
” please Ab karmu kuma maimaita irin wannan kuskuren karmu kuma bawa wani mahaluk’i damar shiga tsakiyar mu balle har ya samu damar raba, please mu had’e kanku mu zama tsintsiya mad’aurin mu d’aya kamar yadda Abba yace, ya k’ara sa maganar hawaye na kuma zubowa daga idonsa, da sauri Abraham ya rugume Zaid yana kuka shima yace ” lalle Mukhtar ya cika cikekken butulu, fasik’i, mugu, macoci, amma da sannu zai girbi abinda ya shuka, a hankali Zaid ya sassauta rungumar da Abraham yayi masa yace ” hmmmmmm bazan tab’a kyale har sai lokacin da sakayya zata fara aiki akan ba.
” To yanzu meye abinyi Zd?
Murmushi Zaid yayi yace ” Allah baya tab’a yin abu babu dadi tunda kaga bullet har hud’u sun huda k’arji na amma still ina a raye kasan akwai dalilin dayasa Allah ya barni a raye, tun da nasan ainahin waye Mukhtar bani da wani dayace na kawar dashi dan na rage mugun iri a doron k’asa, babu abinda ke cin zuciya ta sai wutar fansa, muddin Mukhtar da Teemah suna raye bazan tab’a kyale su suyi rayuwa cikin salama ba har sai na fansa akan su.
” a’a Zaid sai mun d’au fansa dai, dan wannan fansar muce mu biyu, shi ya koya min bariki amma ni kuma zan nuna masa makoyi yafi ma’iyi, wallahi sai mun sanya rayuwar su cikin tsananin uk’uba da k’unci had’i da matsanancin k’angin rayuwa………
MOMYN ZARAH
[21/01, 04:13] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
30
Murmushi Zaid yayi yace ” good brother, yanzu ta ina zamu fara? dariya Abraham yayi a karo na farko sannan yace ” bincike! ina nufin bincikensa zamu farayi mu bi diddiginsa, duk inda yasaka k’afarsa ya cire mu kuma sai mu maida ta mu, yama cewa mun zama inuwarsa, sai mun gama sanin inda ya nufa sannan sai mu fara d’aukar tamu fansar a kansa, “yawwa amma yanzu yaza’ayi musan inda yake?
“Tunda yanzu ya zama shahararren mai kud’i bazai tab’a b’uya a idon duniya ba, binciko shi abu ne mai matuk’ar sauk’in gaske, “kamar ya? bangane ba fa, “ok ina nufin inda ya nufa zamu fara sani, ” oh my God please kayi man bayani yadda zan gane, inda ya nufa kamar ya? “kai Zaid sai kace wanda ya samu matsala a kwakwalwarsa, haba ayi ta magana d’aya amma ka kasa ganewa, murmushi Lubnah dake gefe a zauna tana jinsu tayi sannan ta mik’e a hankali ta fara takuwa har izuwa wajen mijinta, cikin nutsuwa ta zauna kusa dashi ta dafa kafad’arsa ta kalle shi, shima idonsa na kanta, murmushi ta sakar masa sannan tace ” abinda Abraham yake nufi shine, ku fara sanin inda yake a halin yanzu ma’ana k’asar daya koma da zama a halin yanzu dan na tabbatar baya Nigeria saboda yana tsoran abinda zaije ya dawo.
“Kuma dole sai an samu mutum na jikinsa, wanda za’a had’a baki dashi, dan shima yasan zafin cin amana, kuma dole sai an fara shirya makirci da tuggu a tsakanin shi da Teemah ta yadda zamu raba kansu mu kawo zargi, kokonto had’i da rashin yadda a tsakanin su, ta haka ne zamu samu damar cika birin mu akan su, “gud ideas sister kin kawo shawara mai kyau, dama ance d’an gari kan ci gari, shi dai Zaid shiru kawai yayi ya k’ura musu ido yana kallonsu, Lubnah tace ” zan saka Dady na ya binciko min duk inda suke a fad’in duniyan nan, “ok kira shi ki sanar dashi, ba musu Lubnah ta mik’e ta nufi inda wayarta take, bugu d’aya Dady ya d’aga da sallama a bakinsa ta gaida shi, bayan sun gama gaisawa ne ta shiga kwararo masa bayanin duk abinda yake faruwa, cikin kad’uwa Dady yace ” lalle wannan yaron ya cika cikkeken butulu , makiri, kuma maci amana, dole a d’auki mummunan mataki akansa dan hakan yazamo izzina ga ‘yan baya masu hali irin nasa, “haka ne Dady shiyasa yanzu ma muke san sanin k’asar dayake, “badamuwa Auta ki bani nan da 1hr zan kira nayi muku bayani bayan na gama dubawa, “ok thanks dad ta fad’i dayi mishi sallama.
