
Kasa yi mishi magana tayi illa nuna kawai da take masa da hannunta da inda su Zaid ke zaune a hankali ya kalli inda take yi masa nuni da hannunta, gaba d’aya idanuwansa ne sukayi yo waje kamar zasu fad’o k’asa saboda tsabar tsoro da razana, ya kasa magana illa jikinsa kawai daya d’auri rawa, take zuciyar sa ta shiga bugawa da k’arfi, a hankali Zaid ya mik’e yayi tattaki har zuwa inda suke yace ” friend oh! you ask me to call you my Enemy right?
Ai take fitsarin da Mukhtar ke dannewa ya kufce masa sai zarrrrrr fitsarin Zaid ya bi da kallo had’i dayin murmushi sannan yace ” da sauri haka my enemy ai ka bari ma mu gaisa ko, gashi nazo har gidan ka tun safe bako breakfast ya fad’a yana zama akan d’aya daga cikin kujerun dunning d’in ya kalli su Abraham da DSP yace ” bissimillah kuzo mu ci abinci……..
MOMYN ZARAH
GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
32
Murmushi kawai DSP yayi had’i da girgiza kansa dan ba k’aramin burgeshi salon Zaid yayi ba, a hankali duk suka mik’e suka nufi dinning table d’in, cikin kwanciyar hankali Zaid yake cin abincin sa batare da tsoro ko fargabar komai ba, Mukhtar da Teemah na tsaye jikin su sai kerrrrrma yake, zuciyoyin su sai bugawa suke daka gansu kasan suna cikin mummunan tashin hankali.
Sai da yaci ya k’oshi sannan ya tsame hannunsa ya zari tissue ya goge bakinsa yana mik’ewa tsaye, cikin tak’ama da isa yake tafiya har ya isa main parlor gidan, zama ya kuma akan yi akan sofa had’i da d’ora k’afa d’aya kan d’aya, ya kai wajen 10 minutes sannan su Abraham suka gama suma suka dawo kusa dashi suka zauna, ganin har not kacin su Mukhtar na tsaye k’em kamar an dasa su basu da alamar motsawa ne yasa shi cewa “ku zo zauna muyi magana ya fad’a batare daya kalli inda suke ba.
Cikin mutuwar jiki suka tako parlor a sofa d’aya suka zauna kusa da juna, murmushi Zaid yayi had’i da k’ura musu ido yace ” kana mamakin yadda ka fasa k’irji na da bullet har hud’u ban mutu ba nake raye har yanzu ko? “Ina so kasan mutuwa da rayuwa dukkan su a hannun Allah suke, babu wanda ya isa ya kashe wani face kwanakin sa sun k’are,haka ma babu wanda ya isa ya raya wani sai idan yana da sauran numfashi a gaba, wannan kad’ai ya isheka izzina ka kai ni dokar daji inba babu wani d’an Adam dazai zo balle ya ganni harya taimake ni, amma dayake Allah gagara buwayi ne sai gani a gabanka yanzu, Mukhtar ya kamata kasan, mutuwa da arziki da kuma talauci duk a hannun Ubangijin komai da kowa yake.
“Duk yadda mutum yaso dayayi arziki bai isa daya azurta kansa ba har ya idan Allah yayi nufin hakan, kamar dai yadda ya faru dakai, acikin d’an k’ank’anin lokaci ka shahara kayi suna a duniya ka zama number 1 younger rich in Africa, har jiya iyanzu kana da wannan muk’amin amma dayake shi Allah ba azzalumin sarki bane sai gashi yanzu ka zama the jobless, poor, useless, dan yanzu ka zama cikekken talaka kuma matsiyaci abinda kafi tsana a rayuwarka yanzu zayyi maka sallama ya shigo rayuwarka dan shine zai zama babban abokinka, (TALAUCI).
Ya sake kallon Teemah da Mukhtar yace ” kune mutane na farko dana fara yadda da ku na kuma so ku matuk’a na baku amana, na mik’a muku gaba d’aya ragamar rayuwa ta, amma kuka cutar dani, kuka ci amanata kuka yaudare kuka ha’ince had’i da yaudara ta, amma bakomai ita dama duniya ta gani haka yimin in maka ne, ya kalli Mukhtar yace ” kasan abin da ciwo wanda kake tare dashi yaci amanarka kuma ya munafurceka, har gwara wani bare can yayi maka akan na jikinka yayi maka, nasan baka san zafin abin ba maka san ya rad’ad’in da k’uncin abin ba sai kasan cewar Teemah ta kwashe gaba d’aya duniyar ta dawowa da masu ita abinsu, kamar yadda kaci amana ta haka kai ma Teemah tayi maka, nan ya kwashe komai ya fad’awa Mukhtar duk abin ya wakana tsakanin Teemah da Abraham.
