GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yanzu zamu zo da iznin Allah, da Basma aka tafi kai Yasmeen gida, a harabar gidan suka iske Abdul sai safa da marwa yake, yana ganin motarsu ta shigo tun kafin su k’ara sa parking ya k’ara sa da sauri wajen.
Yasmeen ta fito da kyar aiko da sauri Abdul ya rungumeta ajikinshi .
yana sauke naunauyen ajiyar zuciya, gyaran murya Ammar yayi, sai lokacin Abdul ya tuna ashe fa basu kadai ne agurin ba .
sakin Yasmeen yayi tare da nufar inda Ammar yake yana Miko masa sukayi musabaha fuskasa cike da tsansar farinciki taimakon matarsa dasukayi .
sosai yayi masa godiya, sukayi sallama.

Washe gari bayan an gyara motar Ammar yana wajen aiki yayiwa Basma waya yace yanzu bakanike zai kawo mata mota takaiwa Yasmeen, muryarta cike da shagwab’a tace ” ni idan Kai wa zai dawo dani?

Murmushi yayi kamar tana kallan sa yace ” ok to mu had’u a gidan, lokaci d’aya Basma da Ammar suka k’ara gidan, number Abdul da Yasmeen ta kiya ta bawa Ammar ya kira Abdul, aiko da sauri ya fito da fara’a, ya taresu yana cewa ” kwa tsaya daga waje ai ciki zaku shigo, yana maganar yana mik’awa Ammar hannu.

hannunsu rik’e dana juna suka karasa shiga ‘cikin gidan a tsaye suka samu Yasmeen a parlor tana jiran shigowar su, da fara’a ta rungume Basma, nan dai aka k’ara jajantawa juna, Ammar ya mik’awa Abdul key d’in motar ya karb’a had’i da sake yi masa godiya.

Sai da suka ci abinci,s sannan Yasmeen ta matsawa Ammar akan ya bar mata Basma sai dare ya biyo ya d’auke.
hakan ko akayi, anan Ammar ya barta suna ta hirar su .
Shi km suka fita tare da Abdul

Tun daga wannan rana zumumci mai k’arfi ya k’ullu tsakani Ammar da Abdul, har Abdul ya had’a Ammar da Khamal da Naseer, ita kuma Yasmeen ta had’a Basma da Zarah da Fateeha, shi kuma Ammar ya had’a Abdul, Naseer, Khamal da Zaid da Fahad, itama Basma ta had’a Yasmeen da Lubnah da Kausar.

Ahankali Ya juyo ya kalli tarin ‘yan jaridan dake tsaye yace ” to kunji asalin had’uwar mu wanda idan ka duba kasan daga Allah ne, musamman ma yadda duniya ta lalace yanzu ta zama ba yarda da Amana ballanantana uwa uba Gaskiya yanzu.

Kowa a wajen yayi shiru yana ji da sauraro .
Ahankali Al’amern yace ” masha Allah ko zamu iya jin labarin ku d’ai-d’ai ?

dukkan su sukayi shiru batare da kowanensu yayi yunkurin cewa komai ba kafin Daga Naseer yace ” da dai gaba d’ayan mu mun manta da rayuwar mu ta baya, mu rufe babin abinda yagabata akanmu sbd tunoshi bashi da wani amfani sakamakon rudanin dake tattare acikinsa .wanda muninsa kadai ya isa ya nufar da farin ruhi …. amma babu komai zamu iya baku, domin yazama iznah Ga wasu ‘cikin al’uma .. Naseer ya kalli sauran Aminan nasa kana yace ” wazai fara acikin mu ?

Abdul yayi sanyayyiyar murmushi me hade da kwalla tausayinsa kanshi take hawaye ya balle masa batare daya shirya hkn ba ‘cikin rawar murya yace ” bari bari ni na fara, yakarasa fadar hk cikin muryar kuka .
Sannan ahankali ya fara bada labarin sa hawaye Na tsiyaya a idanunshi tamkar ba namiji ba .

LABARIN ABDUL

“Ni d’an asalin garin gambe ne a bakin kasuwa gidan mu yake, mu uku kacal iyayen mu suka haifa mace 1, maza 2 gaba d’ayan mu uwarmu d’aya uban mu d’aya, nine babba sai k’anwata wacce a k’alla na bata sama da shekaru goma,a duniya sannan aka haifeta .
sunan ta Ramlat sai d’an autan mu wanda bazai wuce shekara biyar ba, bayan na gama secondary school aka haifeshi, mu ba talakawa bane ba kuma ba masu arziki bane,muna ‘cikin rufin asirin ubangiji sannan km Muna gudanar da rayuwarmu farinciki Daga mu har iyayenmu .
Tare da lallab’a rayuwar mu.

