
Yana cikin tunanin yaji hannun Ammi na share masa hawayen dake ta ambaliya daga idansa, a hankali ya d’aga jajayen idonsa ya kalle ta ganin itama kukan take yasa shi mik’ewa zaune, fuskantarta yayi ido cikin ido ya k’ura mata ido ya kasa cewa komai, a hankali ta zauna a bakin gadon taci gaba da kukanta hannu Abraham yasa yana goge masa hawayen idonta had’i da girgiza mata kanshi alamar ta daina kuka yayinda da shima idonsa ke zubar da hawaye, Abba da Zaid na tsaye dukkan su suna zubar da kwalla, a hankali Abraham ya bud’e baki yace” Ammi dama ni ba d’an…. da sauri ta d’ora hannunta akan bakinsa tace ” kul kar na sake jin ka furta wannan kalmar kai d’an mu ne har yau har gobe sunanka Abraham Muhammad Bature kamar yadda Zaid zai amsa sunan Muhammad Bature haka kaima zaka amsa.
“Har abada ba’a tab’a canjawa tuwo suna, ni ce na shayar dakai nice na raineka duk wani da uwa zatayiwa d’anta haka nayi maka haka duk wani abu da uba ya kamata yayiwa d’ansa Abban ku yayi muku, mune danginka iyayenka baka da wasu iyaye da suka wuce mu haka baka da wani d’an uwa daya wuce Zaid, daga yau har bada idan ka sake cewa bamu mune iyayenka ba Allah ya isa nono na daka sha, da sauri ya rungume Ammi yana kuka yace ” nagode sosai Allah yasaka muku da alkhairi Ubangiji ya….
Karka sake yi mana godiya cewar Abba, a hankali Abba ya tako yasa hannu ya rungume Ammi da Abraham Zaid na tsaye yana ji a ransa inama bai tsananta bincike ya gano wannan sirrin ba, shiyasa akace garin tune-tunen kaza take tuno wuk’ar yanka ta gashi yanzu ya sanya gaba d’aba Family sa a bak’in ciki, duk abinda Allah yace kar muyi kuma yi tabbas bazamuga dai-dai ba, domin Allah da kansa yace ” karmu tsananta bincike, hannu Abraham ya mik’awa Zaid yace ” don’t miss family hugs murmushi yayi had’i da rungume su gaba d’aya.
Bayan an sallamo Abraham gida ya warke sumul ya wartsake Abba ya tara su a babban falonsa dake sama sukayi secret family meeting su hud’u kawai Abba, Ammi, Abraham, Zaid, Abba ya kalle su yace ” a zahiri mu hud’u ne kawai anan amma a bad’iri mun fi haka domin Allah da mala’iku suna nan, to ina san Allah da Mala’ikun dake wajen nan su shaida cewar na mallakawa Abraham da Zaid gaba abinda na mallaka, na basu kyauta ko bayan raina babu maganar rabon gado, idan kunga dama kuna iya rabawa ta biyu dai-dai kowa ya d’auki tasa, amma da san rainane dakun barta a cure wajen d’aya inyaso sai ku rink’a juyawa tare, duk suka risina suka yi godiya, har sun mik’e zasu tafi Ammi tace ” ku tsaya ina son magana daku bayan sun koma sun zauna ta kalli Abraham tace ” asalin iyayenka ‘yan garin Yobe state ne cikin garin Yoben mahaifiyar ta bani wasu abubuwa tace na baka a baya abinda yasa ban baka ba saboda baka san gaskiya, a hankali Ammi ta mik’a masa wasu abubuwa hannunsa na rawa ya k’arb’a Ammi taci gaba da cewa kaje gida ka nutsu sai ka duba.
Murmushi Abraham yayi had’i da cewa Ammi ai babu wani sirri da zan iya b’oye muku, a hankali ya bud’e hotunane guda hud’u suka fad’o da sauri yasa hannu ya d’auka na farko hoton mahaifiyarsa da mahaifinsa ne, sai kuma na mamansa badan dana babansa daban sai d’ayan wanda akayi na family dayawa mutane sun kai 15, yana dubawa yaga wasik’a kasa karantawa yayi sai Zaid ne ya d’auka ya shiga karantawa a bayyane.
Assalamu Alaikum yaro na ko yarinya ta ni dai da farko sunana Farida Salis Yobe nice mahaifiyar sunan mahaifinka Muhammad Yahaya dukkanin mu ‘yan Yobe ne a unguwar sabon titi ni da mahaifinka mun kasance ‘yan uwa ne domin da Baba na da Baban shi uwarsu d’aya ubansu , kaine yaron mu na fari, idan Allah yasa ka rayu har ka girma ka nemi dangin mu
Wasik’ar dana yawa domin tayi bayanin komai da kowa, bayan sati d’aya Zaid da Abraham , Ammi da Abbasuka shirya suka je Yobe, kasancewar akwai sunan iyayen da kuma hotonsu yasa basu sha wuyar samu familyn Abraham ba, duk da basu san ko suwaye ba sun karb’e su cikin mutunci, mik’a musu hotunan Abba yayi gami da wasik’ar, sannan Abba ya shiga yi musu bayani komai.