A razane Mukhtar ya mik’e da k’arfi yace ” what!? that is impossible, yama za’ayi haka ta faru wallahi k’arya ne ya fad’a yana kallon Zaid, murmushi yayi masa yace “let me explain it 3 you, da farko da Laila taci amanarka domin mun biyata mak’udan kud’ad’e ta d’auko mana wannan ya fad’a yana yi masa nuni da plasma dake manne ajikin bangon parlor, wacce yayi connecting da wayarsa, take video da Teemah ta gani ya bayyana, tarwai, ido Mukhtar ya zaro waje sosai yana tunanin yaushe hakan ta faru, dariya Abraham yayi yace ” ni rainanka ne sannan kuma yaran ka ne ta wannan fannin, irin abinda kayiwa Zaid ka bashi giya ka bugar dashi nima irinsa mukayi maka ni da Laila, giya muka baka kai ta b’arin zance mu kuma muna d’auka, sannan ya juya ya kalli Teemah yace ” all this its setup, cikin kwanciyar hankali ya zauna yayi mata bayanin su suka shirya komai tun daga zuwan Ali lokacin data je shopping har zuwa Idris driver daya bata memory.
Abraham yaci gaba da cewa ” yanzu da kai tantirin talaka matsiyaci duk d’aya kuke dan baka da ko sisi a halin yanzu, sannan gaka ga Alk’ali & lawyer ga kuma DSP suma zasuyi aiki akanka ta yadda zasuyi black mailing credentials d’inka ta yarda bakai ba aikin gwamnati har abada duk wahalar karatunka ya tashi a banza, a matuk’ar harzuk’e Mukhtar ya shak’i wuyan Teemah, yana cewa “shegiya matsiyaciya, karuwa, kin lalata min, plans d’in dana kai a k’allah 20yrs ina tsara shi amma kin wargaza min komai, wallahi sai na kashe ki, gwara ma na kashe ki na huta da cutar da kika sakawa zuciyata kin sa zan rayu cike da bak’in ciki, wallahi sai nayi ajalinki.
Ganin yana niyyar yin kisa yasa DSP da lawyer mik’ewa da sauri, kokawa suka shigayi da Mukhtar dan su kwace Teemah amma sun kasa,sai dakyar suka samu suka kwace ta, yana sakin ta ta fad’a kan sofa rik’e da wuyanta tana kakarin mutuwa, a zuciye Mukhtar ya kuma nufar ta, bindiga Teemah ta gani a aljihun DSP da sauri Teemah ta warci bindigar ta saita kan shi da ita cikin matsanancin kuka tace ” karka sake ya k’ara taku d’aya kana k’arawa wallahi zan fasa kanka, sosai hankali DSP da lawyer da Alk’ali yayi masifar tashi, suka shiga lallashinta akan karta sake ta harba bindigar, Abraham da Zaid ko na Zaune kan sofa sun hard’e kafafu suna kallan ikon Allah, a hankali Zaid ya shiga tafa hannunsa yana murmushi yace ” tarihi ya maimaita kansa da kansa.
Nufo ta Mukhtar yaci gaba dayi cikin tsawa yace ” oya shut me mana, ki harbe ni nace, ” karka sake ka matso kusa dani inba haka ba wallahi zan harbeka, k’irjinsa ya nuna mata yace “harbe ni mana uban wa hana ki, ki harbe ni? , shegiya matsiyaciya karuwa, ai dama tsintacciyar mage bata mage, kin cuce ni, kin lalata min rayuwa ta, kin tarwatsa min komai, Teemah na tsaneki bana k’aunar ko sake ganin ki a rayuwata, cikin kuka tace ” nima ka cuce ni saboda kai ne wanda ya lalata min rayuwa ta ya maida ni karuwa tun ban san kai na ba, nima bana sana Mukhtar na tsane ka, ka cuce ni Allah ya isa tsakanina da kai, in sha sai kayi mummunan k’arshe, mugu azzalumi, macuci, wallahi tun a duniya zakaga tsinci sakamakon abinda ka shuka, hak’k’in lalata min rayuwa da kuma amanar Zaid daka ci bazasu tab’a barinka ka rayuwa a duniya lafiya.



