GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Zuciyar Mukhtar ta kuma yin zafi gami da rad’ad’in zafafan maganganun Teemah, ranshi yayi masifar b’aci matuk’a, a harzuk’e ya nufi Teemah, Abraham ya kalli Zaid yace ” maza kira maana police, ba musu Zaid ya dannawa police kira, a zuciya ya isa inda Teemah ke tsaye rik’e da bindiga tana cewa “karka sake kazoo inda nake wallahi zan harbek……… bata k’arasa ba taji ya kamata da kokawa yana k’ok’arin kwace bindigar daga hannunta, aiko nan dambe ya sark’e a tsakanin su, sosai suka shiga tik’ar dambe suna cikin dambe aka ji k’arar bindiga ta harba har sau biyu , a mugun razane cikin matsanancin firgice kowa ya mik’e tsaye dukkan su suka zuba musu ido dan ganin wanda ya wani harbi a tsakanin Teemah da Mukhtar.

A hankali Teemah ta sulale k’asa yayinda jini yayi tsartuwa daga cikin ta ya wankewa Mukhtar fuska dai-dai inda bullet ya fasa a cikinta tasa duka hannuwanta ta dafe wajen, take idanuwanta suka kad’a suka yi jajir, jikinta ya d’auki kerrmar azabar fitar rai da sauri Mukhtar ya durk’usa a gabanta ya tallafo ta ya rungume had’i da fasa wani irin rikitaccen kuka mai cin rai, cikin kukan yake cewa “please Teemah karki mutu wallahi ina sanki kece rayuwata matuk’ar bakya tare dani bazan tab’a kasancewa cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba, please karki tafi ki barni cikin bak’in ciki,tafa hannu Abraham yayi yace ” Allah kenan, shike zartar da abinda yaso akan wanda yaso, kun shirya mata mutuwar k’arya gashi Ubangiji ya d’and’ana mata mutuwar gaskiya, kamar yadda d’an uwana ya rungume ta a k’irjinsa yana kuka, kai ma gashi nan ka rungumeta kana kukan gaskiya had’i da d’and’anar irin rad’ad’in dayaji alokacin.

Murmushin yak’e Teemah tayi tana kallon Mukhtar cikin k’arfin hali tace ” k’arya kake Mukhtar nafi kowa sanin wanene kai, da hannunka fa kasa ka harbe ni, ka cuce ni tsakanina da kai Allah ya isa, Allah ya saka min, ta juya dakyar ta kalli Zaid tana zubar da hawaye tace ” yau nayi danasani a lokacin da bata da amfani, nayi nadama a k’urarran lokaci, na sani nayi maka mafi girman laifi amma ka dubi girman Allah ka yafe min, Zaid wanda jikinsa ya gama yin sanyi, cikin mutuwar jiki yace ” na yafe miki Fateema Allah ya yafe mana baki d’aya, a hankali ta lumshe idonta ta bud’e saboda tsabar jin dad’in sunan Fateema daya kira ta dashi, gashi ya yafe mata, a hankali tace “nagode, ta juya ta kalli Lubnah wacce jikinta keta faman rawa ta sakar mata murmushi tace” please a d’an zaman da mukayi dake idan na b’ata miki ki yafe man, cikin rawar baki Lubnah tace ” na yafe miki.

Ta kalli Abraham zatayi magana yayi saurin cewa “ni baki yi min komai ba Fateema idan ma kinyi min na yafe miki, nima ki yafe man yaudarar danayi miki, murmushi tayi mishi tace ” bakomai na yafe maka, inbanda kuka babu abinda Mukhtar keyi kamar ransa zai fita, a hankali Teemah ta fara kalmar shahada har rai yayi halinsa da k’arfi Mukhtar ya k’ara matseta a jikinta ya saki wata irin mahaukaciyar k’ara da duk gidan sai da ya amsa, da k’arfi Lubnah ta saki k’ara had’i da sulalewa k’asa a sume, a dai-dai lokacin Holland police suka shigo, da sauri Zaid ya tare Lubnah ta fad’a jikinsa DSP ne yayiwa Police din bayanin Mukhtar ne yayi kisan kai had’i da abinda ya aikata a Nigeria, ba tare da b’ata lokaci ba suka kama shi, sukayi office d’in su dashi.

Cak Zaid ya d’auki Teemah yayi mota da ita, direct hospital ya wuce da ita, bayan Doctor ya gama duba ta yayiwa Zaid bayanin tsorata tayi sosai amma babu wata damuwa, sai tsakar dare Lubnah ta farfad’o had’i da fashewa da gigitaccen kuka, da sauri Zaid ya k’arasa inda take ya rungume ta had’i da shafa kanta kanta yana bubbuga bayanta, sosai ya lallashe ya kwantar mata da hankali, jikinta a sanyaye ta d’ago kai ta kalle Zaid tace” Yaya da gaske Aunty Fateema ta rasu kodai mafarki nayi? Murmushin k’arfin hali yayi mata kawai ba tare daya ce mata komai ba, Doctor na sallamar suka wuce masaukin su direct, a can suka iske Abraham zaune jikinsa duk yayi sanyi, kallan Lubnah yayi yace ” ya jikin baki? ” da sauk’i, ta bashi amsa, Zaid ya kalle shi yace” ya akayi da gawar Teemah? “Basu yi wani bincike ba kasancewar an san wanda ya kashe ta, har anyi jana’izarta, an kaita makwancinta na gaskiya.