Aiko take aka tattaro dangi da ‘yan uwa suka zo sai da aka taru kaf babba da yaro sannan Abba ya maimaita maganar had’i da mik’a musu hotunan sannan ya nuna musu Abraham, aiko iya kuka kam ranar sunyi shi domin mutuwar ta dawo musu sabuwa, sai da suka tsaya suka kwana biyu ana bugawa ‘yan uwa na nesa waya suna zuwa, shima kuma Abraham aka shiga zagayawa dashi birni da k’auye, gaba d’aya dangin Abraham talawa ne sosai fiye da tunani, tun daga nan zumunci ya k’ullu sosai, Abraham ya shiga taimakon danginsa da ‘yan uwansa cikin k’ank’anin lokaci suka farfad’o dan da acikin matsanancin talauci suke amma cikin lokaci kad’an aka fara damawa dasu domin duk samarin family da matasa ya basu aiki a company su, sosai Abraham ya shiryu ya dawo mutumin kirki ya nutsu ya daina duk abinda yakeyi.
Ammi da Abba suka matsa mishi kan maganar aure amma yayi burus,
Abraham zaune kusa da Ammi Abba da Zaid na gefe, Ammi ta kalli Abraham tace ” wai kai baka san naga jikoki nane nayi nayi kayi aure amma kak’i, dariya yayi yana kallon Zaid yace “Ammi bari nayi ai ki zab’a min dan naga kin iya zab’e wad’anda akayiwa suna guduwa da zunb’urar baki ga su nan shiru da an dami mutane da ba’a so, d’ago kai Zaid yayi ya kalli Abraham yaga dai dashi suna had’a ido Abraham ya kanne masa ido d’aya yace ” ko ba haka ba Zaid pillow Zaid ya jefo mishi yana dariya yace ” oho dai “ok haka kace ko? to bari na fasa kwai ya kalli Abba da Ammi yace ” albishirinku? da sauri suka had’a baki suka ce goro, Lubnah dai ai kafin ya k’arasa Zaid ya biyo shi da gudu yana jefansa da pillow yana gudu yana dariya yace ” kun kusa samun jika Lubnah is pregnant, ai Abraham na fad’a Zaid yayi waje da gudu dan yasan idan ya tsaya had’uwa zasuyi suyi ta tsokarsa, cikin dangin Abraham na Yobe akwai wata yarinya Halima wacce ake kira da Lina ‘yar k’anin Baban Abraham ce uwa d’aya uba d’aya yarinyar kyakykyawar gaske ce ajin farko Ammi ta yaba da tarbiyya da nutsuwar ta dan haka ta nemawa Abraham aurenta sosai danginsa sukayi farin ciki ba’a wani d’auki lokaci ba akayi bikin, amarya ta tare Abraham na ganinta yaji ya kamu da mugun santa dan irin matar dayake mafarkin mallaka ce.
BAYAN SHEKARA BIYU
Muhammad Bature Family suna cikin matsanancin farin ciki dajin gami da walwala, babu wani abinda yake damunsu yanzu face annashuwa sosai Zaid da Abraham suka had’e kansu suke yin komai tare ko kayan sawa iri d’aya suke sawa kullum, d’aya bazai tab’a yin abu batare da sanin d’aya ba, duk yadda zan kwatanta muku had’in kan su ya wuce nan, haka ma abin yake a tsakanin Lubnah da Lina, Luban tana da yaranta biyu maza wanda suka ci sunan Abraham da Abba, yayinda Lina ke da d’iya mace mai sunan Ammi sai dai Lina na d’auke da tsohon ciki…
Mukhtar kuwa yana can prison ya gamu da matsanciyar jinya yana d’auke da cututtuka masu girman gaske, HIV, BLOOD CANCER, CIWON K’ODA, KUTURTA, ga wani ruwa dake fita daga jikinsa mai tsutsotsi ga gashen wari, duk da kasancewar su turawa amma sunyi maganin duniyar nan har sun gaji sun hak’ura sun kyale shi dan haka suka kai shi can gefen prison suka yar da shi, babu mai zuwa wajensa dan ko abinci tura masa kawai akeyi kullum sau d’aya, duk yadda mutum yakai ga rashin imani idan yaga halin da Mukhtar yake ciki a yanzu sai ya tausaya masa, dan tsutsotsi harta al’aurarsa suke fitowa had’i da wani ruwa mai shegen d’oyi, kullum addu’a yake yi Allah ya d’auki ransa dan mutuwa hutu ce a gare shi, ya gwammaci mutuwarsa sau dubu akan wannan matsananciyar rayuwar mai tattare da bak’ar wahalar duniya had’i k’unci