GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiko Sanata Sambo yayi hakan ne danya k’ureta yaga iya gudun ruwanta, a hankali ya mik’a hannunsa ya fara shafo mata jikinta, yana bata hot romance amma ita jin jikinta take kamar yana watsa mata wuta saboda tsananin zafi da zugin da jikinta ke mata, jin ya dage ne yasa ta mik’ewa da sauri tace ” Alhaji bari na shiga toilet na fito da sauri shima ya mik’e had’i da rungumo ta ta baya yace ” nima toilet d’in zan shiga ya fad’a yana sakar mata murmushi wanda ita tasan ma’anar murmushin ganin haka yasata daurewa ta bada kai bori ya hau.

Washe gari da safe Sanata Sambo ya sanar da wasu daga cikin ‘yan uwnsa da abokanan sa da daddare zasu rakashi nemarwa Fahad aure, bayan sallahr ishsha motocin su Sanata sukayi parking a k’ofar gidan su Kausar, bayan anyi musu suka shiga, k’anin Sanata Sambo ne yayi magana bayan sun gama gaisawa ” mun zo kan maganar yarinyar wajenka da yaron wajen mu, murmushi k’anin Malam yace ” badamuwa mun san da maganar, nan dai suka tsayar da maganar auren da ranar auren akan juma’a mai zuwa za’a d’aura auren nan da kwana shida kenan, kafin su Sanata Sambo su yafi sai da sukayi komai na al’ada da farillah tun daga kan su kud’in auren aure kudin nagani inaso, kud’in gaisuwar iyaye da kud’in sadaki gaba d’aya suka had’a suka bada dubu d’ari biyar 500k.

Washe garin ranar Malam ya kira Kausar da Ummanta suka zauna a gabansa sai da ya niffasa sannan ya kira sunanta ” Kausar a hankali ta d’ago kanta had’i da cewa ” na’am, sai da ya d’auki d’an lokaci sannan yace ” Kausar ina so na sanar dake wata magana amma ina tsoro dan ban san yadda zaki karb’e ta ba,, amma ya zama dole na sanar dake, Kausar kin san dai nine mahaifin ki bazan kuma tab’a cutar dake ba dan nafi kowa sanki naki kowa sanin zafinki da darajarki, bazan tab’a kaiki inda za’a cutar dake ba, bazan tab’a kuma had’aki da wanda zai cutar dake ba, nasan kuma ke kanki kinsan hakan, nasan duk hukuncin dana yanke akanki bazaki tab’a k’in yi min biyayya ba, dan haka nake son sanar dake ranar juma’ar nan mai zuwa nan da kwana biyar d’aurin auren ki dan na bada aureki da k’arfi k’irjinta yayi muguwar bugawa, a firgice ta d’ago kai ta kalli Malam da Ummanta ganin duk ita suke kallo yasata saurin yin k’asa da kanta.

Shiru tayi ta koda yin kwakwkwaran motsine balle ta iya bud’e baki tayi magana abin kamar a mafarki take jin wai ita za’a d’aurawa aure nan da kwana biyar kacal da mutumin dabatan kowaye ba bata tab’a ganin shi ba, siririn hawayen daya zubo mata tasa hannu ta goge, jin tayi shiru yasa Malam cewa ” ya naji kinyi shiru ko dai baki amince bane, bakinta na rawa tace ” bakomai na amince Allah ya kaimu lokacin, in sha Allah zan kasance mai bin umarnin ku dayi muku biyayya a ko’ina a kuma kan komai, duk abinda kuka ga ya kamata dani kawai kuyi ba sai kin sanar min ko kunyi shawara dani ba, a hankali Malam ya shafa kanta had’i dayin murmushin jin dad’i yace ” Allah yayi miki albarka, ya kuma tsareki daga dukkan sharri da abin k’i, Ubangiji ya kare min ke ya d’oraki akan mak’iyanki, in sha Allah sai kinyi alfahari da wannan auren, sai kinyi alfahari da mijin naki, a hankali Kausar da Ummanta suka ce “Amin, a hankali ta mik’e ta nufi d’akin su.

Ana saura kwana uku d’aurin aure su Hajiya Lailah da k’awayenta suka kawo lefe iya kud’i kam Hajiya Lailah da Sanata Sambo sun kashe a lefen dan akwati 15 akayi harda d’inkakkun kaya kala 40 wanda Hajiya Lailah ta bada Oder su Dubai, tsayawa had’uwar lefen b’ata lokaci ne, duk wani abu da ake yi na shirye-shiryen biki Ni’ima ce keyi dan babu abinda Kausar keyi, dakyar ma tayi lalle ja da bak’i aka sharfa mata kitso ubansu, Hajiya Lailah ta yi Oder masu gyaran jiki aka gyare mata Kausar d’inta tsaf, dan ko gidan lalle da kitso tare sukaje da Hajiya Lailah dan bata matsawa ko nan da can kwata-kwata bata k’aunar abinda zai nisantata da Kausar d’inta, mutane har mamakin irin son take yi mata suke.

