
Kamar yadda ta saba yauma haka ta dafa abinci ta shirya ta fito, driver ya taso ta dakatar dashi had’i cewa Baba ka barshi ba damuwa yau da kaina zanyi driving, “Allah ya tsare, “Amin tace sannan ta shiga motar ta nufi gidan yarin.
Bayan tafiyar Mukhtar Zaid ya sha maganin aiko take k’irjinsa ya rik’e ya fara ganin bibbiyu juwa ta d’ebe shi yayi baya luuuu, da sauri aka sanar da police suka zo,a gigice aka kawo ambulance aka nufi asibiti dashi, ana saka shi a ambulance Lubnah na kawo kai, amma kafin ta fito har sun tafi, motor ta k’ara yiwa key tabi bayan su, sai da ya bari anzo tsakiyar dajin dai-dai wajen da Mukhtar yace masa sannan ya buga tsalle ya duro daga cikin motar yayi daji da gudu, da sauri Lubnah tayi parking tabi bayan Zaid amma kafin ta k’arasa har ya shiga motar Mukhtar, da sauri ta koma inda tayi parking, ta shiga mota ta rufa musu baya.
A wani k’aton fili Mukhtar yayi parking ya fito da sauri Zaid ma ya fito ya dafe k’irjinsa, glass d’in dake fuskarsa ya cire sannan ya yar gefe, a hankali ya tafa hannunsa sai ga Teemah ta fito daga bayan mota, fuskarta d’auke da murmushi direct ta nufi Mukhtar ta rungume shi ta manna masa hot kiss had’i da sakar masa k’ayataccen murmushi, a hankali ta juya ta kalli Zaid ta fashe da dariya had’i da cewa my heart, my Cweet husband ya kake kwana biyu bamu had’u ba ko?
Iya mummunan tashin hankali Zaid ya shiga take k’irjinsa ya shiga bugawa da k’arfi zuciyar sa ta shiga yi masa zafi had’i da k’ona, jinin sa ya tsinke, tsoro da fargaba suka shige shi, zuciyar ta harba had’i dayi masa tsalle kamar zata tsaga k’irjinsa ta fito, mak’ogwaronsa ya fara soya had’i da tuk’uk’in bak’in ciki bakinsa ya shiga fitar da tiriri, nan da nan gaba d’aya jikinsa ya d’auki rawa gami da kyarrrrma, a hankali ya d’ago kai ya kalle shi yace ” ya akayi ne best friend for ever, are you surprise?
MOMYN ZARAH
[21/01, 04:13] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
29
Gaban Zaid yaci gaba da fad’uwa yana dukan uku-uku tsoro da fargaba lokaci d’aya suka shige shi, babu abinda jikinsa keyi sai kerrma da tsoma yadda kasan wanda aka tsamo daga deep freezer cikin tashin hankali yake kallon Mukhtar da Teemah baki na rawa yace ” Friend ban gane ba dama Teemah na raye?
” not friend call me your enemy, a fusace Zaid yayi kan Mukhtar, cikin zafin nama Mukhtar ya zaro bindiga daga aljihunsa ya d’aga ya saita kan Zaid yace ” ka sake ka k’ara taku d’aya daga inda kake wallahi saina fasa kanka da wannan bindigar sakarai kawai, ka ja baya sosai a tsakani na dakai ka bada tazarar taku 30 a hankali Zaid ya ja baya, bindigar na saitin kan Zaid, Mukhtar ya fara magana.
” ni d’an mai gadin gidan ku ne, amma ka d’auke ni a matsayin d’an uwa, kuma masoyi, na taso ne a cikin talauci da k’uncin rayuwa hakan ne yasa tun ina yaro na tsani masu arziki na kuma mayar da masu kud’i a bokanan adawa ta, tun mahaifi na yana matashi yake yiwa mahaifinka bauta amma babu wani abu da kuka tsinana masa gai kyautar gidan zama da kayan abinci duk wata sai kuma kudin makarantar yara, dalilin dayasa kenan na fara tunanin naimarwa kaima mafita, tunanin dana fara yi shine yadda zan shiga jikin ku sosai.
