
Muna da 17yrs muka kammala karatun mu na secondary ni da Ni’ima, dai-dai lokacin ne Allah ya had’a ta da saurayinta Bashir wanda take masifar so da k’aunarsa kamar ranta, Bashir d’an wani hamshak’in mai kud’i ne wanda duniya take damawa dashi, tuni duniya ta dad’e da sanin mahaifin Bashir Alhaji Musa Canji, ganin mugun son da Ni’ima keyiwa Bashir yasa iyayen ta suka nemi daya fito (ya turo iyayen sa) ba’a wani b’ata lokaci ba ya turo iyayensa, kasancewar iyayen Bashir ne yasa ba’a wani tsaya b’ata lokaci ba aka saka ranar biki wata d’aya.
Aiko take muka shiga hidimar biki baji ba gani, kasancewar nice babbar k’awar amarya kuma Aniyarta yasa hidima tayi min yawa bana nan bana can, hmmmmmm rashin sani yafi dare duhu da nasan K’ADDARA TAH tana tattare da bikin aminiyata Ni’ima dabanje ba, dan rana bikin Ni’ima ne silar faruwar komai, silar rugujewar komai gare ni, silar shigata cikin k’unci da taskon ratuwa had’i da matsanancin tashin hankali.
HAJIYA LAILAH
Hajiya Lailah mace ce hamshak’iya kyakykyawar gaske ajin farko, mata d’aya jal a gidan Sanata Sambo, ta kasance tana da yara uku biyu maza d’aya mace, Fahad ne babba sai Haidar sai kuma autar su Shema’u wacce suke kira da Shema, Hajiya Laila macece mai aji ga kud’i da hutu sun ratsata ta had’u iya had’uwa dan ta kowanne fanni kake neman had’ad’d’iyar mace takai harta wuce, gaba d’aya gidan Hajiya Lailah a birkice yake dan kwata-kwata gidan baida tsari bare tarbiyya, kowa harkar gabansa yake babu wanda yasan da zaman wani, kasancewar Alhaji Sambo d’an siyasa mai mak’iya da dama yasa shi b’oyewa duniya iyalinsa ya sanarwa duniya yaransa d’aya shine Fahad sai bayan faruwar labarin Abdul sannan duniya ta san sauran yaransa.
Hajiya Lailah bata nemi komai najin dad’in duniya ta rasa ba sai abu d’aya shine mijinta dan kwata-kwata Sanata Sambo bashi da lokacin ta, harkar siyasar sa kad’ai yasa a gabansa, kullum baya gida wani lokacin ma sai yayi wata d’aya cur baya nan, koda ma yana gari sai ya dama yake biya mata buk’atarta idan tayi masa magana ya rufe ta da fad’a yace ta fiye jaraba,
mijinta Alhaji Sambo ya kasance gagarumin manemin mata ne kamar d’an bunsuru duk inda mata suke idonunshi yana wajen su idan ko kyallara ido yaga mace fa shikenan ba zaman lafiya ya rink’a b’arin kud’in kenan har sai ya cimma burinsa, yayinda matarsa ta gida bata da wani mahimmanci da ita da babu duk d’aya ne a wajensa dan yana samun biyan buk’atarsa a wajen matan banza.
To nasan dai kun riga kun san halin Sanata Sambo tun baya a labarin Abdul ba saina dawo baya ba.
Wannan abu ne kad’ai yake masifar damun Hajiyar Lailah dama gata mace ce ita mai matsananciyar sha’awa, Hajiya Lailah duk ta damu kanta ta rasa nutsuwarta ta shiga tunanin nemarwa kanta mafita, lokaci d’aya ta rame ta fige kallo d’aya zakayi mata kasancewar tana cikin damuwa, ganin ta kasa nemarwa kanta mafita ne yasa ta ta shirya nufi gidan aminiyar Hajiya Rabi, Hajiya ta kasance mace ce ‘yar bariki cikekkiya ta bugawa a jarida, ita mijinta wani hamshak’in d’an kasuwa ne , itama haka taita fama da irin matsalar Hajiya Lailah saboda mijinta baya zama kullum yana k’asashen duniya, wannan dalilin ne yasata tsundumawa bariki ta zama cikekkiyar ‘yar duniya, ta fara neman yara k’anana maza da mata samari da ‘yan mata (Under ages).
Aiko nan da nan Hajiya Rabi tayi k’aurin suna a wajen neman mata da maza matasa, ta daina damuwa da lamuran mijinta ta fita harkarsa ko yana gari ba ruwanta dashi burinta kawai ya sakar mata kud’i ita kuma ta nemi yara k’anana dasu, tana isa gidan Hajiya ta shiga falon da sallamarta da gudu Hajiya Rabi ta taso rungume ta tace ” wooo aminiya ta rai da rai kwana biyu shiru, “hmmm Hajiya Lailah tace tana zama akan d’aya daga cikin kujerun a gefenta Hajiya Rabi ta zauna jiki ba kwari dan daga ganin yanayin k’awarta ta tasan da matsala dukda tasan matsalarta bata ce ta Sanata Sambo amma yau in sha Allah ta k’uduri niyyar fad’a mata halin da take ciki da kuma ainahin wacece ita.
