
Baya Zaid yayi ya fad’i k’asa, sai da suka tabbatar ya mutu sannan suka shiga motar su sukayi gaba suka kyale shi anan, suna barin wajen Lubnah ta k’araso da sauri ta k’arasa inda yake, tana ganin cikin jini kuma ga bullet har hud’u sun fasa k’irjinsa ta fashe da kuka ta rungumo shi a k’irjinta, tana ihun kuka kamar ranta zai fita, a hankali taji zuciyar sa na bugawa, da sauri ta tallafo shi ta kwanta tasa kunnenta a dai-dai k’irjinsa taji zuciyarsa na bugawa a hankali da sauri ta mik’e ta fafa zarya a wajen tayi gabas, tayi yamma ta dawo tayi kudu da arewa, tana hange-hange ko Allah zai kawo wani ya taimake ta ya kama mata Zaid su saka shi a mota, dukta zare ta zama mahaukaciya ta gama fita daga hayyacinta, da gudu ta koma mota tana kuka.
Ringing wayarta ta shiga yi da sauri ta hau zazzage jaka dan ita tama manta da wata waya, hannunta na rawa ta d’aga wayar cikin kuka da rawar murya ta fara magana batare data bari taji kowaye ba, jin muryar ta yasa Abraham cewa ” kina ina Lubnah yanzu na sauka a Nigeria ina airport ko gida ma banje ba, cikin kuka ta fara yi masa magana ” please Abraham kazo karya mutu wallahi ya harbe shi a k’irjinsa har sau hud’u dan Allah kazo yanzu a gigece take yi masa maganar, shima cikin firgici yace ” what waye ya harben shin, kuna ina yanzu?
“Kinga yi sauri ki turo min location d’in inda kuke ta WhatsApp yanzu, “ok kawai ta iya cewa hannunta na rawa tayi mishi sending location d’in, ba’afi 15 minute ba sai gashi ya k’araso wajen da mahaukacin gudu kamar zai tashi sama, da sauri yayi parking ya fito baima bari motar ta k’arasa tsayawa ba,tana rungume dashi a k’irjinta tana ta fama rusa kuka ya k’araso bai jira wani abu ba ya sungume yayi cikin mota dashi, da sauri kamar zata hantsila ta mik’e tabi bayan shi, a site d’in baya ya kwantar dashi, da hanzari Lubnah ta shiga bayan ta zauna ta d’auki kansa ta d’ora akan cinyarta.
Gudu yake tsalawa kamar wanda zai tashi sama, ganin bai d’auki hanyar cikin gari kuma gida direct bane yasa Lubnah d’an tsagaita kukan ta ta kalle shi tace ” ina zamu ne, ba asibiti za’a wuce direct dashi ba, a d’an zafafe yace ” baki da hankali ne yaza’ayi mu kai shi hospital bayan kin san he is wanted, dole mu b’oye shi, guess house d’ina zamu je muyi jinyarsa acan harya warke, yana maganar ya tsaya a k’ofar wani madaidaicin gidan wanda shi kad’ai jal a dajin , tsarin gidan irin tsarin gidajen turawa dake tsakiyar daji a bakin ruwa, gidan mai kyau gaba d’aya gaban gidan an gina shi da glass ne, gidan ko get babu, ga wani katon ruwa daga gefe wanda tsuntsaye ke kewaye dashi suna bada kukan su mai dad’i.
Gidan babu wani bedroom ko parlor daban gaba d’aya a had’e, gefen dama aka tsara bedroom mai geshen kyau,mai d’auke da k’aton royal bed, gefen hagu kuma parlor shima mai shegen kyau wanda yaji royal chairs,sai d’ayan gefen kuma akayi kitchen, sai kuma bathroom & toilet amma shi a rufe yake, da sauri ya zagayo ya sungumi Zaid ya shiga gidan dashi ya kwantar dashi, ya kalli Lubnah yace ” kitsaya anan yanzu zanje pharmacy na siyo duk abinda ake buk’ata, kuma sai na biya hospital na siyo jini dan sai anyi masa k’arin jini, ya fad’a yana fita da gudu.
Wajen 1hr ya dawo, duk wani abu da ake buk’ata dan duba lafiyar Zaid ya siyo, haka ma kayan abinci duk da gidan babu abinda babu, ya biya gidan Zaid ya d’ebo musu kayan sawa shida Lubnah da sauran kayan buk’ata, da sauri ya shiga ya fara duba Zaid, sai da ya fara cire masa bullet d’in sannan, yayi masa allurai ya saka masa k’arin ruwa da jini, ya gama yi masa duk wani daya dace sannan.
