa da murya yace ” please Zaid kar muyi haka dakai, kayi k’ok’arin tuna koda abu d’aya ne.

Shiru Zaid yayi ya shiga tunani ” yawwa tuna, yi tunani abinda DSP ke cewa kenan, amma ina Zaid ya kasa tunana komai a hankali ya d’ago kai yace ” I cant, table d’in DSP ya buka da k’arfi had’i da juya baya yana shafa kansa, da hanzari ya juyo ya kalli yaransa yace ” ku kawo min phone recording “ok Sir d’aga daga cikin su ya fad’a had’i da fita, baifi minti 5 ba sai gashi ya dawo, umarni ya bayar da a had’a na’urar da sauran na’urorin, kwatsam Zaid yayi muryar Teemah cikin firgici da mummunan tsoro gami da mugun tashin hankali cikin kuka take cewa ” nice Fatima Muhammad Bature matar Zaid Muhammad Bature miji na ne zai zai zai sai kuma matsananciyar k’arar data saki da sauri Zaid ya mik’e daga zaunen dayake cikin mugun tashin hankali kansa ya dafe da duka hannuwansa wanda barazanar tsagewa gida biyu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button