“Hakan ne yasa ni shiga jikinka na kuma k’ank’antar da kai, na zama mage mai kwanciyar d’aukar rai, na kwantar da kai na, na shiga jikinku sosai na gama nasanin sirrinku, duk wasu halaye na daga sani masu kyau to ba nawa bane na Abraham ne haka ma duk wasu halayen Abraham daka sani marasa kyau to nawa ne, a zahiri shine d’an iska, amma a fad’iri nina ainahin mugun, nine na mayarda Abraham d’an iska, mazinaci, d’an shaye-shaye, saboda na kawar da hankalinku daga gano ainahin wanene ni.
“Ni na sanya k’iyayya mai k’arfi a tsakanin ku, dan matuk’ar kuna shiri kanku na had’e to ni bazan tab’a samun yadda nake so ba, take maganar Abba ta dawowa Zaid ” ku had’e kanku, ku zama tsintsiya mad’aurinku d’aya, dan idan kanku yana had’e babu wani mak’iyinku da zai samu nasara akanku”, Mukhtar yaci gaba ” rashin lafiyar da Abba yakeyi nine nayi mata poison injection nayi mamakin da har yanzu bai wula ba, sannan duk labarin da Teemah ta baka gaskiya ne, kuma nine MB d’in cikin labarin ta, MB yana nufin Mukhtar Barrister, sannan turai datace maka mun tafi tare shima da gaske ne, lokacin da mukaje Dubai ne, na tafi da ita, sannan karkayi mamakin jin acikin labarin ta tace MB matashin mai kud’i ne, haka ne dan duk satar da akeyi a gida ana zargin Abraham to ni ne.
“Kar in cika ka da surutu da yawa bari na baka labarin yadda muka tsara komai ni da matar ka kuma mata ta Teemah.
Da farko kamar yadda ka sani Teemah budurwa tace, kuma nine wanda ya kai ta wannan party, ni ne na kashe wutar hall d’in, kuma Teemah ce ta rungume ka bakai ka rungume ta ba, sanin irin zuciyar ka da kuma tsananin kishinka shiyasa mukayi amfani da wannan damar muka saka maka zargin Teemah a ranka, muka sanya ka kayi kanka da kanka mummunan furuci a bainar jama’a, sannan nasan har yanzu kana mamakin yadda duk ma’aikatan gidan had’i da matarka suka bada shaidar akanka ko?
” lokacin daka biyo Teemah parlor da gudu, ni ne na murd’a maka jijiyar wuyanka ka fad’i ka suma daga nan kuma muka baka giya ka sha ka bugu, sai Teemah ta baka wuk’a tace maka kayi ta binta da gudu kana cewa sai ka kashe ta, bayan nan kuma sai muka sai muka kwantar da kai, ita kuma Teemah sai nayi mata allurar bacci wacce zata iyayin tsawon sati d’aya tana bacci batare data farka ba, sannan na d’an yanke ta kad’an jini ya zuba ya d’ebi jinin na shafa maka a jikinsa.
Bayan police sun gama binciken su naje na karb’i Teemah da sunan za’ayi mata sutura, da naso na kawar da Abraham ma sai naga b’ata lokaci na zanyi a banza tunda ba d’an Abba da Ammi bane shi bashi da gadonsu dan a gidan marayu aka d’auko shi, dan Abba ya kawar da zargin mutane da kuma ku kanku a kansa shiyasa yace ko ya mutu kar a sake a raba masa gado, a babban gidan marayun dake garin Bauchi aka d’auko shi, ganin bashi da gado kuma dukiya da komai sun zama nawa shiyasa na kyale shi.
“Yanzu buri na ya gama cika, na gama mallakar gaba d’aya dukiyar Bature Family, gashi kuma na mallaki macen danafi so a duniya ya fad’a yana kallon Teemah,wallahi Zaid duk sanda ka kasance da Teemah wutar k’yayyarka k’ara roruwa take a zuciya ta, sai da ta tabbatar sau d’aya suka tab’a yin sex sannan hankalinta ya kwanta, am the younger riche in Africa, ya kalli Teemah yace ” kina da abun da zaki sanar dashi ne?
“No my life ai ka riga ka gama fad’ar komai kawai ka gama dashi, ya kalli Zaid yana murmushi yace ” sai mun had’i a rayuwa ta gaba sai wata rana, kafin Zaid yayi wani yunk’uri tuni Mukhtar ya sakar masa harsashi a k’irjinsa, ya k’ara sakar masa wani, sai da yayi masa harbi hud’u a k’irji sannan ya kyale shi.