GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ranar 21 ga wata, bayan kuwa ya hallara a kotun an gabar da komai Lawyer gomnati ya mik’e yace ” yau ina da manyan shaidu biyu wanda sun isa su tabbatar da cewa Zaid ne yayi wannan kisan kan, yana gama fad’a ya kalli DSP yace ” kawo call recording d’in nan, DSP ya mik’e ya d’auko call recording ya kunna a kotu kowa naji, bayan nan ya kuma kallan Alkali yace ” shaida ta biyu CTV Camera gidan sa d’auki sanda yake bin Teemah da gudu rik’e da wuk’a tana ihu, ya juya tare da bawa wani police umarnin ya kunnan, d’an sandan ya mik’e had’i da kunna babban TV dake kotun ya jona, take Zaid ya bayya yayinda yake bin Teemah da gudu hannunsa rik’e da wuk’a, yana cewa wallahi sai na kashe ki, itama kuma tana gudu tana ihu, ta shige d’aki, daga nan video ya katse.

Ai Zaid suman tsaye yayi kawai ya kasa koda kwakkwaran motsi, sosai ya k’urawa TV idon dan yana son tabbatar da abinda yake gani, tabbas shine babu ko tantama, shi kansa ya gaskata abinda yake gani a gabansa, ya kuma yarda da cewa hotansa ne ke bayyana a kwatin TV hannunsa rik’e da wuk’a abu d’aya ne ya kasa yarda dashi har yanzu cewa shine ya kashe Teemah, yak’i tabbatar wa da kansa hakan, har a lokacin yak’i gaskatawa zuciyar sa tak’i yarda akan shine wanda yayi kisan, sosai tsoro, fargaba sukayi nasarar yimasa dirar mikiya had’i dayi masa k’awanya a kowacce gab’a dake gangar jikinsa tuni zuciyar sa ta tsinke gudun jinin dake jikinsa ya k’aru, bayan an gama gabatar da shaida Mukhtar ya mik’e yace ” idan har gaskiya ne abinda cameran ta d’auka meyasa bata d’auki inda ya kashe ta ba, haka kuma ya akayi Teemah ta shiga duk d’akin wad’anda suke gidan a lokaci d’aya bayan kowanne yace lokacin da suka shiga d’akinsa sai da ya bawa Mr Zaid hak’uri ya hak’ura, haka ma ai a call recording din cewa tayi mijin tane zai zai zai bata karasa abinda take son fad’a ba, kuka sani ko cewa zatayi mijin tane zai kare ta, ko mijin ne zai kwace ta akwai abubuwan da dama da hakan ke nufi ba lalle tana nufin zai kasheta ba.

“Kum.. d’ago jajayen idonsa da Zaid yayi suka had’a idone ya hana shi k’arasawa, a hankali Zaid ya shiga girgizawa Mukhtar kai, yana cewa ” Friend kayi shiru kawai duk abinda zaka fad’a musu baza su tab’a yarda ba, dan ko ni na fara zargin kai na, ni kaina na rasa meye gaskiyar al’amarin nan balle kuma wani, ka barshi kawai Friend nagode sosai Allah yabar zumunci ni dai fatana ko bayan rai na Allah bayyana gaskiya, “amma friend… da sauri Zaid ya d’aga mishi hannu yace ” kabar shi nagode, shiru Mukhtar yayi cikin mutuwar jiki yana share hawaye ya koma ya zauna.

Alkali ya d’ago kai yace ” duba da irin tarin hujjojin da aka gabatar a gaban kotu, kotu ta yankewa Zaid Muhammad Bature hukunci d’aurin rai da rai had’i da horo mai tsanani a baban gidan yarin dake garin Bauchi, wata mahaukaciyar k’ara Lubnah ta saki had’i zubewa k’asa, da sauri Zaid ya yunkura zaije wajen ta police suka tare shi, sukayi caa akanshi suka rik’e shi, yana ji yana gani aka danna shi a mota akayi gidan yari dashi yana ihun mutuwa, ita kuma Lubnah akayi asibiti da ita.

