
Ganin ta k’ura masa ido kuma da gani zancen zuci take yasa shi hura mata iskar bakinsa a fuska yace ” ko ba ki yarda bane ki gwada yanzu ki gani, murmushi yak’e tayi masa, sannan tace “ya za’ayi nak’i yarda bayan na gani da ido na ni ganau ce ba jiyau ba, ta fad’a tana k’ok’arin mik’ewa tsaye, yasa hannuwansa ya sake maida ita jikinsa ya rungume ta tsam a jikinsa yana mai da numfashi sama-sama.
Fuska ta b’ata tace ” nace maka fa bani da lafiya kuma ai sai da lafiya ake komai ko? kayi hak’uri man na d’an wani lokaci na ji sauk’i mana, ido ya k’ura mata yana aiyana wani abu a ransa sai kuma yace ” ok badamuwa, ya sake ta da sauri ta mik’e had’i da d’aukar wayarsa dake kan center table, tana shiga bedroom d’inta ta danne key sannan ta zauna a bakin gado ta shiga neman number Abraham tana yin searching taga number hannunta na rawa da d’auki number tayi serving sannan tayi delete number daga wayarsa sannan ta mik’e ta mayar mishi da wayar bata ko kalli inda yake ba ta dawo bedroom ta shirya tayi ficewarta.
Sai da ta samu wani k’ayataccen garden ta zauna ta nutsu sannan tayi dialing number Abraham, su Abraham na zaune suna tsara next target d’in su, su basu tab’a tunanin Teemah zata nemi Abraham ba, wayar sa ta fara ringing, ido ya k’urawa number na d’an wani lokaci sannan ya kalli Zaid da Lubnah da su Idris yace ” bak’uwar number da sauri Zaid ya zaro ido yana kallo wayar, ya kalli Abraham yace ” pick it, wayar na gaf da tsinkewa ya d’auka Teemah najin anyi picking ta d’auke ajiyar zuciya had’i da cewa ” hello Teemah ce matar Zaid da sauri Abraham yasa wayar a hand free yayi musu nuni da hannunsa da suyi shiru yace ” bana ji wake magana please, kamar a mafarki Zaid yaji muryar Teemah tace ” Teemah ce matar Zaid, please ka tsaya muyi magana dakai, yanzu kana ina?
Kallan Zaid yayi, Zaid yayi masa nuna dayace yana America, da sauri yace ” ina America, “ok please idan zaka samu dama kazo Holland ina so muyi magana dakai, ” wacce irin magana ce wacce bazamu iya yinta a waya ba?
“Maganar tana da mahimmanci sosai “ok ki fara sanar da ni idan naga takai nazo sai nazo, cikin rawar murya tace “akan Zaid da Mukhtar ne, kafin Zaid ya mutu ya mallakawa Mukhtar gaba d’aya dukiyar ku, shine nake so mu d’ana k’arfi da k’arfe mu k’ato duniyar, da sauri Abraham ya dawo cikekken d’an barikinsa kamar da yace ” wow kin san ni fa akwai san kud’i sai dai ni duk san kud’i na ina da rok’on amana, inda magana ce ta kud’i yauma ina biyo jirgin dare, kin ni mayen naira ne, murmushin farin ciki tayi sannan tace masa ” amma ina da sharad’i, cikin k’aguwa yace ” fad’e shi komaye zan yi, “ok da farko raba dai-dai zamuyi ma’ana 50/50.
“Ah indai wannan ne ai mai sauk’i ne, kefa kika zo mana da business d’in ya za’ayi nak’i, karki damu indai wannan na yarda na kuma amince, ” ka bari mana na gama sanar dakai sharud’an, “ok ina jinki, sai da tad’anyi jimmm sannan tace ” sharad’i na biyu shine bayan komai ya kammala dole ka aure ni, ta fad’i maganar batare da wani tsoro ko fargaba ba, duk iskancin Abraham sai da gabansa yayi mummunan fad’uwa da sauri ya kalli Zaid, shima Zaid kallo d’aya zakayi masa kasan ya shiga firgici amma duk da haka ya daure yayiwa Abraham alama daya ce eh cikin rawar murya Abraham yace ” gud idea kinga sai muyi tacin duniyar mu da tsinke ko?
Murmushi jin dad’in amincewarsa tayi sannan tace ” ok yanzu yaushe zaka zo, “yanzu ma zan tashi na yanke ticket, “ok to idan ka isa ka kirani sai nazo Airport na d’auke, “ok badamuwa gani nan, yana aje wayar ya sauke ajiyar zuciya mai k’arfin gaske yana kallan su Zaid, Zaid yace ” ba bata lokaci idan kun had’a ka gaya mata ta san yadda zatayi ta had’a gaba d’ayan takardun sannan tabugar dashi ta bashi yayi singing da zarar yayi singing shikenan duniya ta dawo hannun masu ita, sai kuma musan meye abinyi a gaba.
