
Da k’arfi zuciyar sa ta buga, jin takun na k’ara matsowa yasashi mik’ewa da sauri ya b’uya a bayan k’ofa, dai-dai lokacin da mutum ya shigo d’akin, Fahad dake lab’e yaji an tuntsure da mahaukaciyar dariya had’i da cewa ” big brother idan kayi mana shigar sauri wajen aurenta mu kuma zamuyi maka shigar sauri wajen having sex da ita, na dad’e ina mafarkin samun mace irin Kausar komai yaji, ban tab’a tunanin akwai su a duniyar ba sai gashi kwatsam naci karo da ita, yaza’ayi na iya hak’ura da ita batare dana mayar da kwad’ayi na ba, ya fad’a yana k’ok’arin cire rigar jikinsa, a gigice Fahad ya fito daga inda yake b’oya ya kunna light d’in d’akin Haidar ya gani tsaye yana k’ok’arin cire wandonsa.
Cikin firgici Fahad yace ” what you again?
Cike da matsanancin mamaki yake kallan Haidar yama rasa me zayyi mishi, ya rasa ta ina zai fara hukunta shi, cikin tsoro Haidar ya kalli Fahad bakinsa na rawa yayinda gaba d’aya jikinsa kerrrrma yake, tsoro da fargaba sun hana shi furta koda kalma d’aya ne, a hankali Fahad ya zauna a bakin gado yayi tagumi da duka hannayensa ya fashe da kuka mai cin rai da k’ona zuciya, cikin kuka yace ” a waje ba’a damarmin matata ba sai a gidammu a gidan namu ma ‘yan uwana na jini wand’anda muke uwa d’aya uba d’aya dasu, meyasa Haidar duk matan waje, duk matan duniyar nan ka rasa wacce zaka nema sai matata, why! why!! why!!! Haidar ya fad’a a tsawace yana mik’ewa yaci kwalar Haidar yace ” meyasa Haidar?
A tsawace cikin d’aga murya yace ” nace meyasa Haidar, tsawar da yayi ce ta farkar da Kausar a kid’ima ta mik’e ganin Fahad rik’e da kwalar Haidar yasata fara yiwa kanta tambayoyi da dama, kalaman Fahad data tsinta ne suka sakata fahimtar komai cike da mamaki ta shiga kallan Haidar take hawaye suka shigo zubowa daga idanuwanta cikin tashin hankali ta fara zancen zuci dabata san ma yana fitowa fili ba ” wanne irin bahagon gida ne, wanne irin mutane ne acikin gidan nan, irin wannan kurman gidan na shigo da irin wad’annan mutanen zan zauna harna had’a jini dasu, kalaman Kausar ne suka kuma tun zura zuciyar Fahad ya fara dukan Haidar tako’ina yana yi masa mahangurb’a, tun daga bedroom yake dukan Haidar har sai da suka fito farfajiyar gidan.
Wani wawan naushi Fahad ya sakarwa Haidar take ya saki k’ara had’i da sulalewa k’asa yana zubar da jini a matuk’ar gabaice wata irin razananniyar k’ara Kausar ta saki wacce ta kaure daga d’aya gidan hakan yayi sanadiyyar farkawar duk wani mahaluk’i dake cikin gidan da gudu Hajiya Lailah da Sanata Sambo, Ummi da sauran ma’aikatan gidan duk suka fita waje, inda suka iske abinda ke faruwa da sauri Hajiya Lailah da Sanata Sambo suka k’arasa inda suke dai-dai lokacin da Fahad ya shak’i wuyan Haidar, daga Hajiya Lailah har Sanata Sambo suka shiga kiciniyar kwace Haidar daga hannun Fahad amma duk suka kasa, ganin idanuwan Haidar sun kakkafe jikinsa ya saki yasa Kausar yin mahaukacin ihuuuuuuuu had’i da sulalewa k’asa a sume.
Sakin Haidar yayi ya fad’i k’asa timmmmmm ya nufi inda Kausar ke kwance a sume, bayyiwa kowa magana ba duk da tarin tambayoyin da Hajiya Lailah da Sanata Sambo keyi masa a hankali ya sunkuya ya sab’i Kausar ya shige da part d’in su ya rufe k’ofa, da sauri Hajiya Lailah ta nufi inda Haidar ke kwance a sume ta shiga jijjigashi tana kiran sunan shi, ganin baiko matsa bane yasata kwalawa driver suka suka shi a mota suka nufi hospital.
