
Wata irin gigitacciyar dariya yayi sannan yace ” ba KAUSAR ba? cikin mamaki Hajiya Lailah ta mik’e zaune daga kwancen datake duk tasan wannan ba abin mamaki bane dan kad’an daga cikin hatsabibancinsa tace ” ya akay….. da sauri ya katse ta had’i “kin san bana san yawan tambaya ko?
Ayi min afuwa ya bokan duniya, ajiyar zuciya boka jimrau yayi sannan yace ” ki bani nan da gobe saboda ina so nayi duba (bincike) akan al’amarin sosai, “ok shikenan badamuwa Allah ya kai mu gobe, Hajiya Rabi kuwa sai dai muce Allah ya kyauta dan abu yaci tura kullum bata da wani aiki sai na tunanin Kausar, dan har gizo Kausar d’in keyi mata, duk ta rame tasa kanta uku duk wanda zata ambaci sunansa sai ta kira shi da Kausar ko bacci ta iyawa, kusan kullum yadda taga rana haka take ganin dare, a b’angaren Hajiya Lailah ma haka abin yake da kwata-kwata kasa runtsuwa tayi Allah Allah take gari ya waye ta kira Boka jibrau.
Tun k’arfe 7:00 na safe ta kira boka dan ta kasa hak’uri, yana d’aga wayar ya tuntsure mata da dariya sai da yayi mai isar sa sannan ya tsagaita, itako Hajiya Lailah ta kawo iya wuya ta shak’a iya shak’a, dan dai ba yadda zatayi dashi ne, Boka Jimrau yace ” Hajiya a gaskiya akwai matsala, da sauri tace ” wacce irin matsala ce? “Eh to gaskiya a halin yanzu bazamu tab’a iya cin narasa akan yarinyar nan ba, saboda yarinyar tana da k’arfin addu’a sannan ma’abociyar ibada ce, wata irin mummunar fad’uwar gaba Hajiya Lailah taji, yadda kasan saukar aradu, rikin in’ina tace ” to …. to ya.. nz.. u.. ba.. bu…wata… mafitar… kenan? “to ni dai mafita d’aga na gano, da sauri tace ” wacce? “sai dai idan zaku kasance a gida tsaya har na tsawon wata uku kuna cin abin iri d’aya kuna shan ruwa iri d’aya sannan zan baki wani magani dazaki rink’a zuba mata a abincinta tana ci, zan baki wani turare da zaki rink’a shafawa a jikinki kullum da daddare duk sanda kika shafa ki tabbatar data shak’a har na tsawon wata d’aya, zan baki wanda zaki rink’a turara gidan kullum da safe kafin ta tashi daga bacci shima wata d’aya zakiyi kina amfani dashi, da wanda zan baki kullum ki tabbatar kin shafe mata jikinta dashi, har tsawon wata d’aya, duk aiyukan da zan baki idan aka fara su ba’a tab’a bashi har a gama gidan kika kuskura kika yi fashi to aikin ya lalace koda kin kai kwana 29, sannan ba’a had’a su lokaci d’aya duka sai dai gidan kin gama wani ki fara wani, kin shi zai baki wata uku kenan.
Tunda ya fara magana Hajiya Lailah tayi shiru dan bata san ta yadda zata kasance da Kausar har na tsawon wata uku ba, Hajiya Lailah ta karaya sosai jikinta yayi sanyi, tana dai sauraran sa ne har sai da ya dasa aya yakai k’arshen maganarsa, cikin fidda tsammani tace ” to yanzu ta wacce hanya zan kasance da itan harna tsawon wata uku? wallahi boka bani da wata mafita, murmushi Boka Jibrau yayi had’e da cewa ” akwai mafita d’aya tak, amma tana da matuk’ar wahalar gaske ba lalle ne ki iya ba, a hanzarce tace ” boka fad’i komaye zanyi duk muninshi duk had’aranshi kuma duk wahalar shi matuk’ar zan mallaki Kausar, cike da isa boka Jibrau yace ” sai dai idan zaki aura mata d’aya daga cikin ‘ya’yanki maza, da sauri Hajiya Lailah ta mik’e tsaye had’e cewa ” what?
” kai ma kasan hakan bazata tab’a yiyuwa ba, ni da nake son nakance da ita shine kuma zan aura mata d’a kasan yadda nake tsananin kishin Kausar kuwa? ina matuk’ar san ta sosai sanda ban tab’a yiwa wani d’an Adam arayuwa ta ba, bana kuma tunanin zan k’ara yiwa wani irin bayan ita, yama za’ayi ni da kai na da hannu na aurar da Kausar ga wani d’a namiji?
