GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Dan ko yaya Sanata Sambo da Hajiya Lailah suka kuskura suka shiga gonar Sheemah ko Haidar sai buzun su, haka dai rayuwa taci gaba da tafiya a gidan Hajiya Lailah babu wani gyara kullum sai k’ara tab’arb’arewa da watsewa gami da tarwatsewa da gidan keyi, yayinda hakan bak’aramin k’ona zuciyar Fahad yake ba, dan duk cikin su babu wanda bai san bak’ar halayarsa ba, Hajiya Lailah ce kawai har yanzu bai san ainahin wacece ita ba, yana iya kar k’ok’arin sa dan ganin ya gyara gidan da mutane gidan sun dawo normal suna tsaftatacciyar rayuwa mai inganci gami da tsabta amma ina abin ya wuce tunanin sa dan abun ya faskara ya wuce saninsa, lalacewar gidan ya lura da tushe ta samu.

A gefe kuma Hajiya Lailah da K’awata sai abinda yayi gaba dan wolewarsu kawai suke yi, ba ruwansu da tunanin duniya ko sakamako da makoma balle suyi tunanin k’arshen al’amarin, gaba d’aya rayuwar duniya suka saka a gabansu, kullum idon su yana kan ‘yan shilan mata da maza ‘ya’yan talakawa suna bud’e musu ido da mahaukatan kud’i, yayinda da a gefe d’aya Ummi da Sheemah ke k’ara holewarsu suna kuma shak’uwa da juna kamar hauka, amma kwata-kwata Hajiya Lailah bara lura da abin ke faruwa tsakanin su ba.

Su Kausar an shiga hidimar bikin aminiyarta Ni’ima haik’an dan an shigo satin bikin dan haka kwata-kwata basa samun zama 24hrs suna busy , yau tun da safe da suka tashi suka tafi kasuwa dan k’arasa yin sauran siyyar data rage musu, basu dawo daga kasuwar ba sai yamma lik’is a kuma matuk’ar gajiye, hakan ne ya hana su zuwa k’unshi da kitso suka bari akan sai gobe dan yau sunyi masifar gajiya, tun da aka fara hidimar bikin Kausar ta dawo gidan su Ni’ima anan take yin komai dan har kwana acan take kwana, suna shiga gidan suka zube a parlor had’i da cewa “wash, Umman Ni’ima dake shigowa parlon d’auke da tiran abinci ta aje agaban su tana cewa ” ya naji kuna wash ku duka biyun?

Fuska Kausar ta d’an yamotsa cikin shagwab’a tace ” wallahi Umma munyi masifar gajiya ne, tun safe fa muke yawan kasuwa duk rana yau da aka kwala a kanmu ta k’are ga muguwar yunwar da muke faman ji, murmushi Umman tayi had’i cewa “tab tun yanzu har kun fara kukan gajiya, to wallahi inzaku zage gwara ma ku zage dan acikin kashi goma baku d’auki ko d’aya ba, Ni’ima data kasa magana saboda wahala ta mik’a hannu dakyar ta jawo abincin gabanta ta fara ci, Kausar ma ta sanya hannu suka fara cin abincin.

Washe gari ma tun da safe suka fice wajen saloon dan Ni’ima bamai san kitso bace shiyasa ta zab’i saloon itako Kausar tace kitso take so, sai da aka gyarawa amarya kansa aka wanke mata k’afa sannan suka wuce gidan kitso, kasancewar Kasar nada yawan gashi kuma k’ananun kitso akayi mata yasa basu dawo gida ba sai magrib, dan ko k’unshi basu samu sunyi ba, kitson Kausar yayi masifar kyau dan ‘yan mitsi-mitsi aka yarfa mata irin na ‘yan Nijar, akayi mata shuku a tsakiya sai kuma ayi mata na gaba.

Tun da safe yauma suka k’ara ficewa suka nufi gidan k’unshi aiko an yana musu lallan ya zanu mai ja da bak’i yayi masifar kyau, amma ita Kausar saboda kasancewarta bak’a yasa akayi mata red & golden color, suna dawowa suka Ni’ima ta fad’a wanda saboda a ranar ne akeyin dinner kuma gashi har lokacin ya kusa ga masu make up sun su sai faman jiran su ake yi, wata irin fitinanniyar kwalliya aka yiwa su Kausar sun fito sosai sunyi kyau dan Kausar komawa tayi kamar aljana saboda kyau.

