GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan komai ya lafa tace ” bari na kira Dady in tambaye shi idan ma zayyiyo ko bazayyiyo ba shi zai sanar damu, bayan ta kira Dady tayi masa bayani yace ” dole sai Zaid ya canja passport da kuma, amma zayyi duk abinda ya kamata, godiya ta kuma yi masa had’i dayi masa sallama, sannan tayi musu bayani, sannan tace ” Abraham ya kaiwa Dady password d’insa dan ita nata yana hannunsa, murmushi yayi mata yace “ok badamuwa in sha Allah yau da daddare zan kai masa, ya fad’a yana mik’ewa, har yakai bakin k’ofar fita unexpected yaji Zaid yace ” I’m sorry Brother, a hankali ya juyo ya kalle shi had’i sakar mishi murmushi yace ” never mind.

Tun daga lokacin babu wani abu daya k’ara shiga tsakanin Zaid da Abraham sai farin ciki da k’aunar junansu da suke mugun yi kowannen su baya k’aunar yaga ko k’uda ya tab’a masa d’an uwansa,balle kuma su suyiwa junan su, kasancewar Abraham ya kama ya tsare ne ya hana wani abu shiga tsakanin Lubnah da Zaid dan duk inda Zaid yake to Abraham na tare dashi, ga gidan mai tsarin turawa, yayinda da Dadyn Lubnah keta faman k’ok’arin nemar musu Visa dan tafiya Holland, Allah yasa cikin satin aka samu visar ta fita dan haka babu wani b’ata lokaci suka hau shirin tafiya, ranar tafiya Dady ne ya tsara musu komai, shi Zaid yayi shigar larabawa ya saka jallabiyya da hijami yayi shigarsa tsaf su haka ma Lubnah ta saka abaya da tarha (mayafin abaya) had’i da k’attuwa (Nik’ab) ta rufe jikinta tsaf, shi kuma Abraham yayi shigar Pakistan, hakan yasa basu samu matsalar komai ba, har jirginsu yayi landing a Holland.

Kasancewar da tskar dare suka sauka ne yasa su yanke shawarar fara zuwa restaurant kafin su wuce hotel d’in su, suna isa wake cikin za’a suka same taxi driver d’an Nigeria da fara’a ya tare su, ganin shigar da sukayi ne yasa shi yi musu turanci, umarni Abraham ya bashi daya kaisu Nigerian restaurant a hankali ya juyo ya kalle su yace ” are you Nigerian? wata uwar harara Zaid ya watsa masa hakan daya gani ne yasa kame bakinsa yayi shiru, dan yanzu kwata-kwata Zaid bashi da yarda, ya daina yarda da mutane.

Murmushi Abraham yayiwa driver yace ” yes, but why do you ask? “Because am Nigerian too, “ok Abraham, sai kuma ya juya ya kalle shi yace ” your tribe please? murmushi driver yayi sannan yace ” am Hausa fulani what about you, dariya Abraham yayi yace ” nima haka ya bashi amsa da hausa, aiko da sauri driver ya juyo yace ” haba kwata-kwata bakuyi kama da hausawa ba, ko kuma kunzo wajen bikin bud’e a Nigerian Company ne matashin mai kud’in nan wanda ake yiwa lak’abi yaro da kud’i?

Murmushi Abraham yayi yace “wake nan? Driver yace ” MUKHTAR yana ambatar sunan Mukhtar take jikin Zaid ya d’auki rawa, ya harzuk’o da sauri Lubnah tasa hannu ta mai dashi had’i dayi masa rad’a a kunne, ” Lah aiko kamar kasani wajen taron muka zo ya akayi ka sani? “ai tunda aka saka ranar bud’e company kullum sai munyi bak’i, kuma ma aboki na ne babban yaran sa, da tare muke aikin taxi driver dashi, shine Allah ya taimkesa ya samu aiki a gidan sa, aiko take wani irin mugun farin ciki ya lullub’e su, cikin dabara Abraham yace ” kai amma yayi za’a amma nasan yanzu dayake shi ya samu duniya ya manta da kai ko?

Dariya driver yayi yace “nine fa baban abokinsa sanda ma yazo nan garin a waje na ya fara zama, kuma babu yadda bayyi da ni akan zai samar min aiki a gidan ba ni ne naki, “mai yasa? haka nan kawai, ni da nama kusa komawa gida, idan na samu aikin naji dad’i bazan koma Nigeria yanzu ba, ” kuma har yanzu kuna gisawa dashi abokin naka bai wutak’anta ba? ” A ‘a shi ba haka yake ba, mutum ne mai kirki ga tsoran Allah, kwata-kwata ya tsani zalunci da azzalumai, haka dai Abraham yai ta jansa da hira yana kuma bugar cikinsa har suka k’arasa restaurant d’in.

