
Zaid ya kalli jama’ar dake wajen yace ” kunji labari na, Al’amin yace ” Masha Allah amma yanzu ina Abraham da Lina?
Murmushi Zaid yayi yace ” babu inda zaka ganni a duniya ba tare da Abraham ya fad’a yana kallan gefe gaba d’aya jama’a suka kalli inda Zaid ke kallo, murmushi Abraham yayi yace “gani nan ina tare dasu sai dai bana d’aya daga cikin SIX’S STARS kasancewar dukiyar mu a had’e take, kuma ni da Zaid abu d’aya ne shiyasa Zaid kawai ya shiga amma dukda haka muna tare.
Al’amin yace ” ina Ammi da Abba suke?
“Duk suna nan a raye dan sune iyayen SIX’S STARS
Sosai jama’a suka jinjina musu akan cin amanar da makusantansu sukayi musu, wasu sai kuka suke, haka dai taro ya watse jama’a nata alhinin duniya da mutanen cikinta, wasu suka ce sun d’auki darasi gami da izzina daga rayuwarsu.
Lokaci d’aya duniya ta d’auka akan LABARIN SIX STARS duk wata tasha dazaka kunna a TV ko radio labarin sukeyi, jama’a sai kuka suke yi suna tausaya musu, nan da nan sunan su ya k’ara shahara a duniya suka k’ara samun d’auka, duk inda kayi sai kaji ana ambatar sunansu.
Yauma kamar kullum SIX STARS ne zaune a parlor wanda ke gidan Abraham suna meeting akan wani business , matan su da yaran su na zagaye da su hankalin kowa nakan abinda akeyi amma banda hankalin Zarah dake kan plasma tana kallon wani film take idanta suka fara zubar da hawaye ba tare data sani ba a hankali kukan nata ya rink’a tsananta harta fashe da kuka ba tare data sani ba, sautin kukan da suka ji ne yasa su daina abinda suke yi suka fuskance ta a hankali BASMA, YASMEEN, FATEEHA, KAUSAR, LUBNA, LINA suka mik’e suka nufe ta zama sukayi gaba d’ayan su a kusa da ita, a hankali Lina ta rungumo ta jikinta suka shiga lallashinta, sai da tayi kukan mai isarta sannan ta hak’ura, cikin badara Kausar ta shiga tambayarta abinda ke damunta cikin muryar kuka tace” film d’in can ne yayi min kama da labarin rayuwa ta hakan ne ya tuna min komai, kuma komai ya dawo min sabo take KAUSAR, BASMA ma suka fashe da kuka domin suma sun tuna da tasu rayuwar.
A hankali su Yasmeen suka shiga lallashin su itako Zarah baki ta bud’e tana kallan su, sai kuma tayi murmushi tace ” meya saku kuka kodai kuka nane ya saku kuka?
Cikin kuka Basma da Kausar suka ce “muma mun tuna da tamu rayuwar ne, a hankali kowa ya fara kallan juna Zarah tace ” gaskiya ya kamata muma mu bawa juna labarin mu, “gaskiya kam cewar kausar cikin kuka, a hankali mazajen su suka mik’e suka nufi inda suke, Zarah ta kalli Naseer tace ” dan Allah ina nemar alfarmar a karo na farko a wajenka akan ka bari na fad’awa ‘yan uwna labari na, shiru yayi ya kasa cewa komai, haka ma Kausar da Basma kowacce ta shiga neman izini a wajen mijinta akan bada labarin rayuwarta duk sukayi shiru sai can Naseer ya sauke ajiyar zuciya yace ” Bawai na hanaki ki sanarwa da su Lubnah labarinki bane haka kawai sai dan saboda sirrin mu ne, a hankali Khamal yace ” what sirri? Au dama akwai wani sauran sirrin da muke b’oyewa juna mufa duniya muka sanarwa da namu sirrin akan abinda ya shafi personal life d’in mu, ashe a junan mu akwai sauran abinda muke b’oyewa juna?