Tunda aka kaishi prison ya shiga tunanin wanda zai iya had’a masa wannan GADAR ZARE, ran shi ya tsaya akan Abraham saboda shi a sanin sa duk duniya bashi da wani abokin gadawa ko gaba, shi dai yasan Abraham ne kad’ai ya fito ya nunawa duniya baya k’aunarsa akan dukiya, kuma yasan babu abinda Abraham bazai iya akan kud’i ba, kuka ya fashe da shi saboda tsabar bak’in ciki da takaicin wai d’an uwansa uwa d’aya uba d’aya ne yayi masa haka akan dukiya, a cikin gida yarin yake ihu yana kuka, sai da Lubnah tayi kwana 3 a hospital sannan ta wartsake ta koma normal, tun daga ranar da aka sallamota daga asibiti kullum sai ta kaiwa Zaid abinci kuma sai ta tsaya ta tabbatar da yaci, yauma kamar kullum ta shirya ta d’auki abincin ta kai masa, bayan yaci ya d’ago kai ya kalle ta yace ” Lubnah ni dai kinga yadda Allah yayi dani da rayuwa ta dan haka k’addarar mu bazata tab’a zuwa iri d’aya ba, bazan bari kema rayuwarki ta salwanta kamar yadda tawa tayi ba, dan haka na yanke hukuncin sauwak’e miki aure na dake kanki dan kar in barki da nauyin aure na a kanki, a firgice ta mik’e ta shiga girgiza mishi kai hawaye suka shiga zubo mata ido kawai ta k’ura masa ta kasa cewa komai, da gudu ta wuya ta fice daga prison din yayinda Zaid keta kwala mata kira amma kota juyo.

A hankali Mukhtar ya tako har bakin k’ofar d’akin da Zaid ke tsare ya tsaya idonsa yana zubar da hawaye daga ganinsa kasan yana cikin mummunan tashin hankali game da firgici, a hankali yasa hannu ya share hawayen dake zubo masa ya kalli Zaid yace ” har abada bazan tab’a daina kukan bak’in ciki ba Friend, murmushi Zaid yayi yace ” ka cika aboki na kwarai da ako’ina zan iya alfari dakai, nagode sosai dan kayi iya k’ok’arin ka, ni yanzu rayuwata ta k’are, please Friend kayi min wani abu d’aya, da sauri Mukhtar yace ” meye shi ka fad’i ko meye nayi maka alk’awarin zanyi maka shi duk wahalarsa, ” murmushi Zaid ya kuma yi a karo na biyu sannan yace ” so nake kafin na mutu na fara kashe wanda ya kashe Teemah tukunna, bani da wani buri daya wuce wannan a rayuwata, dan girman Allah Friend kayi min wannnan k’ok’arin.

“Ina bakin cikin yadda zan mutu nabar makashin Teemah a raye yaci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, murmushi Mukhtar yayi yace ” indai wannan ne burinka zan cika maka shi a satin nan, Zaid yace ” yawwa friend please ka taimake ni, sannan gobe kazo da gaba d’aya takardun companies d’in mu had’i da takardar kotu ta yarjejeniya dan zan bar maka amanar dukiyar mu, dan bazan tab’a bari burin Abraham na mallakar dukiyar mu ya cika ba, bazan tab’a barin dukiyar da Abba yasha wuya wajen tara ta salwanta ta ba, shiru Mukhtar yayi sai can kuma ya sauke ajiyar zuciya yace ” gaskiya Friend bazan iya d’aukar maka wannan amanar ba, dan amana tana da matuk’ar wuya zan dayyi k’ok’arin fitar dakai daga nan, hawaye ne suka shiga zubowa Zaid da sauri Mukhtar yace ” haba Friend kukan kuma na meye ko so kake ka tada min hankali?

Ido Zaid ya k’ura masa kawai yana zubar da hawaye, sosai hankalin Mukhtar yayi matuk’ar tashi, cikin tashin hankali ya shiga tambayar Zaid abinda ke damunsa, dakyar Zaid yayi magana ” yanzu ina ji ina gani zan bar dukiyar mu ta salwanta, yanzu a hannun Abraham zan mutu nabar dukiyar mu? dakyar Mukhtar ya lallashi Zaid yayi shiru, shima Zaid ya shiga rok’on sa akan ya karb’i amanar dukiyar, dakyar dai Mukhtar ya karb’a badan yaso ba.

Washe gari Mukhtar yazo da takardun companies dana yarjejeniya, ya mik’ewa Zaid had’i da cewa kayi tunani dai Friend, tsaki Zaid yayi tare dayin sigh a takardun , ya mik’ewa Mukhtar yace ” na baka amana, murmushi Mukhtar yayi yace ” bakomai Friend, sai da ya juya gefe da gefe sannan ya ciro magani daga aljihunsa ya bawa Zaid yace ” kasha maganin nan, idan kasha zakaji kamar heart attack amma bashi bane, daga nan za’a saka a ambulance dan akaika asibiti idan kunje tsakiyar daji sai kayi k’ok’ari ka gudu, ni kuma zan jira ka da mota a dajin daka fito sai mu gudu, da sauri Zaid ya warci maganin yace ” kaje yanzu ka jira ni, ” Ok kawai Mukhtar ya fad’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button