Bayan sun gama cin ya kai su hotel, ya sauke musu kayan su, ya zaro card ya basu yace ” duk sanda suke san driver suyi mishi magana, Abraham yana dariya ya karb’a, bayan sunje d’aki sunyi wanka sun shirya Abraham ya same su a d’akin su, a zaune shima zaman yayi sannan ya kalli Zaid yace ” ka gani ko da kana neman yi masa wulak’anci, ajiyar zuciya Zaid ya sauke had’i da cewa yanzu meye abinyi ? ” to ni dai a shawara ta mu kira shi, shida abokin nasa muyi magana da su, tunda dama Lubnah tace dole sai an samu na jikinsa, “haka ne to amma kai a ganin ka me zamu gaya musu? “Gaskiya cewar Lubnah taci gaba da cewa ” ita gaskiya d’aya ce daga ita kuma sai b’ata, idan ka dubi mutumin nan sosai zaka san mutumin kirki ne kuma baka ji abinda yace akan abokin nasa ba, ni dai a ganina mu sanar dasu gaskiya kawai, idan sunga dama su taimake mu, idan kuma sunk’i sai Allah ya dubi gaskiyar da muakayi ya taimake mu, duk sukayi shiru kana daga bisani suka sauke ajiyar zuciya, “ok badamuwa hakan ma yayi cewar Zaid, sannan ya kalli Abraham yace ” ka d’auki number sa ajikin card d’insa ka kira shi kace yazo shida abokin nasa, “ok kawai Abraham yace sannan yayi dialing number bayan ya d’auka ne ya sanar da shi suna san ganin su.

Washe gari su Zaid zaune tare da driver da abokinsa, bayan su gama sanar da su komai, sosai suka jinjina al’amarin sannan sukayi musu rantsuwa akan zasu rik’e musu alk’awari zasu kuma basu duk taimakon da su, sannan suka rabu bayan sun gama tsara komai had’i da shirya komai.

Washe gari Ali abokin driver ya samo wata kyakykyawar budurwa ya had’a baki da ita ya sanar mata abinda yake tayi masa, ba musu ta amince, bayan kwana biyu ta kawo masa dukkan abinda ya umarce ta, ya karb’a yana murmushi sannan ya biyata iya adadin kud’in da sukayi akan zai bata yayi mata godiya.

Ranar taron bud’e Nigerian Company hall yacika mak’il da jama’a ciki kuwa harda su Zaid, Abraham, anyi masifar kashe mak’udan kud’i wajen tsara hall da kuma kayan ciye-ciyen dake gaban jama’a dan motsa baki sai da aka gama ciye-ciye sannan mc yayi sanarwar cewa ga uban taro nan da matarsa, take Mukhtar da Teemah suka bayyana sunsha kwalliya da shegun kaga iri d’aya fuskarsu d’auke da murmushi hannunwansu sark’e dana juna, suna shigowa kowa ya mik’e amma banda Zaid da tuni zuciyar sa ta kama da wuta, jama’ar dake wajen suka shiga yi musu tafa, duk inda sukayi masu camera da ‘yan sai d’aukar su pics suke, bayan an gama komai, komai ya kamla Teemah da Mukhtar suka shiga ferri car d’in su sukayi gida, a hankali idris (taxi driver) ya take musu baya ya rink’a bin su a baya har suka isa gida, daga Zaid har Abraham ba k’aramin rud’ewa sukayi ba dan ganin irin mahaukacin gidan da su Mukhtar ke ciki, suna tsaye suna kallonsa sanda get d’in ya bud’e kansa, suka shiga gidan, Mukhtar da kanshi ya zagayo ya bud’ewa Teemah k’ofa ya d’auke ta cak yayi ciki da ita, da k’arfi Zaid ya rintse idonsa saboda ganin irin rayuwar farin cikin wad’anda yafi tsana a duniya sama da kowa sukeyi.

A hankali Abraham ya dafa kafad’arsa, tare da bawa idris umarnin ya maida su hotel, tun daga wannan rana su Zaid suka zamewa su Mukhtar inuwa dan duk inda suka shiga suna biye da su a baya, har suka gama sanin sirrin su kaf.

Ranar Sunday Teemah ta shirya zata siyayya a mall ta kalli Mukhtar tace ” please dear ka raka ni shopping please yau ma karka ce baka da time, rungumo ta jikinsa yayi yace ” am sorry my love ina busy yanzu haka ma, amma in sha Allah next week I promise i will spend all my weekend with you, murmushi yak’e kawai tayi ta mik’e dan idan da sabo ta riga da saba da halin Mukhtar kullum ace mata yana busy yake kwata-kwata baya bata lokacinsa, a halin yanzu bata da wata damuwa data ce na rashin bata lokaci, bata k’ara bi ta kansa ba ta fita abinta, driver ta bawa umarnin ya kaita inda ya saba idan zatayi siyayya, ba musu yaja motar, bayan ta gama siyayyar ta fito ne su Zaid dake lab’e a cikin mota ya umarci Ali dacewa yi sauri gata can, da hanzari Ali ya fita, yayi kamar bai ganta ba, ya nufi k’ofar shiga mall d’in da fara’a fuskar Teemah tace ” a’a su Ali ne murmushi yayi mata yace ” eh nine amma please kiyi hak’uri dan ban gane mai magana ba, “Fateema ce matar Ogan ka Mukhtar “matarsa kuma ya akayi kika zama matarsa bayan ya gaya min shi bashi da aure?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button