Sosai hankalin Abraham yayi mummunan tashi ganin mummunan halin da tilon d’an uwansa yake ciki na rayuwa ko mutuwa, dan haka ya dage da bashi kulawa ta musamman ba dare ba rana, haka ma Lubnah ta shiga matsanciyar damuwa sosai ta rame ta fita hayyacinta kullum bata da wani aiki sai kuka da rok’an Allah ya bawa mijinta lafiya, ganin gashi har tsawon wata d’aya amma bai farfad’o ba Abraham zaune a gefensa hannunsa cikin nasa, ya k’ura mai ido yana zubar da kwallah, haka ma Lubnah tana zaune a gefensa sanye da zumbolelen hijab, hannunta rik’e da Qur’an tana karanta masa a kunne cikin muryar kuka, sannu a hankali ya fara bud’e idonsa yana kallan inda yake a hankali ya gama bud’e idonsa tarwai ganin yanayin da Lubnah da Abraham ke ciki ne yasa shi zubar da kwalla a ransa kuma yana tunanin irin soyayyar da d’an uwansa yake yi masa wanda yafi tsana da k’i fiya da komai da kowa a duniya.
Wanda aduk shekarun baya Zaid kallan mak’iyi yakeyiwa Abraham, shi a ganin sa Abraham yafi tsanarsa fiye da kowa a duniya ashe ba haka abin yake ba, ashe duk zaton da suyi masa na munanan halaye gami da d’abi’u ashe duk makircin Mukhtar ne wanda yafi so da k’auna wanda ya zab’e shi akan tilon d’an uwansa, wanda shi a tunninsa Mukhtar yafi son shi fiye da kowa da komai, ashe ba haka abin yake ba, a hankali yakai dubansa ga Lubnah matar da dakyar Ammi ta aura masa, Allah ya taimke shi bayyiwa Ammi musu ba, bai kuma biyewa san zuciyar shi yak’i yi mata biyayya ba, Lubnah ta cika ‘yar halak, mace mai hak’uri kunya, juriya, kawaici, ga rufa asirin mijinta da kuma auren ta.
Take yaji kunyarta ta shige shi abisa abubuwan dayayi mata na rashin bata kwananta da kuma hakk’inta, a hankali ya abubuwan da suka faru suka shiga dawo masa sababbi fil kamar yanzu aka yi su, take jikinsa ya d’auki rawa zuciyarsa ta fara bugawa da k’arfi, take ya shigo tuno abinda Teemah da Mukhtar sukayi masa, idonsa yayi ja, k’irjinsa ya shiga yi masa k’ona, wata irin mahaukaciyar k’ara saki tana sambatu da sauri Abraham da Lubnah wanda bama su san ya farka ba sai a lokacin sukayi kansa, ganin Abraham ya rungume d’an uwansa yana kuka ne yasa Lubnah ta zama dai-dai k’afafuwansa had’i da rik’o k’afafuwan nasa, Zaid ya mara sambatun da shi baima san yana yin sa ba ” wallahi koda zan rasa rai na bazan tab’a barin su ba, sun ci amanata sunyi min butulci, na yarda da su amma suka had’a min GADAR ZARE.
“amintattu nane sukayi silar jefani cikin wannan mawuyacin halin, ya k’ara fashewa da matsanancin ” wallahi koda zan rasa rayuwa ta bazan tab’a kyale su ba, yana maganar yana fisge-fisge, dakyar Lubnah da Abraham suka shawo kansa yayi shiru.
A hankali Lubnah ta taimakawa Zaid yayi wanka ya rama sallolin da ake binsa, dakyar suka samu yaci abinci, bayan ya gama ya nutsu Abraham ya kalle shi yace ” ZD wai meke faruwa ne, ni fa har yanzu ban san komai ba na kuma kasa fahimtar komai, an kira ina America ance nazo maza-maza wai ka kashe Teemah duk ba babu wata shak’uwa a tsakanin mu sosai haka kuma ban san halinka ba amma gaskiya nasan bazaka tab’a iya aikata kissan kai ba, a hankali Zaid ya d’ago kai ya k’urawa Abraham ido hawaye na zuba daga idonsa, yace ” kai dayake d’an uwan nane shiyasa duk da babu wata shak’uwa a tsakanin mu amma harka mahinci abinda zan iya da wanda bazan iya, daga na ya kwashe duk abinda Mukhtar yayi musu har allurar poison da yayiwa Abba, da yadda ya lalatawa Abraham rayuwa batare da kowa ya sani ba ya sanar dasu komai bai b’oye musu komai ba tas ya fad’a musu, illa maganar cewa Abraham bad’an Ammi da Abba bane ita kad’ai ya barwa ransa, idon Zaid na zubar wahaye yace ” Ab kuskure ne dai mun rigada munyi shi gaba d’ayan mu kuma dama sai da Abban mu ya fad’a mana, a hankali Zaid ya rik’o hannun Abraham yace.