
Akwai wata yarinya a unguwar mu mai suna Yasmeen k’awar k’anwata tace sosai, sun yi masifar shak’uwa da junan su abin ma har ya wuce tunani, rana d’aya na tsinci kaina da mugun k’aunar Yasmeen amma babu wanda na baiyanawa .
Har Umar, nabar dai bar abin a raina. Ina cigaba da renan soyayyarta acikin zuciyata.
Haka zalika a b’angaren Umar ashe tuni sun tsunduma cikin soyayya shi da tilon k’anwa ta Ramlat, batare da wanda ya sani,b a.
tuni km har soyayya rsu tayi nisa.
“Umar wai bazaka raka ni bane, a ‘yan kwanakin nan na rasa me kake yi a gida da dare idan nace kazo mu fita sai ka k’i,.Ko meyasa hk ?
murmushi kawai Umar yayi hade da yatsina fusakarsa yana kallon Abdul kasa kasa kana yace ” kawai dai ban san fitar ne.
, nafisan na zauna gida tare da Mama da Baba ina taya su hira.
, kallon sa Abdul yayi da alamar rashin yarda atare dashi da km maganar sa.
” kai dai ka san dalilin dayasa kake kunshe kanka ciki gida yana maganar yana tafiya har dai yakarasa fice Daga gidan gabadaya.
Sakamakon ruwan saman da ake tsulawa yasa Abdul dawowa gida da wuri, yana danna kai ‘cikin d’akinsu yaji hirar soyayya tsakanin Umar da Ramlat, d’an b’ata rai Abdul yayi sosai sannan yace ” ke tashi ki fita, da fara’a Ramlat tace” Yaya mai ya faru?
“Nace ki fita ko, da sauri Ramlat ta fita,tana mamakin abinda yayanta yayi .
kallon Abdul, Umar yayi yana shafa sumar kanshi , Abdul yayi dariya yace”Ok dama wannan ne da yake hanaka fita kullum ko ?
ka lik’e a gida,kana sacewa kanwata zuciya ko ?
munafiki to Allah ya kamaka.
Dariya shima Umar yayi yace ” kodai Allah ya kamamu, “kai da wa?
” ni kai cewar Umar yana dariya, shima Abdul dariya yayi sosai yace ” kamar ya ban gane ba.
Kallosa Umar yayi da alamar zolaya ya fara wak’a “Yasmeen abar k’auna ta, dariya Abdul yayi sosai yakai mai duka, suka shiga wasa suna tsokanar junan su, Umar yace ” haba d’an uwa har akwai abinda zaka iya b’oye man to ai har na tura mata sak’onka, ta kuma amince, ido Abdul ya zaro waje yace ” kai haba?
” Wallahi da gaske nake maka sosai Abdul yaji dad’i had’i da rungome Umar ajikinshi yana yi masa godiya.
Washe gari Baba da Mama, da Umar da Abdul da kuma Ramlat da Auta duk muna zaune a parlor, muna hira Abdul ya kalli Mama yace ” Mama d’anki fa ya fad’a soyayya, Ramlat naji haka ta zaro ido da alamar tsoro.
, Mama tayi dariya tace” ikon Allah ina kuma ya samu min sirikar?
Da sauri Umar ya mik’e ya rufewa Abdul baki yana janshi waje, yana dariya, shima Abdul dariya yake, dakyar Abdul ya kwace bakinsa yace ” ‘yarki ce ai, ‘yar gida za’ayi, yana jin na fad’a ya sake ni yayi waje da gudu, Ramlat ma ta mik’e ta shige d’aki, sosai iyayen mu sukayi masifar farin ciki da soyayyar Umar da Ramlat dan su a tunanin su Umar yaran kirki ne, mai nagarta gashi nutsatstse zaifi rik’e musu Ramlat da daraja, shiyasa kowa ya nuna farin cikin sa da amincewarsa.
Soyayya sosai ta k’ara k’arko tsakanin Umar da Ramlat, a b’angaren Abdul da Yasmeen ma haka abin yake soyayyar su, dan kowa ya sani har iyayen su sun sani, dan haka aka tsaida ranar auren Abdul da Yasmeen, Umar da Ramlat da zarar sun k’are Secondary school.
Mummunar rana ta farko dabazan manta da ita arayuwata ba.
, lafiya lau muka ci abinci da Baban mu, mukayi hira yayi mana fad’a sosai akan gaskiya da rikon Amana, da zumunci, sosai yayi mana fad’a daga k’arshe yayi mana addu’a tare da fata na gari a rayuwar mu.
, ya shiga d’aki, da sallar asuba ma shiya tashe mu tare muka tafi masallaci, amma hukuncin Ubangiji yafi k’arfin wasa, da misalin k’arfe 7:00am najiyo kukan Maman mu tana kiran mu, da gudu muka fito muka iske ta a tsakar gida.
Sosai Mama take kuka ta kasa magana da hannu take nuna mana d’akin Baban mu dukkan mu muka shiga da gudu har Ramlat, Allahu Akbar rai yayi halinsa su Baba an riga mu tafiya gidan gaskiya.
