
Da k’arfi k’irjinta ya buga ta kalle shi tace ” kamar ya? yace ” eh shi da kansa yace “min bashi da aure har nake tambayarsa to ke fa, sai yake ce min ke karuwa ce wacce ke kanki baki san asalinki ba, yana dai taimaka miki ne kawai kafin burinsa ya gama cika akanki harma yake ci min wai kin tab’a kashe mijin ki sunanshi zadi kowa, wai mai zayyi da mace maci amana kamar ki, wasu siraran hawayen ne suka shiga zubowa Teemah a ranta tace tabbas maganar nan daga bakin Mukhtar ta fito saboda duk duniya babu wanda san wad’an nan maganganun sai shi da ita kawai.
Wato shiyasa baya san fita da ita, shiyasa yake yi mata wasu abubuwan data kasa gane kanshi, ganin haka yasa Ali yin kalan tausayi kamar da gaske yace ” please ki rufa min asiri karki sanar dashi saboda zai iya korata daga aiki kuma wannan aikin dashi kad’ai na dogara,kuma karki damu in sha Allah zan binciko miki komai, kai kawai ta iya gyad’a masa ta shige mata driver yaja, suna cikin tafiya , motar su Zaid tasha gaban motar su Teemah driver ta ya taka burki da k’arfi k’uuuuuuuuu tsorace Teemah wacce keta faman sharar kwalla ta d’ago kai tana duban gaban ta gabanta ne yayi mugun fad’uwa jikinta ya d’auki rawa a matuk’ar firgice take bin shi da kallo, shima a tsorace ya ya bito daga motar su a d’an firgice jikinsa sai rawa yake alamar tsoro da sauri ya bud’e motar ya figi hannun Teemah da gudu yayi wani uncompleted building da ita………
MOMYN ZARAH
GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
31
Idris driver na zuwa uncompleted building d’in da ita ya tsaya cikin alamar tsoro da firgici had’i da mummunan tashin hankali ya fara magana ” Hajiya kin tab’a taimako na dan haka bazan tab’a bari ina gani wani mummunan abu ya same ki ba, da sauri yasa hannu a aljihu ya zaro memory card ya mik’a mata yace ” gashi idan kinje gida ki nutsu ki gani kinji duk shirin da Mukhtar keyi a kanki yana ciki, sannan ya k’ara da cewa ” a kowanne lokaci kina iya jin ance maki na mutu to ba mutuwar Allah da Annabi bace dan Mukhtar yana neman rayuwata akan wannan memory, yana kaiwa nan bai tsaya ya jira abinda zata ce ba ya fita da gudu a matuk’ar firgice, a tsaye ya barta tana ta zancen zuci yayinda da hawaye sai ambaliya yake yi a fuskarta, dakyar ta iya jan k’afarta zuwa inda mota take ta shiga, koda suka isa gida a parlor ta iske Mukhtar bata tsaya bin ta kansa ba ta shige d’aki had’i da danna key.
Jikinta na rawa ta saka memory a wayarta ta kunna ta fara kallon abinda ke cikin, iyakar tashin hankali kan Teemah ta shige shi, jikinta ya shiga rawa had’i da kerrma cikin tsoro da mummunan tashin hankali taci gaba da kallon video, Mukhtar ta gani tsirarar Allah yana aikata zina da wata zankad’ed’iyar budurwa bayan sun gama aikata masha’arsu budurwar ta kwanta a saman k’irjinsa tana shafo fuskarsa a hankali ta d’aga kai tana duban sa, ido d’aya Mukhtar ya kanne mata yace ” ”yan mata ya akayi ne?
Murmushi tayi had’i da yin wani farrr da ido sannan tace ” yanzu duk irin soyayyar nan da mukeyi amma bazaka aure ne ba? “Inji wa yace bazan aure ki ba? “gani nayi da ido na ai ba sai an fad’a min Teemah zaka aura ba, “what Mukhtar yace had’i da mik’ewa zaune yana kallanta yace ” God forbid na aure ni wallahi ko mata sun k’are a duniya ni kuwa mezanyi da ita, wanne dare ne jemage bai gani ba, tun Teemah tana 14yrs nake kusantarta, haba ke ko abinci ne ai yaci ace ka gaji dashi haka, nayi amfani da ita ne dan cikar burina, dan ni babu abinda bazan iya akan kud’i ba, ke ni in tak’aice miki magana idan ta kama ma na kashe Teemah to tabbas zan kawar da ita daga doran duniya abu mai sauk’in ne na tsinke mata numfashin ta matuk’ar naga zata bani ciwon kai, ” a firgice budurwar ta d’ago tana kallan Mukhtar tace ” kai my dear yanzu zaka iya kashe Teemah?