Muna da mak’ota wanda a wajen iyayen mu sun wuce mak’ota sun zama kamar ‘yan uwa, juna saboda zaman aminci da makotan dake tsakani kan iyayen mu a had’e yake daga maza har mata, tunda muka taso bamu tab’a jin wani abu na rashin dad’i ya shiga tsakanin su ba.ko a tsakaninmu yaransu bbu wani bambanci idan ba’a gaya mutun ba wallahi zai dauka shakikan yan’uwan juna ne ..

Sosai suke zumunci wanda ni tunda Na taso a Haka na gansu km a tunani ‘yan uwan mu ne na jini ashe, sam abun ba Haka bane .
sai da na girma ba k’ara wayo sosai sannan na fahimci ba haka bane

, su din makwatamu ne km ‘yan asalin kasar niger ne, tunda suka zo neman kudi basu tab’a komawa gida ba.
, mahaifin mu yayi yayi suje suka ki zuwa harya gaji da yi musu nacin zuwa kasarsu ya kyale su, suna da d’an su d’aya mai suna UMAR tun daga kanshi Allah Bai sake basu haihuwa ba.
, wanda a shekaru sa’a nane,muke a haihuwa .
an haife da da kwana 2 shims aka haife shi,muna da shekaru 10 ne, kwatsam ranar da iyaye na bazasu tab’a mantawa ba, domin sun tashi da mummunan labarin Na rashin iyayen Umar.

Suna kwance da dare babbar moatar daf ta kwacewa matuk’inta tayo ‘cikin gidan su Umar tabi takan iyayen sa, ta murk’oshesu.
, shi yana gefe yana kwance, Allah bai sa kwanakin sa sun k’are ba, iyaye na sun ji bbu dadi sunyi jimamin mutuwar sunyi kuka har sun gaji,sakamakon rasa makwaftansu da sukayi haka sukayi ta neman danginsu domin sada ummar dasu amma basu samu ba.
Dan ko wanda yasan su Allah Bai Sa sun samu ba . Haka suka gaji da nema da cigiya suka hakura suka rungume umar ajikinsu da tarin tausayin yaron .

Haka suka had’a mu nida Umar suka rik’e komai iri d’aya suke sai mana, idan ko basu da arzikin abu biyu hak’ura suke yi, tunda Umar yako hannun iyaye na bai tab’a kukan maraici ko rashin iyaye ba, .
Sannan ko su iyaye na basu tab’a nuna san kai a tsakanin mu ba sun daukeshi tamkar su suka haifeshi .

Bayan mun gama secondary school ne, iyaye na suka nemi mu ci gaba da karatu kai tsaye na amince wanda hakan shine burina, amma abinda ya bawa kowa mamaki k’in amincewar Umar babu yadda iyaye na basuyi ba akan yacigaba da karatu kmr yadda zanyi amma fir Umar yak’i amincewa acewarsa yafi san yayi hakar kasuwanci.

‘Cikin matsanancin damuwa Mahaifina ya kalleshi , yace ” to Umar ko gaba karkayi kuka damu .
kayi kuka da kanka,sbd Shi ilimi abu ne me mahimmanci a rayuwar Dan Adam ban hanaka yin kasuwanci ba Amman nafi son ka dan samu illimi me zurfi .
Shi ilimi haske ne a rayuwa ,duk abinda mahaifina yasan zai yi Dan ganin umar ya amince da cigaba da karatu yayi km ya fada masa , babu irin shawarar da iyaye na basu bashi ba amma fir umar yaki amincewa yace shi sam a’a business yake da raayin .
Haka iyayena suka hakura suka barshi ba Dan ransu yaso ba sai Dan basa son matsa masa amatsayinsa Na maraya .

Bayan wasu kwanaki aka damu mahaifina da yawan kawo k’arar Umar jama’a kowa yace Umar yayi masa kaza ko yayiwa ‘yarsa kaza.h k
mahaifina yasa me shi yayi masa fad’a sosai .

Amma mu a gidan da kuma kamanni duk inda kake neman mutumin arziki kona kirki Umar yakai, ko mahaifina da yakeyiwa Umar fad’a bawai dan ya yarda bane, dan matuk’ar yarda mun yarda da Umar.

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)

      ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

5

Sanu ahankali Cikin ikon Allah na samu gurbin karatuna anan University of Gombe, kullum k’orarin iyayen Mu shine suka inganta rayuwarmu tare da son faranta mana.ni da umar musamman sbd
, muguwar shak’uwar dake tsakanina dashi . dan duk inda ka ganni dole zaka ganshi, komai namu iri d’aya ake mana bbu wani bambanci atsakaninmu shiya wasu suke kiran mu ‘yan biyu, babu wani sirri na da Umar bai sani ba.
haka Nina babu wani sirrin sa daban sani ba. Sosai nake matsanancin kaunarsa tare da maidashi tamkar Dan uwana Na jini .yadda nake jin umar acikin raina ko kanina da muka fito ciki guda bana yi masa irin son da nakeyiwa umar ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button