Sosai mutuwar mahaifin mu ta girgiza mu, haka muna ji muna gani akayi masa wanka aka kaishi gidan shi na gaskiya, duk wanda yaga Umar yasan yashiga mugun taahin hankali wanda daga k’arshe mu muka dawo muna lallashin shi, sosai mutuwar Baba ta shigi Umar, gaba d’ayan mu jikin mu yayi mugun yin sanyi, kasancewar Abdul karatu yake bashi da wata sana’a,nauyin gidan gaba d’aya ya koma hannun Umar, kusan komai shi yake yi a gidan, har nauyin karatu na shiya d’auka yake yi.
Kwanci tashi babu wuya awajen Allah har Baba yakai wata biyar da rasuwa Mama ta fita daga takaba, cikin ikon Allah kud’in Baba ya fito dayake bamu da ‘yan uba, shiyasa ba’ayi maganar rabaon gado ba, d’akin Baba aka fasa ta waje aka bud’e babban shago (shop) sosai muke ciniki dan duk unguwar babu shago kamar kamarsa, dan haka nauyi yabar kan Umar.
Sosai na maida hankali na kan karatu na yayin da soyayya ta da Yasmeen ke k’ara zurfi, sosai rayuwa ta canja mana saboda har yanzu mutuwar Baba bata gama sakin mu ba, duk da kasancewar mun yarda da k’addara, mun karb’eta da hannu biyu.
Haka dai rayuwa tayi ta tafiya yayinda ta ko wanne fanni aka damu mahaifiyarmu da kawo k’arar Umar sosai fiyye da da, wasu ma har cewa sukayi yana shaye-shaye da bin ‘yan daba daga k’arshema aka ce yana fashi da makami sosai abin yake bani dariya a duk sanda aka danganta Umar da wad’an nan halaye, a fannin Mamanmu kuma sosai abin ya fara damunta, yayinda Umar ke kuka sosai kamar ransa zai fita.
, a d’aki na samu Umar yana ta faman kuka, a hankali na durk’usa a gabansa na shiga lallashin sa, amma ina na kasa, tashi nayi naje na kira Maman mu, itama jikinta a sanyaye ta shigo d’akin, a gabansa ta zauna ta jawo shi jikinta ta rungume itama ta shiga kukan.
Cikin kuka Umar yace ” Mama kodan anga ni ba d’anku bane ansan bani da kowa sai ku shiyasa ake min, sharria .
sannan idan yau kuka ce kun barni na shiga uku, Ina zan saka kaina bani da wasu dangi ko iyaye da suka wuce ku, ban san kowa ba sai ku, a hannunku na girma kunfi kowa sanin halina ku zaku gayawa duniya waye Umar d’inku.
, dan Allah Mama karku bari maganganun mutane suyi tasiri a zucikataku , harku watsar dani, Mama karki fushi dani dan fushin uwa ba k’aramin masifa bace ga rayuwar d’a ba, dan Allah Mama karku yarda wallahi Allah sharri suke yi min, ga Abdul nan duk inda zamu tare muke zuwa yafi kowa sani na da hali Na .
Cikin kuka Mama ta k’ara rungume Umar ajikinta tace ” kaima kamar Abdul kake a waje na,umar daga yau karna k’ara jin kace baka da iyaye ko dangi balle harka k’ara cewa baka da dangi, mu mune komai naka a rayuwa, kana da iyaye dan mune iyayenka kana da dangi dan dangi mu sune naka, kana da ‘yan uwa dan Abdul, Ramlat, Ja’afar sune ‘yan uwanka.
Rungume Mama ya k’arayi sosai yana kuka yace ” nagode Mamana nagode sosai Allah yabar zumunci Allah ya bani ikon saka muku da mafi girman alkhairi, dafa shi Abdul yayi ta baya yace” tsakanin mu ba godiya, mun riga mun zama tsintsiya mad’aurinmu d’aya.
, gabadaya sukayi dariya had’i da rungume junansu cikin farin ciki da k’aunar junan su.
Amma sai me?
Washe gari da safe tun 8:00am na shirya domin ina da lactures, bamu fito ba sai 6:20pm a matuk’ar gajiye muke lik’is, ga yunwa ga ba mota, ganin karna b’atawa kai na lokaci yasani yankar hanya nabi ta gefen gari, kasancewar yamma tayi sosai ina fara tafiya magrib tayi, ga tsakanin gidan mu da makaranta akwai Dan tazara sosai, nasan kafin na k’arasa anyi isha’i, ina cikin tafiya duhun dare ya farayi, me zan gani a gaba, cikin firgici na zaro ido na, tabbas ido na ba k’arya yake min ba, abinda nagani gaske ne ba karya ba .
Take ban san sanda kwalla ta fara zubarmin ba, dan in tabbatar na matsa kusa dasu sosai, daga gefe na d’an rakub’e ta yadda zan rik’a jiyo maganar su.