Murmushi yayi irin nasu na cikakkun ‘yan bariki sannan yace “ke nifa tunda nake a duniya ban tab’a ganin mace irin Teemah, shegiya mahaukaciya kawai ita in banda bata da cikekken hankali yama za’ayi tayi tunanin zan aure ta bayan naga irin abinda tayiwa Zaid ni karan hauka ne ya cije ni zan aure ta, ni ma idan ta samu wani wanda tafi sanshi akayi na abu mafi sauk’i ne tayi min irin abinda tayiwa tsohon mijinta.
“To yanzu meye target d’inka akanta? shiru Mukhtar ya d’anyi sannan ya kalli busurwar yace ” kinga dai har yanzu ban bata kasonta ba, ina lallab’a ne dan mu rabu lafiya kin san fa halin karuwai, idan ta gane mai nake nufi da ita komai yana iya faruwa, dan haka nake son tsara komai a hankali, ta yadda bazata tab’a fahimtar komai ba, wani mahaukacin kuka Teemah ta saki had’i da buga wayar da bango aiko take wayar ta tarwatse, durk’ushewa tayi a wajen tana wani irin mahaukacin kuka mai cin rai, sai da tayi mai isarta sannan ta mik’e ta shiga bathroom ta watsa ruwa, ta canja kaya, ta zube a gado ta fara tunanin neman mafita, dan yau Teemah ko parlor bata fito ba balle tabi takan abinci.
Takai 3hrs tana tunanin ta inda zata b’ullowa Mukhtar inda daga k’arshe tunaninta ya tsaya akan ta nemi ABRAHAM, batare da sake tunanin komai ko wani kokonto ba ta mik’e ta nufi parlor inda Mukhtar ke zaune, a zaune ta iske shi a gaban system, k’ok’arin saita kanta ta fara yi kafin ta isa inda yake fuskarta a sake, a hankali ta rungumo shi ta baya ta d’ora hab’arta akan kafad’arsa ta shiga hura masa iska a kunne tana yi masa wani irin salo mai wuyar basarwa, a hankali yasa hannuwansa ya juyo da ita, a d’an firgice ya zaro idonsa waje yace ” my life ya haka kuka kikayi meya sameki? Murmushi tayi masa had’i da d’an yamutsa fuska tace ” kai na ne kemin mugun ciwo, amma karka damu nasha magani ma, mik’ewa yayi tsaye da ita a hannunsa ya koma kan sofa 3 sitter ya zauna yana kallan cikin kwayar idonta yayinda wutar k’aunarta yake sake roruwa a zuciyar sa, take yaji zai iyayin komai akan Teemah zai kuma rabuwa da kowa akanta, babu koma abinda bazai iya yi ba matuk’ar zai sanya ta cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
A hankali ya had’e bakin su ya fara tsotsar bakin ta cikin kwarewa, bakinsa ya zame daga cikin nata yace ” dear ince dai bani na saka miki ciwon kan ba ko? murmushi tayi masa batare data ce komai ba, ganin duk ya rikice mata yasa ta mik’ewa da sauri ya k’ara mai da ita jikinsa ya cigaba da rod’a mata jiki, tasan idan ta tsaya bazai tab’a kyale taba sai yayi koda damba ne yasa cewa ” please my heart ka kyale ni wallahi bana jin dad’i yau, yanzu ma aran wayarka nazo ka bani in kira layi na, na rasa inda waya ta ta fad’a na nema harma gaji, rinannun idanunsa ya d’ago ya kalle wanda dama idan jarabarsa ta tashi haka yake komawa in few minutes, murya can k’asan mak’ogwaro yace ” please ki taimake ni my life wallahi nakai mak’ura wajen buk’atar ki, kin san daga wajen ki ne kad’ai nake samun nutsuwa, ke ce duniya ta, ina sanki fiye da kowa da komai aduniyar nan ta mu, wallahi zan iya yin komai matuk’ar zai saki farin ciki, ido kawai ta k’ura masa a ranta kuma tana jinjina girman munafurci irin na d’a namiji, kai maza munafukai ne duk zaman da zakayi dasu baka isa ka gane inda suka dosa ba, sai dai muyi ta addu’a.