‘Yan sanda kuwa sai bincike suke haik’an babu dare ba rana dan gano inda Zaid yake sunje gidan shi sun bincika in an out amma babu ko alamar yazo gidan ma, haka ma sunje gidan su nan ma sunyi bincike amma basu samu komai ba, duk ma’aikatan gidan tun tara su sun bincike su amma babu wata kwakkwaran maganar kamawa balle su samu shaida, sosai hankali DSP Hassan yayi mugun tashi saboda a hannunsa case d’in yake, haka ma drivers d’in da suka d’auke shi yayinda za’a kai shi asibiti duk an kama su an tsare su ana ta bincike akan su dan ana zargin da sa hannun su kuma da had’in bakin su Zaid ya gudu ana tunanin ko an basu wasu mak’odan kud’i ne.
Bayan 1hr Dady ya kira Lubnah yake shaida mata cewar Mukhtar da Teemah suna Holland ya kuma fad’a musu ya fara gudanar da kasuwancin sa acan dan this week ma zai bud’e sabon Company a can, godiya tayi masa sannan ta aje wayar ta kalli Abraham da Zaid wanda gaba d’ayan hankalinsu na ganta jira kawai take ta gama wayar tayi musu bayani dan a k’agare suke matuk’a, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta shiga yi musu bayanin da Dady yayi mata, aiko wata uwar zabura Zaid yayi ya mik’e yana huci, jikinsa sai kerrma yake, take zuciyarsa ta shiga buga masa da k’arfin gaske, mak’ogwaransa yayi masa mugun d’aci ya juya ya kalli Abraham yace ” duk inda zaka samo mana Visa kayi in just 2 days, da sauri Abraham ya mik’e yace ” baka da hankali ne baka san yanayin da ake ciki bane yanzu kasan fa kai ko wanene, to idan ma baka sani ba gwara ka sani you are wanted, ta ko’ina nemanka ake a raye ko mace ka tsaya abi komai hankali, tsawa Zaid ya dakawa Abraham yace ” koma meye kuma koma wanne hali zan shiga babu ruwanka kai dai kawai kayi k’ok’arin samo mana visa ” you are totally mad Zaid, idan kai baka cikin hayyacin ka ni ina cikin nawa hayyacin, da harzuk’e Zaid ya shak’i Abraham, ganin haka yasa Lubnah saurin mik’ewa tayi wajen Zaid, dakyar ta janye shi, a hankali ta zaunar dashi akan sofa ta mik’e ta nufi fridge ta d’auki masa ruwan sanyi ta bashi ta bawa Abraham , sai da sukayi kusan 15 minutes babu wanda yacewa k’ala.
A hankali Lubnah ta numfasa ta d’ago kai ta kalle sannan tace ” da farko matuk’ar kuna san samun nasara a gaba d’ayan rayuwarku sai kun cire wannan zafin zuciyar had’i da rashin jituwa a tsakanin ku, na d’auka iya abinda ya faru yanzu kad’ai ya isheku izzina bama ku ba harga wasu, ta kai dubanta ga Zaid tace ” kaifa Mukhtar yayiwa bayanin komai ya kuma ce maka da kuna shiri a tsakanin ku da bai samu nasara ba, gaskiya yanzu ya kamata ace kun san Annabi ya faku, ku had’e kanku ku cire wannan zafin zuciyar dan yazo lokaci ne na zumunci da k’aunar juna ya kamata ace kunyi watsi da duk abinda ya faru a baya, nan dai taitayi musu nasiha mai ratsa jiki da karya zuciya ta kuma rink’a kawo musu misalai had’i da kawo musu Hadisai da ayoyin Quran, sosai ta kashe musu garkuwar jiki, take suka manta da duk abinda ya faru, Zaid ko k’ura mata ido kawai yayi yana kallanta yana kuma ganin baiwar kyau, hankali, nutsuwa, tunani ga kuma tarbiyya, haka nan kawai ya rink’a jin farin ciki, a k’ark’ashen zuciyar sa kuma yana yiwa Allah godiya da samun mace ta gari irin Lubnah.