
A hankali DSP ya mik’a masa ruwan sanyi ya hard’e hannuwansa a k’irjinsa ya k’urawa Zaid ido yana murmushi, hannun Zaid na rawa ya karb’i ruwan, “na baka 2hrs ka huta, ya fad’a had’i fita, zaman dirshan Zaid yayi a k’asa yasa hannuwansa duka biyun ya dafe kansa, bayan 2hrs DSP ya dawo ya zauna a gaban Zaid da tunda ya zauna ya kasa motsawa DSP ya kalli Zaid yace ” All the evidence goes against you, as for ur wife, dat ur wife’s call 2 the control room at 12:20am, if not ur wife’s voice, say dat no 1 tried 2 kill her, or say dat u know nothing at all.
Ido Zaid na kallon gefe yace ” yes, it is Teemah, but I don’t know how it happened & when, DPS, if dat’s true we must find Teemah killer first, some 1 must’ve attacked her when I was out, but u can grill me if you want to, da k’arfi DSP ya buga table d’in ya durk’uso da fuskarsa dai-dai ta Zaid ta yadda zuna iya jiyo numfashin juna yace ” skip d act, Mr Zaid, ur wife has clearly mentioned ur name, another thing the call was being taped & u had no idea about it, da k’arfi Mukhtar ya bango k’ofar cikin zafin rai yace ” waye in charge d’in ces d’in nan, ” DSP Hassan Lawan yaji an fad’a daga bayan sa ciki tak’ama Mukhtar ya juya yana facing DSP , DSP yaci gaba ” I’m in charge of did case, all dis is happening as per my wish wish, murmushi gefen baki Mukhtar yayi yace ” ur wish?
Kun san dama Mukhtar lawyer ne, kuma shine Lawyer d’in Muhammad Bature Family
Mukhtar yaci gaba ” d law doesn’t allow u to act according 2 ur whims & fancies, if you want to grill him, you should have a remain order from the court, murmushi DSP yayi idonsa nakan Mukhtar yake yiwa yaran sa magana ” Isma’il ” yes Sir ” Barrister fa yayi magana mai kyau, kuma gaskiya ya fad’a ko? shiru yaron nasa yayi dan ya gano so yake ya rainawa Mukhtar hankali, ya fuskanci Mukhtar yace ” if you think you will get him bail tomorrow morning then you are wrong, murmushi Mukhtar ya k’arayi masa yace ” ok that’ll be decided tomorrow morning, as of now, ya sauke ajiyar zuciya ya kuma cewa ” I want to talk my client in private if don’t mind ya k’arasa maganar yana yi masa murmushi, kallonsa DSP ido cikin ido yace ” sure, it’s all your ya fad’a had’i da juyawa yayiwa sauran yaransa inkiya da su fita suma.
Da sauri Mukhtar ya k’arasa wajen Zaid da tun shigowar sa yake bin su da kallo, a kusa dashi ya zauna had’i da dafa kafad’arsa ya kalle shi ido cikin ido yace ” Friend wai ya akayi ne mai ya faru tsakanin ka da Teemah me kayi mata? Wani irin kallo Zaid yayiwa Mukhtar “ok kai ma kana zargi na kenan? kaima ka yarda da cewar ni na kashe Teemah? “haba Zaid tambayar ka fa kawai nayi wallahi na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kai na, kawai ina son jin gaskiya abinda ya faru ne saboda mu samu mafita a kota saboda nine lawyer ka, kuma ko ba wannan a matsayi na na babban abokin ka dole ne nasan komai, Zaid na yarda da kai sosai fiye da tunani saboda na tabbatar da bazaka tab’a aikata mummunan abu ba, murmushi Zaid yayi yace ” thank you friend, ” you are welcome, babu godiya a tsakanin mu dan haka daga yau kar ka kuma yi min godiya, jiya ai ba yau ba you are my childwood friend, family ku sunyi man komai matsayin nan ma danake ciki dan ku ne, murmushi kawai Zaid yayi sannan ya bawa Mukhtar labarin komai tun daga farko har k’arshe.
Ajiyar zuciya Mukhtar ya sauke da k’arfi cikin mutuwar jiki ya dafa Zaid yace ” karka damu Friend Allah yana bayan mai gaskiya kaji, kuma in sha Allah mu zamuyi narasa, murmushi kawai Zaid yayi, Mukhtar ya mik’e ya fita, Mukhtar na fita DSP ya shigo yaci gaba da gudanar da bincike kasancewar gobe ne za’a fara zaman kotu.