Direct bedroom d’insa ya wuce da Kausar a hankali ya kwantar da ita akan bed ya mik’e ya nufi fridge ya d’auko, yana watsa mata ta sauke ajiyar zuciya ta fara bud’e idanta, karaf ta had’a ido da Fahad ai sauri ta mik’e tayi baya can k’uryar gado jikinta yana kerrrrma da wani mugun tsoron Fahad take ji tana kallan shine kamar wani monster, murmushi yayi dan ya fahimci tsoransa take ji, a hankali ya d’ago jajayen idanunsa ya zuba mata, kallanta kawai yake da jajayen idanuwansa ya kasa yin komai, yana tunanin meyasa Haidar da Sheemah ke neman keta masa haddi, a hankali ya jawo ta jikinsa ya rungume gam ya fasa kuka mai k’ona zuciya, itama fashewa tayi da kukan aka rasa mai rarraahin wani a tsakanin su.
Kasancewa Haidar ya daku sosai yasa likitoci kwantar dashi, sai bayan gama komai sannan Hajiya Lailah ta dawo gida, tabar Ummi a wajensa, bayan ta dawo gida tayi wanka ta fito falo ganin har lokacin Sheemah bata fito daga bedroom bane yasa zuciyar ta yin zafi, cikin zafin rai ta nufi d’akin Sheemah, a harzuk’e ta tura k’ofar d’akin, ganin halin da Sheemah take ciki ne yayi mummunan d’aga mata hankali ta k’arasa inda take da sauri, cikin hanzari ta fito ta kira driver suka d’auki sukayi hospital da ita, itama mawuyacin halin datake cikine yasa dole aka kwantar da ita.
BAYAN SATI D’AYA
Yau jirgin su Hajiya Rabi yayi landing a Nigeria, suna isa gida ko bari batayi ta huta ba ta kira boka jimrau, ” sannu da dawowa Hajjaju an dawo lafiya?
A tak’aice tace ” Alhamdulillah, ya maganar mu dakai kace in bari sai na dawo Nigeria, to na dawo dariya yayi sannan yace ” haba Hajjaju gaggawar mekikeyi ne?
Cike da k’usawa tace ” hmmmmm Boka Jimrau dan baka san yadda nake jin yarinyar a raina bane, ina yi mata matsanancin so na bam mamaki, dariya ya kuma yace ” kinje gidan k’awarki? “A’a ta bashi amsa, “bakiji labarin babban d’anta yayi aure ba? d’anki taja had’i da cewa naji mana, akwai abinda d’ayan mu zayyi batare da sanin d’ayan ba, “akwai Boka Jimrau yace had’i da cewa ki bari ki huta ki nutsu sannan sai muyi maganar, ta bud’e baki zatayi magana ya dakatar da ita had’i cewa ” karki sake kira na har sai kinje gidan Hajiya Lailah, dan babu wani abinda zan iya yi miki har sai kinje gidan tukunna, yana kaiwa nan bai bari tayi magana ba ya kashe wayar, wayar Hajiya Rabi tabi da kallo dan ta kasa fahimtar abinda Boka yake nufi.
Jin yace karta k’ara kira har sai ta je gidan Hajiya Lailah ne yasata mik’ewa da hanzarinta bata ma bari ta huta ba ta nufi gidan.
A parlor ta iske Hajiya Lailah zaune tana kallo amma gaba d’aya hankali ta baya kan kallan dan har yau ba’a sallamo Haidar da Sheemah, da sauri Hajiya Rabi ta k’arasa had’i da rungumar Hajiya Lailah cike da jin dad’i Hajiya Lailah tace ” kawata yaushe a gari? shine kikayi min zuwan bazata? dariya Hajiya Lailah tayi had’i da cewa so nake nayi surprising naki, “aiko kinyi cewar Hajiya Lailah, bayan sun gama zantuttukan su, sunci abinci Hajiya Rabi ta kalli Hajiya Lailah tace ” ni ko k’awata ina surukar tamu kuma sahibarki abar k’aunarki?
Dariya Hajiya Lailah tayi had’i da rik’o hannun Hajiya Rabi tace ” me kike ci na baka na zuba, taso muje ki ganta, da sallama suka shiga part d’in su Kausar inda suka iske ta daga ita sai mini skat black da red half best, tayi peaking gashin kanta da red reborn isan ka kanta kamar ‘yar baby tayi masifar kyau halittun jikinta sun k’ara fituwa sosai d’as.
Fuskar Hajiya Lailah d’auke da murmushi ta k’arasa inda Kausar ke zaune ta mik’ar da ita tsaye had’i da rik’e ta kalli Hajiya Rabi dake tsaye kamar mutum mutumi tayi sororo kamar doluwa tace ” ga surukata nan.
Wani irin mahaukacin fad’uwa gaban Hajiya Rabi yayi yayinda cikinta ya bada k’uluuuuuuuu, idanuwanta sukayi ja, cikin rawar baki tace “…………