Kamar yadda suka tsaka haka ce ta kasance, wajen 3:00am yayi mata waya yace gashi a Airport ya k’araso, da sauri taje ta d’auke takai shi wani tsadadden hotel, suka d’anyi hira, acikin hirar ne Abraham ya fada mata tasa Mukhtar yayi singing akan takardun, dan baya son su bata lokaci so yake kawai ya mallake ta, murmushi tayi masa tace “karka damu gobe da safe zan zo maka da su, tana fita ya kira su Zaid ya sanar musu yadda sukayi da ita, washe gari Teemah ta bugar da Mukhtar da giya ta saka shi gaba ta rink’a yi masa kwarkwasa tana d’auke masa hankali had’i da rod’a masa jiki da salonta irin na ‘yan bariki, aiko take ya rud’e ya zauce, ganin haka yasa ta fito masa da duk takardun ta cikin wata irin murya tace “yi singing ba musu ya rink’a yi singing a duk inda ta umarce shi, har ya gama yana gamawa ta hankad’e shi gefe ta mik’e, wayarta ta ciro tana sanarwa da Abraham cewar komai ya kammala da sauri yace tazo hotel din data sauke shi.
Ba’afi 30 minutes ba ta k’ara so hotel d’in, kai tsaye ta danna kai d’akin, tana shiga ta iske shi zaune akan sofa yana busa sigarinsa da sauri ta k’arasa inda yake ta manna masa kiss a fuska tace ” burinmu ya cika yanzu saura me? da sauri ya mik’e yace ” kai haba, batayi mishi magana ba ta bud’e jakarta ta ciro takardun ta mik’a masa hannunsa na rawa ya karb’a ya fara dubawa sai da yaga komai ya cika sannan ya d’ago yana yi mata murmushi yace ” komai ya kammala amma shi Mukhtar fa? “Mukhtar kuma ai ban bar mishi komai ba wallahi dan har takardun account dana kadarorinsa dake Nigeria duk na had’o yanzu dashi da matsiyaci mai kwanan kasuwa duk d’aya dan ban barshi da ko sisi ba, dariya suka saka a tare sai da sukayi mai isar su sannan ya kalle ta yace ” ki bar takardun nan a hannuna gobe in sha Allah ni da kai na zanzo har gidan daga nan sai mu sanar masa Komai, “ok badamuwa kawai tace.
Tana fita su Zaid dake lab’e a toilet suka fito, Abraham ya mik’a masa takardun yana murmushi hannun Zaid na rawa ya karb’a ya k’urawa takardun ido, sai hawaye sharrrrr a hankali Abraham ya mik’e daga inda yake zaune ya koma kusa da Zaid ya shiga share masa hawayensa ” karka damu Zd ita duniya inda ta halak ce bata tab’a guduwa tabar mai ita har abada kota tafi sai ta dawo, wannan gumin Abban mu ne na halak, wanda yasha fafutuka da tad’i tashi cikin sanyi, zafi, damuna ya tara ta.
Sosai Abraham ya lallashi Zaid ya kuma kwantar mishi da hankali,
Abraham ya kalli shi yace ” ya maganar su DSP sun taho “eh sun taso tun jiya yau zasu k’ara so, “ok shida waye zasu zo, “shi da alk’alin daya yanke hukuncin, da lawyer gomnati, sai DSP “ok Allah ya kawo su lafiya “hope dai an tsara komai yadda ya kamata “eh karka ji komai.
tun lokacin da Teemah ta kira Abraham suka yanke hukuncin jiran DSP da sauran wand’anda case d’in ke hannun su dan suzo su gani da idon su
Tsakar dare jirgin su DSP yayi landing a Holland, Abraham ne yaje ya d’auko su daga Airport ya sauke a lafiyayyen hotel cikin karamci da girmamawa, Washe gari tun 8:30am Zaid, Abraham, Lubnah, Idris, Ali, suka d’unguma sukayin gidan su Teemah sai wajen 9:30 sannan suka fito, Teemah daga ita sai rigar bacci shi kuma sai boxers direct dinning table suka nufa dan basu lura da su Zaid, Teemah ta d’auki spoon zata zata kai bakin ta idonta ya sauka akan Zaid wanda ke sanyi cikin wani d’anyen farin yadi fari sol, kyansa ya k’ara fitowa sosai yayi so fresh dashi fuakar nan sai kyalli take, ya had’e k’afa, gefansa ga Lubnah wacce kamar zata shige masa cikinsa, d’aya b’arin ga Abraham shima sanye da kaya irin na Zaid sunyi anko, sai su DSP wata mummunan kwarewa tayi, cikin zarana had’i da firgici ta mik’e tsaye da sauri Mukhtar ya mik’e tsaye shima yana tambayar ta “meye?