Lubnah kuwa ana fita da Zaid da gudu ta koma d’aki ta fad’a gado ta saki kuka mai cin rai, tana kukan tana magana ” maiyasa Zaid me tayi maka, akan me zaka kashe ta, sai da tayi mai isarta sannan ta mik’e ta shiga bathroom tayi wanka, doguwar riga kawai ta zira a jikinta sannan ta kira iyayenta ta sanar da su halin da ake ciki, cikin tashin hankali Mama da Baban ta suka ce gasu nan, aiko ba jimawa suka k’asaro Lubnah na ganin su ta rungume su had’i da fashewa da gigitaccen kuka, sosai Mamanta ta lallab’a tayi shiru ta basu labarin komai, a hankali Lubnah ta d’ago kai ta kalli iyayen nata cikin kuka tace ” please karku sanar da iyayensa dan a halin yanzu Abba bashi da lafiya sosai nan ta sanar dasu halin da Abban ke ciki, ran Baban ta ne ya b’aci sosai yace ” amma Lubnah baki kyauta min ba ace Abba yayi rashin har a fitar dashi waje amma koki sanar da ni?
Cikin kuka ta basu hak’uri, rungume ta Dady yayi yace ” bakomai daughter in sha Allah mu zamu zame masa iyaye zamu yi masa gata za kuma mu tsaya mishi amma dole a gayawa Hassan d’insa (Abraham) ya kalle ta yace ” kina da number Abraham? “A’a amma wayar Zaid na hannuna ” ok duba nasan zaki ga number sa, ba musu ta mik’e ta d’auko wayar tako ci sa’a babu pin, tana dubawa taga number ta bawa Dady, bugu d’aya ya d’aga Dady ya sanar dashi duk halin da ake ciki, a firgice Abraham yace ” what!! da sauri Dady ya rok’e shi akan karya sanar da su Ammi, “ok in sha bazan sanar dasu ba amma ni gani nan gobe.
Washe gari a kotu
A babban kotun dake garin Bauchi motar police ta faka d’auke da Zaid wanda hannuwansa ke d’auke ankwa, yana fitowa dubban jama’a tare da ‘yan jarida sukayo kan shi dakyar da taimakon hukuma aka samu aka shigar dashi kotun, bayan kowa ya zauna lawyer gomnati ya fito ya gabatar da kansa had’i da cewa ” ya mai girma duk wata shaida da ake nema akan kisan da Mr Zaid yayi na kashe matarsa Teemah an riga an samu an kuma tabbatar domin da kanta ta kira police station ta sanar dasu cewa mijinta yana san kashe ta, bayan haka kuma duk ma’aikatan gidan sun tabbatar da faruwar hakan, ina mai neman alfarmar kar wannan koto mai adalci ta bada bailing Mr Zaid akan kud’i ko nawa, yana kaiwa nan ya koma mazaunin su, da sauri Mukhtar ya mik’e ya gabatar da kansa yace ” my load kamar dai yadda kowa ya sani Mr Zaid sanannan d’an kasuwa ne a wannan k’asar kuma yana da tarin dukiya had’i dama a hannunsa ta yadda idan yaga damar kashe mutum abu me mafi sauk’i a wajen sa, zayyi abinsa ne cikin tsari ta yadda babu wanda zai zarge shi balle har a sani kuma zai iya d’aukar killers suyi masa kisan ba tare da sanin kowa ba da wannan jawabin nake rok’on wannan kotu mai adalci data bada bailing Mr Zaid dan har yanzu zarginsa ake ba’a tabbatar ba, da sauri lawyer gomnati ya mik’e yace ” ina rok’on wannan kotu da kada ta sake ta bada bailing shi saboda zai iya amfani da kud’i da kuma hanyar da yake da ita yayi wasa da hankalin shari’a, ajiyar zuciya alk’ali yayi sannan ya d’ago kai yace ” za’a dawo zaman kotu na biyu a ranar 14 ga wannan watan sannan hukumar ‘yan sanda zataci gaba da tsare shi a hannun su, yana kaiwa nan ya buga table alamar an tashi, gaban Mukhtar DSP yazo ya kalle shi ido cikin yana murmushi.
Bayan sun koma police station ne DSP tare da yaran sa suka sake taruwa a d’akin binciken, DSP ya kalle Zaid yace ” ko za iya bamu labarin farkon had’uwar ku, a hankali Zaid ya d’ago kai ya kalli DSP sannan ya shiga bashi labarin had’uwar shi da Teemah har zuwa ranar da abin ya faru daga k’arshe ya kuma kallon DSP yace “That’s it, I don’t know what happened afterwards, when I regained consciousness, you folk were before me, whatever Teemah was, whoever she was I love her dearly, I could never kill her, murmushi DSP yayi yace ” the court will decide that.