GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan an gama duk binciken da za’ayi da gawar Teemah ne aka kaita gidan ta na gaskiya aka binneta a makwancinta,

Ranar 14 ga wata aka koma kotu kamar yadda Alk’ali yace ” bayan kowa ya zauna an nutsu ne lawyer gomnati ya mik’e ya kuma gabatar da kansa sannan ya kalli Alk’ali yace ” hujjoji game da shaidu duk sun bayyana akan Mr Zaid ne ya kashe matarsa Teemah, ina rok’on kotu ta bani dama na gabatar da shaidata ta farko, alk’ali yace ” an baka, risina kai yayi yace nagode, juyawa yayi ya kalli jama’ar dake zaune a kotu yace ” kotu tana san ganin Baba mai gadi a gaban kotu, a d’an tsorace Baba mai gadi ya fito ya tsaya, gabansa lawyer gomnati yace ” ko zaka iya sanar da kotu ainahin sunana? ” cikin rawar murya yace ” Malam Mamman ” Malam Mamman shin shekarar ka nawa kana aiki Zaid?

” tunda yayi aure na tare dashi a gidan sa amma nakai sharaka 15 ina aiki a k’ark’ashen mahaifin sa, ” ok shin menene gaskiya abinda ya sani akan tuhumar da ake yiwa mai gidanka? “Eh to ni dai ina daga d’aki na dake bakin get na rink’a jiyo ihun matarsa tana cewa ” dan Allah karka kashe ni wallahi bazan kuma ba, ni dai ina nan zaune sai naga ta shigo d’aki na da gudu tana ihu tana cewa Baba ka taimake ni wallahi kashe ni zayyi, ana haka sai gashi shima ya shigo d’akin hannuwansa rik’e da wuk’a yana cewa wallahi sai na kashe ki, da sauri Zaid ya d’ago ido yana kallon Baba mai gadi, Baba mai gadi yaci gaba ” dakyar na rok’eshi ya hak’ura ya kyale ta, lawyer gomnati yayi murmushi yace ” ina kar abinda ka sani kenan? yace ” eh ” ok koma ka zauna, ya juya wajen alkali yace ” ina rok’on kotu ta bani dama na gabatar da shaida ta biyu kai kawai alkali ya d’aga masa, ya juya yakira baba mai aiki, itama ta fito yayi mata irin tambayar da yayiwa Baba mai gadi tace ” nima ina daga d’aki na na rink’a jiyo ihunta daga k’arshe sai gata ta shigo d’aki na da gudu ta b’oya a baya na sai gashi ya shigo hannuwansa rik’e da wuk’a yana haki yana cewa wallahi sai na kashe ki, dakyar nima na bashi hak’uri ya kyale ta, in banda mamaki, tsoro had’i da muguwar fargaba babu abinda Zaid ke ciki duk ya tsorata yana cikin wannan hali yaji lawyer gomnati yace ” bashi dama ya gabatar da shaida ta k’arshe, bayan an bashi damar ne yace ” LUBNAH da sauri Zaid ya d’ago kai cikin Firgici da tashin hankali.

A hankali take takowa harta k’araso wajen tsayawar shaida ta tsaya, ido Zaid ya k’ura mata gani yayi tayi muguwar rama da gani tana cikin mugun tashin hankali, a hankali ta d’ago kai tana zubar da hawaye ta kalle shi aiko karaf suka had’a ido, aiko take gabansa yayi muguwar fad’uwa k’irjinsa ya shiga bugawa da k’arfi…………

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:13] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

28

Barrister ya kalle ta yace ” ya sunanki ” Lubnah Muhammad Bature, “meye alak’arki da wanda ake tuhuma? ” miji na ne, ” ok kiji tsoran Allah ki fad’awa kotu gaskiyar abinda kika sani game da wannan kissan, d’an shiru tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya had’i da share hawayen dake zubo mata a hankali ta kuma kai idonta kan Zaid taga shima ita yake kallo sosai ya kafe ta da idon shi, Barrister yace ” kiji tsoran Allah ki dubi girman Allah ki sanar damu gaskiya karki duba alak’arki da wanda ake tuhuma, ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na biyu sannan ta fara magana cikin kuka ” a ranar da abin ya faru bayan ya dawo gida yayi wanka ya shigo part d’ina yaci abinci, har muka gama cin abincin amma banga Aunty Teemah ta zo ba alhalin tare muke cin abinci, danaga bata shigo sai na zuba mata nata a food flask nace ya kai mata, da farko kin zuwa yayi sai da na k’ara yi masa magana sannan ya d’auki abincin ya fita dukda ransa bai so ba.