Cikin mutuwar jiki Hajiya Rabi tace lafiya k’awata?
“Hmmmm ta kuma cewa had’i da sauke ajiyar zuciya, a hankali Hajiya Lailah ta shiga kwararowa Hajiya Rabi matsalarta ba tare data b’oye mata komai ba, murmushi Hajiya Rabi tayi ta talle ta sannan tace ” kin fad’a min wannan matsalar taki ta a irga wacce kema kanki shaida ce duk irin matsalarmu d’aya to ni dai gaskiya na nemarwa kai na mafita, da sauri Hajiya Lailah tace ” kai K’awata amma shine koki fad’a min a gudu tare a tsira tare, dan Allah sanar da ni mafitar da kika samu, ba tare da tsoro ko fargabar komai Hajiya ta kalli Hajiya Lailah ido cikin tace ” LEZ nake kuma ina neman matasan samari irin wad’anda bazasu wuce 25yrs ba a firgice Hajiya Lailah ta mik’e tsaye had’i da cewa “what?
Mik’ewa Hajiya Rabi tayi tana murmushi tace ” yes of course, kunnan ki baijiye miki k’arya ba da gaske nake miki, ni yanzu cikekkiyar ‘yar lesbian ce ta bugawa a jarida nan da Hajiya Rabi ta shiga sanar da Hajiya Lailah komai bata b’oye mata komai ba, ta kuma shiga kwad’aita mata abu da dad’insa, ta k’ara da cewa ke a tunaninki su mazajen namu hak’uri suke? to idan ma kina tunanin haka gwara ma ki daina tunda su ba waliyai bane, ke kin san irin buk’atar mijinki, kin fi kowa sani idan ma zai iya jure rashin mace na tsawon wata da watanni, take kwakwalwar Hajiya Lailah ta shiga juyawa tsayawa cak kawai tayi ta k’urawa Hajiya Rabi ido harta dasa aya, batare data ce mata komai ta sab’i jakarta ta fice, bayan ta Hajiya Rabi ta biyo tana kwala mata kira amma tayi mata banza, bata ko juyo ba balle ta amsa mata.
Tsaki Hajiya Rabi tayi ta koma cikin gidan ta zauna had’i da cewa “banza wahalalliya a haka zaki k’are inbaki bawasa bak’in cikin d’a namiji ne zaiyi ajalinki sakaryar wofi, haka dai tai fad’a ita kad’ai tana bambami, can kuma tunanin kar Hajiya Lailah ta tuna mata asiri ya zo ta, wani d’an guntun murmushi tayi had’i cewa ” yo tama fad’a mana idan ta tuna min asiri kanta ta tunawa dan duniya ta riga ta sammu tare iyakaci na fututtuke na rufe ido nace tare mukayi, kuma nasan duniya yarda zatayi saboda yadda muke da ita.
To k’alubale anan shine karka yadda kayi abota da mutumin banza, karka sake duniya ta sanka da banzan mutum dan duk abinda yake yi tunani za’ayi kai ma hakan kake koda kuwa ba hakan kake ba, domin Hausawa sunce abokin b’arawo, b’arawo ne, Allah yasa mu dace duniya da lahira.
Bayan Hajiya Lailah ta koma gida ta kasa zaune ta kasa tsaye ta rasa gaba d’aya sukuninta duk inda tayi tunanin maganganun Hajiya Rabi na ranta, tabbas tasan Alhaji Sambo bazai tab’a iyayin hak’urin rashin sex ba harna tsawan wata da watanni, saboda ta riga tasan shi mabuk’aci kenan hakan na nufin manemin mata ne? tayiwa kanta tambayar take wasu abubuwa suka shiga dawo mata, dan a lokutan baya tasha kama shi ire-iren wad’annan laifuka kuma mutane sunsha kawo mata tsegumin irin wannan maganar, tabbas maganar Hajiya Rabi gaskiya ce, dan idan ba gaskiya bace mai yasa Alhaji Sambo ya b’oyewa duniya su?
Haka Hajiya Lailah ta kwana cur tana ta tunanin maganganun Hajiya Rabi dan yadda taga rana haka taga dare, da safe wajen 10:30am ta fito falo bayan ta gama shiryawa ganin bata ga Ummi mai aikinta bane yasa ta nufar d’akinta, Ummi yarinya ce dan bazata wuce 27yrs ba, a hankali Hajiya Lailah ta tura k’ofar d’akin Ummi ta shiga da sallamarta bata iya k’arasa sallamar ba saboda yadda taga Ummi tsirara haihuwar uwarta da ubanta ta fito daga wanka tana shafa mai a jikinta, suman tsaye Hajiya Lailah tayi dan ganin surar Ummi bayya ne a gabanta, take maganar Hajiya Rabi ta kuma fad’o mata rai.