Rayuwar duniyar kenan yau ga kai gobe ga d’an uwanka, tun ana fad’ar mutuwar wani kanaji wata rana taka za’a fad’a, idan tamu tazo Allah yasa mu dace ya kaimu a sa’a yayi mana rahama, ya yafe mana zunubanmu, ya haskaka makwancin mu, Amin ya Allah

Kasancewar su turawa ba wani tsayawa b’ata lokaci aka yankewa Mukhtar d’aurin rai da rai a gidan yarin k’ark’ashin k’asa, ga zafi ga duhu, ba’a d’auki lokaci ba Mukhtar ya fara matsananciyar rashin lafiya, su Zaid kuwa bayan komai ya lafa direct America suka wuce wajen Ammi da Abba, inda suka iske Abba ya warke sumul kamar bai tab’a yin wata rashin lafiya ba, cike da farin ciki suka tarbi yaran su, daga nan suka d’unguma suka dawo Nigeria, sai bayan sun dawo Allah yake tambayar Zaid ya baiga Mukhtar bane, ganin Abba ya samu lafiya yasa Abraham da Zaid basu b’oyewa iyayen nasu komai ba, suka sanar dasu abubuwan da suka faru, sosai Abba da Ammi suka jinjina al’amarin had’i dayi musu addu’a tsari da kariya.

Tunda suka dawo Lubnah na gidan Ammi ta hanata komawa sai an gyara gidan, bayan Ammi tasa an gyara gidan an canja komai sabo, sannan ta bawa Zaid matarsa suka tare, bayan sun koma gida yace ta shirya musu kayan su zasuyi tafiya yanzu, ba musu ta shirya musu musu kayansu a trolley, da kanshi yasa kayan a boot din mota suka tafi, basu tsaya a ko’ina ba sai wannan k’ayataccen gidan mai tsarin turawa wanda Abraham ya kasu sukayi jinyar Zaid acan, murmushi tayi cikin zumud’i tace ” la nan zamu zo dama?

“Eh yace ” had’i da sunkuyawa ya sungume ta yayi cikin gidan da ita hannunta tasaka ta sak’alo wuyansa tace ” thanks Yaya, kiss yayi mata a goshi yace ” ba godiya a tsananin mu, “wow!! tace ganin ganin an canja komai na gidan ya koma sabo an k’ara gyara gidan fiye da da, a hankali ya sauke ta akan sofa ya koma yana shigo da sauran kayan su, kallanta yayi yace ” tashi muje muyi wanka, ido ta zaro jin abinda yace, ” wanka kuma Yaya, kadai bari naje nayi “ok jekiyi kawai yace, mik’ewa tayi ta shiga bathroom d’in, sai daya tabbatar data fara wankan sannan yayi naked ya shiga shima, lokacin daya shiga ta gama sab’e jikin sa soap tana tsaye, kai tsaye ya wuce wajenta ya kai hannu kan nononta, ai da sauri Lubnah ta bud’e idonta tana gashi ta sakar mishi kuka tana kare jikinta.

Ta shiga rok’onsa akan ya fita sai dakyar sannan Zaid ya fita ya barta tayi wanka, had’i da d’auro alwala dan yace mata tayiyo alwala, tana fitowa ya shiga yayi wanka yayi alwala shima ya shirya sallah ya ja su suka gabatar sannan ya dafa kanta ya shiga kwararo addu’a kana daga bisani ya tashi ya d’auko musu abinci suka ci suka k’oshi, hankali ta fara rufe ido alamun bacci zatayi cak ya d’auke ta ya kai kan gado yaja bargo ya rufe ta had’i da maida wutar gidan deep light, sannan ya koma kan sofa ya zauna yaci gaba da kallan labarai, ganin haka yasa Lubnah sakin jiki ta fara bacci, bayan 1hr ya mik’e ya kashe kayan kallan ya hau gadon ya iske ta lokacin Lubnah ta dad’e a duniyar bacci, a hankali ya janyota jikinsa ya mannata da k’irjinsa, take jikinsa ya d’auki wata irin muguwar kirrrrrrrma cike da shauki mara misaltuwa ya soma aika mata da zafafan sak’oninsa, cikin bacci sama-sama Lubnah taji electric na janta,a hankali ta bud’e idonta ta zuba masa, ganin yadda ya rud’e ne ya d’an tsora ta ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button