Fad’ar had’uwar da wajen bikin yayi b’ata lokaci ne, an kashe kud’i iya kud’i wajen tsara wajen, Ni’ima da Angonta suna zaune a high table yayinda da kid’an police band ke tashi daga gefe, duk inda ka juya Kausar zaka gani tana ta hidima da jama’a sai kyalli take had’i da shek’i tana d’aukar ido kamar gold kusan gaba d’aya hankalin mazan dake wajen na kanta.

Bayan an gama ciye-ciye da shaye-shaye MC ya buk’aci ganin babban k’awar amarya a filin rawa domin ta d’an taka, gaban Kausar ne yayin mugun fad’uwa dan bata tab’a yin rawa a rayuwarta a ba ita kunyar rawa ma take balle yanzu acikin wad’annan dubban jama’a, MC ya k’ara maimaitawa had’i cewa idan bata fito kafin ya irga goma ba to zai sa mata tarar daba ta kud’i wacce tafi rawar, ganin MC har ya kai eight yasata saurin mik’ewa dan bata san wacce irin tara zai saka mata ba gashi yace bata kud’i bace, a hankali ta fara takawa har izuwa filin rawar ta rawa d’an jujjuwa jikinta a hankali, kasancewar Kausar mace ce har mace akwai diri wacce idan tayi taku duk ilahirin jikinta sai ya motsa yasa nan take gaba jikinta ya d’auki sheken, gaba d’aya hall d’in akayi tsit ana kallonta hankalin kowa yayi kanta.

Shurun da Hajiya Rabi taji anyi ne yasata d’ago kanta a hankali, domin ganin abinda yasa mutane shiku, tana d’agowa idonta ya sauka akan Kausar, nan take gabanta yayi mummunar fad’uwa k’irjinta ya buga da k’arfi, take yawon bakinta ya d’auke mak’ogwaronta ya bushe had’i daui mata d’aci, a fili ta furta ” wow masha Allah, Ubangiji yayi halitta anan, bata san sanda ta mik’e ta nufi inda Kausar take a filin rawar ba, tana gaf da isa Mc yace ” masha Allah muna godiya k’awar amarya Allah yasaka da alkhairi, zaki iya komawa ki zauna, dama kamar jira take dan jinta take kamar akan k’aya da sauri tabar filin rawar bata k’ara koda 1 second bane.

Tsaki Hajiya Rabi tayi gami da cizon yatsa dan taso ta iske Kausar a filin rawar ta fakaice da rawar ta tab’a jikinta, nan take Hajiya Rabi ta shiga neman Kausar ido rufe a hall amma duk inda ta hango Kausar d’in kafin ta k’asa sai ta iske harta bar wajen, sosai Hajiya Rabi ta tada hankalinta akan son yin magana da Kausar amma Allah bai bata ikon yin hakan ba har aka tashi daga dinner d’in haka Hajiya Rabi ta nufi wajen motar ta cike da matsanancin bak’in cikin rashin magana da Kausar, Hajiya Lailah ce ke jansu a mota motar tayi shiru babu mai cewa da kowa k’ala, shirun da Hajiya Lailah taji yayi yawa ne yasa ta sauke ajiyar zuciya had’i da cewa ” kai gaskiya bikin nan an tsara komai akan tsari abin ya burge ni wallahi, shiru Hajiya Rabi tayi bata ce komai dan gaba d’aya hankalinta baya kan Hajiya Lailah bare tasan me take cewa, tuni ta tsunduma duniyar tunanin Kausar wacce tunda take bata tab’a jin ta kamu da son mace lokaci d’aya haka ba, kai bama ta tab’a son wani mutum kamar yadda take jin son Kausar haka ba, dan sosai Kausar ta gama tafiya da hankalinta da tunaninta burinta kawai ta kasance da yarinyar, take taji zata iya yin komai akan ta mallaki yarinyar koda na tsawon dare d’aya ne, kuma taji zata iya koda abinda ta mallaka kaf ne akan Kausar, had’i da k’udurcewa ranta zanta aikata komai, kuma zata iya rabuwa da kowa akanta.

Hajiya Lailah takai hannu tad’an tab’a kafad’arta had’i da cewa ” lafiya kuwa k’awata? nannauyar ajiyar zuciya Hajiya Rabi ta sauke tare yin murmushin k’arfin hali tace ” bakomai k’awata kawai dai ina tunanin rayuwa, ta b’oyewa Hajiya Lailah gaskiyar abinda yake damunta dan tasan matuk’ar Hajiya Lailah taga yarinyar itama sai abinda Allah yayi, koda suka k’asara gida sama-sama Hajiya Rabi tayiwa Hajiya Lailah sallama, tana shiga gida ta wuce bedroom d’inta ta fad’a kan bed had’i da lumshe ido ta fad’a tunanin yarinyar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button