“Ranar kwanki ne? da sauri Zaid ya d’auko kai suka had’a ido, haka nan Lubnah taji kawai bazata iya bayyawa duniya sirrin zamantakewar auren ta ba, dan idan tayi hakan kamar ta nunuwa duniya mijinta ba adali ba bane, babu wanda zayyi masa adalci a take za’ayi masa mummunar fassara, dan haka tace ” eh tana kallan fuskarsa da k’arfi Zaid ya sauke ajiyar zuciya game da runtse idonsa, Barrister yace ” daga nan fa?

“D’aki na koma na kwanta sama-sama na rink’a jiyo ihunta da sauri na mik’e nayi parlor, a parlon muka ci karo da Teemah ta shigo da gudu a firgice tana kuka ganin yanayin da Teemah ta shigo ne yayi mugun tsora ta ni, da gudu nayi bedroom Teemah ma tabi bayana, daga ni har ita muka koma can k’uryar gado muka b’oye yayinda ni na k’urawa k’ofa ido ina sauraren ganin abinda ya firgita Teemah haka, da sauri naga Zaid ya shigo hannunsa rik’e da wuk’a tsirara, k’ara k’ank’ame ni Teemah tayi tana cewa wallahi kashe ni zayyi Lubnah please ki taimake ni karya kashe ni, shi kuma sai huci yake yana cewa wallahi sai na kashe ki, dakyar na lallab’e shi na bashi hak’uri ya hak’ura ta k’arasa maganar cikin azababben kuka.

Barrister yace ” iyakar abinda kika sani kenan?

“Eh cewar Lubnah, “ok koma wajenki ki zauna, tunda Lubnah ta fara magana Zaid ya k’ura mata ido cike da matsanancin mamaki had’i da mummunan tsoro, shi dai a saninsa hakan bata faru ba, iyakar abinda ya sani kawai ya biyo ta parlor kuma hannunsa ba wuk’a, take ya fara yiwa kansa tamayar ya akayi hakan ta kasance, shin meke faruwa dashi, meke damun shi, kodai bashi bane, meke shirin faruwa dashi ne, tabbas yasan akwai wani b’oyayyen al’amari a k’asa.

Barrister yace ” da wannan shaidu nake kira da wanna kotu mai adalci data yankewa wanda ake zargi hukunci domin duk wata hujja da ake nema an samu an kuna tabbatar da shine wanda ya kashe matarsa da kansa, da sauri Mukhtar ya mik’e domin tuni jikinsa ya gama yin mugun sanyi shi kansa tsoro da firgici sun shige shi, cikin mutuwar jiki ya fara magana ” ina rok’on kotu ta bani dama nayiwa Lubnah, Baba mai aiki, Baba mai gadi tambayoyi, bayan an bashi ya kira su duka gaban kotu ya kalle su yace ” ko a cikin ku akwai wanda wata matsala ta tab’a shiga tsakanin shi da Zaid ko Teemah?

Duk suka ce a’a,ya kuma cewa acikin ku akwai wanda yaga sanda Zaid ya kashe Teemah da idonsa? nan ma suka ce a’a, “to ya akayi kuka tabbatar shi ya kashe ta, ko kuna da hujjar hakan? cikin sanyin jiki suka ce a’a, “to mai yasa kuka bada shaidar shiya kashe ta? Baba mai gadi yace ” ai bamu ce shiya kashe ta ba, ” ok to idan bashi bane waye? cewar Mukhtar “wani ne, cewar Baba mai aiki, “wani wa? “zai iya yiyiwa wani ne ya kashe ta dan ya d’orawa Zaid dan ya b’ata masa suna, ” gud cewar Mukhtar, ku koma ku zauna, ya juya wajen Alkali yace ” su wad’anda aka gabatar a matsayin shaida sunce basu tabbatar da cewa Zaid ne ya kashe Teemah ba, sannan sun k’arawa kotu haske akan ko wani ne ya kashe ta dan ya b’atawa Bature Family suna, da wannan nake rok’on kotu data sake bada damar bincike, bayan kowa ya zauna an nutsu ana jiran abinda Alkali zaice ne ya d’ago kai yace ” kotu ta d’age k’ara nan da ranar 21 ga watan nan, kuma a ranar ne kotu zata yanke hukunci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button