
Zaid ya shiga motarsa ya nufi gidan su, shima Abraham ya shiga tashi motar ya nufi company, Abraham na gaf da isa wayarsa ta fara ruri ganin sunan secretaria sane yasa shi d’aukar wayar bayan ta gaidashi tace masa ta kwashe takardun daya bari ta tafi gida dasu amma gobe zata kawo mishi su office ganin masu mahimmanci ne takardun shiyasa tayi haka, “ok baduwa nagode kawai ce had’i da kashe wayar, kan motarsa ya kanya ya nufi gida, Zaid nayi parking a harabar gidan ya fito da sauri dan Allah Allah yake suyi maganar kafin Abraham ya dawo,yana shiga gidan ya iske su a main parlor gidan na k’asa, cikin ladabi da biyayya ya durk’usa har k’asa ya gaida iyayen nashi.
A hankali Ammi ta zubawa tilon d’an nata ido ganin yayi muguwar rama gashi daga ganinsa zaka san yana cikin muguwar damuwa abinda keyi shi Abba ma keyi dan sosai dan shima yaga ramar da Zaid d’in yayi, Abba ya mik’e had’i da kallan Zaid yace ” ka same ni a sama na ina son magana dakai, ya juya ya kalli Ammi yace ” tashi muje sama, magana anan batayiyo ba saboda ‘yan aiki dake giftawa akai-kai, cikin mutuwar jiki Ammi da Zaid suka mik’e sukayi saman gaba d’ayansu, Abraham na shigowa shima yayi parking a indaZaid yayi, a hankali ya fito ya nufi parlor ganin duk basa k’asa ya sashi hawan saman, bayan Abba da Ammi sun zauna ne ya kalli Zaid yace ” meke damunka, meye damuwarka ko tun abinda Mukhtar yayi maka ne yake tab’a har yanzu bai bar zuciyarka?
Shiru Zaid yayi ba tare daya ce komai ba, a hankali Ammi ta shafa kansa tace ” Zaharaddeen idan baka sanar damu damuwarka ba duk duniya wazaka sanarwa koda ace bamu da abinda zamu iya taimakon ka dashi ai zamu baka gudunmawar addu’a, ka dubi girman Allah da manzonsa ka sanar damu damuwarka cikin sanyin jiki ya d’ago kai ya kalli Abba da Ammi yace ” kuyiwa girman Allah ku bani amsa ta gaskiya akan abinda zan tambaye ku dan girman Ubangiji, duk sukayi shiru sai Abba ne ya iya bud’e baki yace ” muna jinka, cikin rawar baki Zaid yace ” meye alak’arku da Abraham sannan su waye asalin iyayensa? Abraham na kawo kai zai shiga d’akin yaji maganar Zaid ta daki dodon kunnensa dan haka ya tsaya cak, Ammi da Abba kuwa sun shiga cikin mummunan tashin hankali take gaban su ya shiga fad’uwa had’i da bugawa da k’arfi , take zufa ta karyowa Abba, cikin rawar baki Abba yace ” maganar banza maganar wofi kamar ya wacce irin alak’a ce tsakanin mu da Abraham wannan wacce irin banzan tambaya ce, kai Zaid ya d’ago fuska cike da hawaye yace ” daman nasan za’ayi haka amma Abba ku sani ita gaskiya d’aya ce kuma komai daren dad’ewa saita bayyana Ammi gwara ma ku sanar da mu da bakin ki akan duniya ta sanar damu,a hankali Zaid ya mik’awa Ammi takardun yarjejeniyar da sukayi lokacin karb’ar Abraham, Abba yayi shiru yana tunanin ta inda maganar ta fito shi dai a iya saninsa daga shi sai Ammi da shugaban gidan marayu ne suka san wannan maganar amma gashi Zaid ya zo musu da ita bayan tun kan yazo duniya aka binne ta.
Abraham na tsaye a bakin k’ofa yana jinsu, Ammi ta bud’e baki zatayi magana Abba ya rik’e hannu ta yana kallan fuskar Zaid yace ” gaskiya Zaid yake fad’a ki nutsu ki kalli kwayar idonsa anan zaki gane yana cikin matsananciyar damuwa, ban san yadda akayi maganar nan ta fito domin bayan mu uku babu wani mahaluk’i dayasan wannan maganar da farko ina mamaki da al’ajabin jin maganar daga bakinka amma daka ce man gaskiya bata tab’a b’oyuwa komai nisan lokaci saita bayyana hakan yasani sanin cewa dole lokaci yayi dazan sanar dakai, amma da sharad’in idan ka sake ka sanarwa da Abraham ko bayan ran mu ne bamu yafe maka ba duniya da lahira, Ammi ta fasa kuka tace ” haba Abba kaifa kayi alk’awarin duk rintsi duk wuya bazamu tab’a fito da maganar nan ba.