“Kai ma kasan bazan iya yin hakan ba, dariya Boka Jimrau yayi yace ” to ruwanki kuma sharawa ta rage gamai shiga rijiya, ni dai na gaya miki wannan ne kad’ai mafita matuk’ar kina san kasancewa da Kausar, kuma kiji wajen duk wani boka a duniyar nan kiga idan yana da wani abunyi bayan wannan, haba sai kace ba mace ‘yar bariki ba, ke kika san yadda zaki b’ulluwa al’amarin, ki tsara shi yadda zai tafi akan tsari, a cikin yaran naki sai ki aurawa nutsatstsen danshi ba lalle ne yabi ta kanta ba balle harya nemi wani abu daga gare ta ba, kuma zamu iya yin asiri mu kawar da hankalinshi daga kanta yaji kwata-kwata baya ko san ganinta, amma idan kika aurawa wancan d’an iskan kin ba asiri ba kome zamuyi sai yayi amfani da ita saboda shi na banza ma nema yake balle wannan, sosai Boka Jimrau ya d’auki lokaci yana fahimtar da Hajiya Lailah ya kuma nuna mata wannan ce kad’ai mafita, akayi sa’a Hajiya Lailah ta fahimta sosai ta kuma yarda ta amince.
Har sunyi sallama zata aje wayar sai kuma ta tuno da iyayen Kausar d’in aiko da sauri tace ” Boka to iyayen Kausar d’in fa? cikin dariya yace ” karki damu da wannan kibar komai a hannuna zanyi musu aiki dukkansu daga yaron har yarinyar da kuma iyayenta duk zan rufe musu bakin su ta yadda dakinje neman auren ba musu zasu amince miki, haka shima yaron dakin je mishi da maganar bazai yi miki musu ba zai yarda, cike da jin dad’i da matsanancin farin ciki tayiwa Boka Jimrau godiya sannan sukayi sallama.
Bayan Boka Jibrau ya gama aikin ya sanar da Hajiya Lailah akan ta taje wajen iyayen yarinyar ta nemi auren, sannan bayan komai ya kammala sai ta sanar da yaron nata cike da farin ciki ta kashe wayar, da sauri ta kira layin Momyn Bashir mijin Ni’ima take ce mata tana so ta rakata wajen nemarwa Fahad aure, nan tayi mata bayanin taga k’awar matar Bashir mai hankali da tarbiyya shine take son aurawa Fahad ita, Momy dayake bata san dawar garin na, cikin farin ciki tace bakomai sai ta k’araso, koda suka isa unguwar basu wuce gidan su Kausar kai tsaye ba sai da sukaje gidan su Ni’ima suka yiwa Umma da Baban Ni’ima bayanin komai, cike da farin ciki yayi musu jagora har zuwa wajen Malam Baban Kausar, a falon gidan aka sauke cikin mutantawa da girmamawa, Malam na zaune Baban Ni’ima na gefensa yayinda duka matan GE zaune daga gefe, Baban Ni’ima ne yayiwa su Malam bayanin komai, dayake Boka Jimrau ya gama aiki a kansu gaba d’aya, shima ba musu ya amince cike da farin ciki, Hajiya Lailah tace bata son bikin ya d’au lokaci idan ita asan ranta ne karya wuce sani biyu, ba musu kowa ya amince da hakan, suka rabu akan nan da kwana biyu yaran da Baban shi zasu zo.
A ranar Hajiya Lailah ta samu Fahad da maganar auren sai da yayi d’an jimmmmm sannan daga bisani ya amince shima ba musu duk da bai san wacece matar daza’a aura mishin ba, washe gari Friday Alhaji Sambo yazo gida weekend , sai da Hajiya Lailah ta bari ya gama cin abinci yayi wanka ya nutsu a bedroom d’insa sannan ta shirya tsaf ta nufi bedroom d’in nasa cike da kissa ta ta zauna a gefensa take k’arshin turaren da Boka Jimrau ya bata yace ” ta rink’a amfani dashi a dun lokacin da take ta buk’ata a wajensa take zai amsa koda bai shirya, k’arshin turaren ya bugi Sanata Sambo, a hankali ya d’ago kai ya kalle ta tayi masa wani irin rikitaccen kallo gami da cewa ” sweetheart dama wata magana nake son muyi dakai aje duk abinda yakeyi yayi ya funkance had’i da jawo ta jikinsa yace ” ina jinki………….
MOMYN ZARAH
[26/01, 02:37] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)