“Cool down Khamal ba haka nake nufi ba ka fahimce ni ma, baka bari na k’arasa fad’ar abinda zan fad’a ba ka katse ni so nake nace amma tunda yanzu mun gama zama d’aya nayi mata izini, cikin zumud’i Zarah ta rungume Naseer tace “thank you so much dear, Basma ma ta kalli Ammar tace ” please mana murmushi yace ” duk mun baku dama, cikin zumud’i suka rungume junansu suna matsananciyar murna, bayan kowa ya nutsu ya zauna kowa ya bada hankalinsa ga sauraren labarin, cikin farin ciki Zarah tace wazai fara? da sauri Kausar tace “ni, “ok to fara muna jinki
LABARIN KAUSAR
Ban muku Alk’awarin samun labarin su ZARAH, KAUSAR, BASMA ba, dan ban gama yanke hukunci ba, zaku iya ganin ci gaba koyaushe ko kuma bazaku iya gani ba ina nan dai ina shawara, dan ba tabbacin zan ci gaba
MOMYN ZARAH
[22/01, 16:44] +234 803 948 8935: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
34
LABARIN KAUSAR
A salin sunana Kausar Muhmud ni haifaffiyar garin Katsina ce, mumu uku ne a wajen iyayen mu, ni ce babba sai k’anwa ta Meenal da d’an autan mu Zita’ulhaq, wanda tun daga kansa mahaifiyar mu bata kuma samun haihuwa ba, mahaifiya wacce muke kira da Umma ita kad’ai ce a wajen mahaifin mu da muke da Malam, abinda yasa muke kiransa da Malam sai dan kasancewar sa Malami tun tasowarsa kuma haka muka ji kowa na kiransa, Umma da Malam suna zaune lafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali tunda muka taso bamu tab’a ganin ko musu ya shiga tsakanin su ba,daga Umma har Malam mutane ne masu matsanancin hak’uri da kawaici had’i da kara shiyasa suka zaune da kowa lafiya, haka yasa muma yaransa muka taso da hak’uri dan duk cikin mu babu mai kwaramniya balle fad’a ko yawan magana, haka muka taso cike da so da k’aunar junan mu.
Muna zaune ne a unguwar k’ofar k’aura dake cikin garin katsina, k’ofar k’aura tana d’aya daga cikin k’ofofi masu d’unbun tahiri, Malam mahaifin mu ba wani mai arziki bane haka kuma ba talaka bane dan munfi k’arfin duk wasu buk’atun mu tunda muke bamu tab’a neman wani abu mun rasa ba, bamu tab’a rasa ci ko sha ba haka kuma bamu rasa sutura ba, dan Malam yana iyakar k’ok’arinsa wajen magancewa iyalansa buk’atun su ,dan haka muka taso acikin rufin asirin Allah.
Haka ma a b’angaren karatu Malam ya tsaya mana dan kamaranta mai kyau ta ‘ya’yan gata yaran manyan masu kud’i mukayi anan garin katsina ALHUDA tun daga primary har secondary school anan mukayi, makaranta ce babba sosai wacce ake koyar karatun boko da Islamic duk d’aliban dazasuyi Candy tare suke yi da saukar Qur’an, lokacin ina SS3 dan har mun fara zana waec examination yayinda Meenal ke SS1 Zita’ulhaq ke JSS 2, ni da Meenal tun tuni mukayi saukar Al’kur’an a islamiyyar mu.
Duk wanda yasan Kausar yasan Ni’ima haka zalika duk wanda yasan Ni’ima yasan Kausar, Ni’ima k’awata tace ta rai da rai mak’otan mu ne su daga gidan su sai gidan su, mun shak’u sosai da Ni’ima tun muna yara tare mukayi primary and secondary school site d’in mu d’aya haka ma islamiyya a tare muke , koyaushe muna tare ko kayan sawa ma irin d’aya muke yi, k’awance mu ne yayi sanadiyyar had’a iyayen mu k’awance.
KAUSAR
Mace ce san kowa k’in wanda ya rasa duk da ba fara bace dan kausar b’ace sosai irin bak’ak’en nan da ake black beauty irin wad’anda sukafi farare da yawa kyau, bata da tsayin gashi sosai dan gashinta iyakacinsa kafad’a amma yana da masifar cika (yawa) gata da d’an k’aramin tsukakken baki mai d’auke da fararen hak’ura sol a jere, Allah ya wadata ta da dadaran idanu farare sol manya dasu masu kamar tana jin bacci sai dogon hancinta siriri, a b’angaren diri kowa ba’a magana dan tana cikar k’irji nonuwanta manya madaidaita d’as dasu, k’ugunta mai fad’i , sai uban hips da tudun d’uwawo irin su ne ake kira da coca cola sharp,kai ko macece tayi arba da k’irar Kausar sai taji wani abu balle kuma d’a Namiji mai GANDA.