Murmushi Abba yayi irin nasu na manya, yace ” to yanzu da bamu fitatan ba ta ina ta fito, a hankali Abba ya juya ya kalli Zaid ya shiga bashi labarin tun farkon auren su da Ammi har zuwa d’auko Abraham daga gidan marayu har lokacin da aka haife shi, Abba bai b’oye masa komai ba, Ammi ta kalli Zaid tace ” wallahi tallahi idan ka sake ka gayawa Abraham koka nuna masa wani abu a fuska Allah ya isa tsakanina dakai, kuma shima d’ana ne saboda yasha nono nah, ni na shayar dashi, cikin matsanancin kuka Zaid yace ” nayi matuk’ar bak’in cikin jin Abraham ba d’an uwana na jini bane, amma duk da haka ya rigada ya zama nawa tunda mun sha nono d’aya a lokaci d’aya, kuma baisan kowa nashi ba sai mu, nayiwa Allah godiya daya bani d’an uwa da ni kad’ai zan taso nayi rayuwa cike da k’unci cikin rashin abokin wasa da Mukhtar ya samu nasara akaina, in sha Allah Abraham bazai tab’a gane ko fuskantar wani abu daga gare ni b……….
Abraham da tunda Abba ya fara magana jikinsa keta faman tsuma had’i kerrrrma sosai ya shiga cikin mummunan tashin hankali, gabansa ya shiga fad’uwa k’irjinsa yayi masa mugun nauyi, mak’ogwaron sa yayi masa mugun d’aci take ya nemi nutsuwarsa ya rasa ya fara zancen zuci “dama ni ba jinin Abba da Ammi bane, dama basu ne iyaye na, basu suka haife ni ba duk irin abinda nayi a baya suka jure lalle mutanan nan sun cika ‘yan halak kuma ‘ yan amana, cikin muguwa kid’ima had’i da matsanancin firgice ya danna kai d’akin, shigowar Abraham ce ta hana Zaid k’arasa maganar sa, cikin tashin hankali duk suka mik’e tsaye kai daka kalli Abraham kasan yana cikin masifaffan tashin hankali, duk ya zare ya fita daga nutsuwarsa yana shiga direct wajen takardun yarjejeniyar ya nufa ya duk’a ya d’auka yana dubawa.
Su Ammi na ganinsa suka mik’e tsaye cikin masifaffiyar razana gami da matsanancin firgici had’i da muguwar fad’uwar gaba, hannunsa na rawa ya shiga duba takardun, kwallar dayake ta k’ok’arin addu’ar fitowar dan samun sauk’i ta shiga gangaro masa, a hankali ya fara kokawa da nufashinsa yayinda da idanuwansa suke gani dishi-dishi, cak numfashi ya d’auke idanuwansa suka rufe ruf gaba d’aya ya daina ganin komai, ya sulale k’asa a sume cikin firgice Abba da Zaid sukayi kansa suna kiran sunansa, Ammi na tsaye ta kasa motsawa inbanda hawaye babu abinda ke fitowa daga idanuwanta, basu jira wani tab’a lokaci ba suka sungume shi sukayi Hospital dashi, da gudu Nursing suka karb’e aka shigar dashi Emergency, sai da akayi wajen 3hrs sannan Doctor ya fito yana share gumi, da sauri su Abba taryi Doctor d’in, d’an guntun murmushi yayi musu sannan yace ” Allah ya taimaka kun kawo shi akan lokaci daya samu HEART ATTACK, “heart attack Zaid ya maimaita cikin tsoro “yes kawai doctor yace had’i da nuna musu d’akin da aka kwantar dashi.
A hankali suka turo k’ofar d’akin suka shiga cikin mutuwar jiki, Abba na gaba sai Ammi da Zaid, idon Abraham biyu ya kawar da kansa gefe yana zubar da hawayen bak’in ciki da takaicin abubuwan da yayiwa su Ammi da Abba a baya shi yanzu ma kunyar su yake ji ya rasa ta ina zai fara had’a ido dasu, zahirin gaskiya yana masifar jin kunyar had’a ido dasu, saboda abubuwan dayayi a baya duk mugayen halayen sa suka jure suka shanye basu tab’a k’amatarsa ko nuna banbanci a tsakaninsa da Zaid koda na second d’aya ne bane, gaskiya su Abba sun cika cikakkun ‘yan halak, duk wata da zasu b’oye ainahin shi waye sun bi dan ganin bai san ko waye shi ba, ashe shiyasa suka hana rabon gado ko bayan ba ransu gaskiya sunyi masa gata iya gata shi bashi ma da bakin da zai iya yi musu godiya a bisa karamcin da sukayi masa, haka kuma bashi da abinda zai iya saka musu dashi.