GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari d’aurin aure tuni su Kausar suka gama shirya komai sannan Ni’ima ta shiga wanka tana fitowa aga watsa mata make up mai shegen kyau, har Kausar zata shiga wanka Umman su Ni’ima ta aiko kiran su, sai dyar Kausar ta zame ta dawo d’akinsu dan ta samu tayi wanka ta shirya itama dan har an d’aura auren azahar ma ta kusa, ga jama’a ko’ina ka duba fal da gidan, a hanzarce ta cire kayanta ta zare towel ta fad’a bathroom, Hajiya Lailah zaune a gefen Umman su Ni’ima dayake su Hajiya Lailah k’awayen mahaifiyar Bashir angon Ni’ima ce amma ita bata Lez kawai da suna business tare ne, Hajiya Lailah ta mik’e da niyyar shiga toilet, Umman su Ni’ima tace ” aiko Hajiya kamar da akwai mutum sai dai kije d’akin su Ni’ima can ne nake ganin kamar bakowa, “ok to ina ne d’akin, Umma da kanta ta rakata har k’ofar d’akin sannan ta jiyo.

Hajiya Lailah ta shiga d’akin had’i da tura k’ofar d’akin direct ta nufi bathroom takai hannu zata murd’a handle d’in taji an bud’e k’ofar bathroom d’in Kausar ta fito da sauri daga ita sai wani guntun towel d’an mitsitsi wanda dakyar ya rufe mata d’uwawonta, haka ma duk rabin nononta a waje ita bama ta lura da mutum a d’akin ba dan sauri take ta shirya tabar Ni’ima da k’awayen su, Hajiya Lailah wacce ke tsaye kamar mutum mutumi tayi dan ta juma dayin suman tsaye take taji wani irin abu ya tsarka mata tun daga k’afarta har zuwa cikin kwakwalwarta, wani irin bugawa k’irjinta ya shiga yi da k’arfi yayinda zuciyarta ta shiga daka uban tsalle, lokaci d’aya taji wani mugun reaction a jikinta musammanta yadda taga k’unshi da kitson Kausar sunyi bala’in yi mata kyau, ga koyaya ta motsa sai jikinta ya motsa, take taji wata muguwar sha’awar daba tab’a jin irinta a rayuwarta ba na taso mata a hankali ta nufi wajen Kausar………

MOMYN ZARAH
[24/01, 07:12] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

37

Hajiya Lailah na gam gaf da k’arasawa inda Kausar take su Ni’ima suka shigo d’akin “sai kace mai canja fata kin wani yi zamanki, murmushi Kausar tayi dayasa dimples d’inta suka lotsa had’i da cewa ” I’m really sorry k’awata, jin sassanyar muryar Kausar ya sake zauta Hajiya Lailah dake tsaye cak ta kasa gaba ko baya, take ta fara hango ta kwance ita da Kausar kwance akan gado suna soyewa, tana cikin wannan tunanin taji k’ara rufe k’ofa da sauri ta kai idonta kan k’ofar taga su Kausar ne suka fita, wani irin yawo ne ya wucewa Hajiya Lailah ta mak’ogwaronta ba shiri, a hankali ta zauna a gefen gadon, a hankali ta furta ” kota halin yaya sai na kwanta da yarinyar na, koda zan k’arar da abinda na mallaka na rabu da kowa a duniya sai na cika burina akanta.

Cikin mutuwar jiki ta fita batare data shiga bathroom d’in ba, tana isa parlor’n gidan ta hango Kausar a tsakiyar k’awayen ta tana da murmushi yayinda dimples d’inta ke lotsawa, tsayawa Hajiya Lailah tayi cak ta k’urawa Kausar ido k’em batare datasan me take yi ba, dan gaba hankalinta yana wajen Kausar, Umman su Ni’ima ta k’araso inda Hajiya Lailah ke tsaye kamar mutum mutumi , tace ” Hajiya har kin fito, shiru Hajiya Lailah bata amsa ba dan bama tasan Umman na tsaye ba balle tasan abinda takeyi, k’ara yi mata magana Umman tayi amma shiru ba amsa, a hankali Umma tabi inda Hajiya Lailah take kallo, da kallo ta kalli wajen itama, ganin su Ni’ima zaune sunata harkar gabansu bama susan da ita ba yasa tace ” ikon Allah.