Dakyar Hajiya Lailah ta matsawa Fahad yaje shida abokanan sa suka gaida iyayen Kausar , amma tsaya yaga Kausar d’in ba, ita kuwa Hajiya Lailah yadda Fahad ke nuna kiyayyarsa ga Kausar abin ba k’aramin dad’i yake yi mata ba, bata k’aunar abinda zai dai-daita tsakanin shi da Kausar d’in, ranar juma’a bayan an idar da sallah juma’ar aka d’aura auren Kausar da Fahad, Allah kad’ai yasan iyakar mutanen da suka sakawa auren albarka.

Duk wannan sha’anin da akeyi Hajiya Rabi bata sani ba dan mijinta ya matsa mata wannan karan akan dole sai ta bishi China haka nan ta bishi ba’asan ranta ba amma duk shirin bikin da akeyi Hajiya Lailah na sanar da ita cewar Fahad zayyi aure dayake akwai yarda da amana mai k’arfi a tsakanin su yasa Hajiya Lailah bata iya b’oyewa Hajiya Rabi gaskiyar dalilinta na aurawa Fahad Kausar ba, ta gaya mata komai tas, amma Hajiya Rabi bata san Kausar ce wacce take haukan so ba, dan har yau har gobe Kausar na nan zaune daram a zuciyar ta, kuma tana nan akan kudurinta na cewar zata iyayin komai akanta, zata iya rabuwa da kowa akanta tana iya kuma kashe ko nawa ne matuk’ar zata mallake ta.

Da yamma gaf da magriba Hajiya Lailah ta aiko masu make up aka tsalawa Kausar kwalliya ta uban su, bayan an gama kwalliyar aka fito da Kausar domin kaita wajen iyayenta dan tuni Hajiya Lailah ta aiko da motocin d’aukar amarya, nasiha mai sanyaya jiki da ratsa zuciya Malam da Umma sukayi mata sannan aka wuce da Kausar zuwa gidanta, a parlor Hajiya Lailah aka dank’a mata amanar ta sannnan aka kaita b’angaren ta dake cikin gidan, wanda nan ne b’angaren Fahad, wanda yake d’auke da 3 bedroom 1 parlor sai 4 toilet & bathroom, kowanne bedroom yana da toilet d’aya sai kuma toilet 1 a parlor, parlor babba ne sosai daga gefe akayi kitchen da dining area, royal chairs ne a parlor masu shegen kyau da tsada haka ma a bedroom daga d’aya royal bed ne, wanda suka amsa sunansu royal bed, dinning table ma royal ne, kai gidan Kausar da Fahad ya gaji da had’uwa dan an kashe mak’udan kud’i wajen tsara gidan, bayan ‘yan kawo amarya sun watse Hajiya Lailah ta shigo d’auke da abinci, ganin mugun kyan da Kausar tayi take matsanancin kishi ya saukar mata, dakyar ta kanne kishin, ta bata taci sannan tace karta sake ta rink’a wahalar da kanta wajen girki ita zata rinka yi musu a b’angaren su.

Hajiya Lailah na komawa b’angaren ta ta shige d’aki had’i da rufe k’ofa ta kira Boka Jimrau ta sanar dashi ta fara amfani da maganin daya bata, murmushi yayi yace ” wani hanzari ba gudu ba, da sauri tace ” me kuma? “Karki sake ki bari Fahad ya kwanta da ita, dan matuk’ar ya sadu da ita duk aikin mu ya tashi a banza, gabanta yayi muguwar fad’uwa jin abinda Boka jimrau yace, amma data tuna Fahad bai wani damu da Kausar d’in ba sai tayi murmushi tace ” bakomai karka damu da wannan,tana haka taji shigowar Fahad da sauri ta kashe wayar had’i da mik’ewa ta fita, a parlor su ta iske shi zaune da kayan d’aurin aure a jikinsa bai cire su ba, a hankali ta zauna kusa dashi ta jawo shi jikinta tana shafa kansa.

” yanzu yaro na ya girma ya zama cikekken mutum magidanci, dan Allah ga amanar Kausar nan na bata dan ita rayuwa ta ce ina matuk’ar santa fiye da yadda nake son nakai da sauri Fahad ya d’ago kai ya ta, sai lokacin ta gane ta kwafsa murmushin yak’e tayi gami da cewa ” saboda san da nake maka ne yasa nake santa saboda kai ne komai nawa Fahad, sai dai dan Allah ina neman wata alfarma daga gare ka murmushi yayi yace “ina jinki Momy k’ara raunana muryarta tayi sannan tace ” karka sake ka kusance, kai ni baba ma san ko d’aki d’aya ku had’a balle wani abu ya shiga tsakanin ku, da mamaki k’arara a fuskarsa ya kalle ta, amma sai ya tsinci kanshi dayi mata murmushi yace “kima daina tunanin akwai haka tsakani na da ita ya fad’a yana mik’ewa tsaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button