A hankali Umma ta dafa kafad’ar Hajiya Lailah had’i girgiza ta tace” lafiya Hajiya? firgigit Hajiya Lailah ta dawo hayyacinta, ganin Umma a gabanta yasa ta fara kame-kame a kunya ce tace ” hmmmm hmmmm uhnnnnn wallahi yaran ne masu hankali da nutsuwa, murmushin jin dad’i Umma tayi, Hajiya Lailah ta nuna Kausar da hannunta tace ” ya sunan wacce? “KAUSAR Umma ta bata amsa, a hankali Hajiya Lailah ta maimaita sunan ” KAUSAR, Ok wacece ita, ko itama ‘yarki ce? “A’a ‘Yar mak’otan muce Mamanta ma k’awata ce sosai, kinga ma mamanta ta can, Umma ta fad’a tana nuna mata Maman su Kausar, a hankali tabi inda Umma ta nuna mata da kallo, Murmushi Hajiya Lailah tayi had’i cewa ” kai masha Allah.

Wasu mata ne suka kira Umma ta tafi tabar Hajiya Lailah anan a tsaye tana cewa ” Hajiya ki shiga d’aki ki zauna ina zuwa, Hajiya Lailah bata samu damar amsawa Umma ba, saboda ganin Kausar ta mik’e ta nufi d’akin Ni’ima, aiko da sauri Hajiya Lailah tabi bayan ta, a d’akin ta iske ta tana k’ok’arin fitowa, da sauri Hajiya Lailah ta k’arasa inda take, cikin nutsuwa Kausar ta kalli Hajiya Lailah ta d’an risuna tace ” ina yini?

Hannu Hajiya Lailah tasa ta dafa Kausar tana murmushi tace ” lafiya lau, ya sunan ki? ” Kausar ta bata amsa, ” nice name ta fad’a tana kallan Kausar ido cikin ido, Kausar kina da aure? da sauri ta sunkuyar da kanta had’i da girgiza kai alamar a’a, hannunta data dafa kafad’arta ta dafa had’i mammatsa mata kafad’ar cikin wata irin murya tace ” you are very beautiful Kausar, a hankali Kausar ta zame jikinta ta d’an matsa baya kad’an had’i dayin murmushin yak’e, k’ara matsowa gaf da ita Hajiya Lailah tayi ta mik’a hannu zata rik’ota Ni’ima ta shigo tana cewa ” to shekarau d’anko hand bag d’in kenan? murmushi had’i fita batare datayiwa kowa magana ba, Ni’ima ma tabi bayan ta.

Bayan sallar ishsha aka kai amarya Ni’ima gidanta, bayan iyayenta da abokanan arziki sunyi mata nasiha mai ratsa jiki, sosai Ni’ima da Kausar ke kuka kamar ransu zai fita daga jikinsu, koda suka isa gidan suna rungume da juna, koda Hajiya Lailah ta shigo d’akin taga yadda Kausar ke ta faman ji tayi kamar ta d’ora hannu aka ta kura ihu dan jin kuka Kausar d’in take yi har cikin ranta da ruhinta, ganin yadda kuma suka ruk’unk’ume juna ita da Ni’ima ne yasa ta jin wani irin mugun kishi ya taso mata, take taji zuciyar ta tayi bak’i k’irjinta yayi mata zafi yayinda mak’ogwaronta ya fara yi mata d’aci.

Da kyar Hajiya Lailah ta iya controlling kanta saboda tsananin kishin dataji na taso mata, a hankali ta mik’e ta koma gefen Kausar ta zauna had’i da jawo ta jikinta ta rungume tana d’an bubbuga mata bayanta tare da lallashinta, dakyar Kausar ta iya rabuwa Ni’ima ta fito domin mutocin abokanan ango da zasu maida su gida sunzo, Hajiya Lailah na rungume da Kausar da sunan lallashinta take domin daga Kausar har jama’ar dake wajen basu san halayyar Hajiya Lailah ba balle su ankara da abinda take nufi da Kausar, Hajiya Lailah kuwa yak’e kawai take dan jin zuciyar ta take kamar zata kama da wuta saboda tsananin kishi, ko da aka je shiga mota Hajiya Lailah tace su tafi kawai ita zata mai da Kausar gida, amma fir tak’i yadda, babu yadda batayi ba amma tak’i yarda, haka Hajiya Lailah ta hak’ura dole ba dan taso ba.

Tun da Hajiya Lailah ta koma gida ta kwanta take ta faman juyi akan bed ta kasa bacci saboda tunanin Kausar da kuma tsananin santa datake ji yana ratsa duk wata jijiya da b’argo dake jikinta yana bin magudanar jinin jikinta, tun da take a duniya bata tab’a kamuwa da son wani abu a duniya kamar yadda take jin son Kausar ba, jinta take yi kamar ranta, bata tab’a jin sha’awar wata halitta a iya rayuwarta kamar Kausar ba, ganin ta rasa mafita ne yasa ta kiran Jimrau bokan su ” yana d’agawa yace ” hala an gano wata ‘yar shilan ne dan ba’a jinku sai idan da aiki, dariya tace ” kamar ka sani, Boka mai duniya, amma wannan yarinya ba kamar sauran matan dana saba kawo maka bace dan tasha bam bam dasu ita ta daban ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button