
Mik’ewa yayi yana niyyar fita, har ya kai bakin k’ofa ya juya karaf suka had’a ido da sauri ta mayar da kanta k’asa, murmushi ya kuma yace ” sannan ki rink’a sakawa k’ofar parlor key koda ina gida ta yadda duk wanda zai shigo sai yayi miki nocking, kinga babu wanda zai rink’a shigawa kai tsaye, murmushi tayi masa batare dace komai ba, dan ta fahimci inda ya dosa, shima murmushin ya kuma yayi mata sannan ta ya fita.
Dauriya kawai Hajiya Rabi keyi dan iya tashin hankali ta shigeshi, ko sallm bata iya tsayawa tayiwa Hajiya Lailah ba tayi tafiyarta, tana shiga gidanta tayi cilli da hand bag da mayafinta ta shiga safa da marwa tana neman fita, ” ashe shiyasa Boka Jimrau yace na fara zuwa gidanta mean yasan komai, to me hakan yake nufi, mace dake mugun so ita aminiyata ke yiwa mahaukacin so, macen dake da burin yin lez da ita, ita aminiyata ta makance akanta, cikin mugun tashi hankali, firgitaccen tsoro da fargaba, matsanancin bak’in ciki tace ” wallahi bazan tab’a iya hak’ura da Kausar ba.
Ta kai wajen 2hrs tana nemarwa kanta mafita amman ta rasa, tana cikin haka Boka Jimrau ya fad’o mata da sauri ta nufi inda tayi wurgi da hand bag d’inta ta bud’e ta ciro phone hannu na rawa tayi dialing number Boka Jimrau bugu d’aya yayi picking.
Cike da izza ya d’aga wayar yace ” kinje gidan kenan? cikin rawar murya tace ” eh naje, jin yadda muryarta ke cracking yasashi tuntsurewa da mahaukaciyar dariyar mugunta, wani mugun b’akin ciki ya kuma tokare Hajiya Rabi cikin takaici tace ” ai dama ba’a tab’a baku amana ku maciya amana ne, cikin b’acin rai ya buga mata wata irin fitananniyar tsawa yace ” ke bana san sakarcin banza, duk da Hajiya Rabi tayi mutuwar tsoro, amma halin datake ciki ne ya kawar mata da tsoran dan zuciyar ta ta gama k’ek’ashewa, cikin dakewar rai tace ” dalla Malam karki kuma yi man tsawa sakarai shashasha kawai, idan har kai kana da amana za’a had’a baki dakai aci amanata ne.
Ganin ran Hajiya Rabi yayi mugun b’acin tunda duk tsoransa da take ji amma gashi harta iya yi masa tsawa yasan akwai matsala, kuma yasan da Hajiya Rabi ya dogara dan duk wasu manyan matan dayake ji dasu itace ta had’a shi da su, dan haka ya sausauta murya yace ” Hajiya ki nutsu ki dawo cikin hayyacin ki, ni dai bani da abinyi sai dai shawara tunda Hajiya Lailah ta gaya miki duk yadda aikin danayi mata yake, kuma gaskiya aikin yana da matuk’ar k’arfi makarin aikin d’aya tak, da sauri tace ” meye makarin aikin?
“Fahad ya kwanta da Kausar shine kad’ai makarin aikin, cikin rashin fahimta Hajiya Rabi tace ” kamar ya ban gane ba? “Idan Fahad ya sabu (sex) da Kausar duk wani aiki da akayi na asiri zai karye, amma fa shima Fahad d’in anyi masa asirin hana shi kusantar ta, cikin b’acin rai Hajiya Rabi tace ” ka karya aairin da akayi tsananin Fahad da Kausar ko nawa kake so zan baka, sauran aikin kuma ka barmin, dariya Boka Jimrau yayi had’i da cewa ” hatsabibiyar mace, amma ni a gani na kafin duk ayi wannan ki fara zuwa ki samu Hajiya Lailah ku fahimci juna tukunna ki bayyana mata Kausar itace wacce kike so kema, tunda ita abokiyar barikinki ce kuma ba’a b’oyewa abokin harka, harka, idan tak’i ne sai a buyo mata ta bayan gida.
Shiru Hajiya Rabi tayi nad’an wani lokaci sannan tace ” ok badamuwa, bari na koma gidanta yanzu duk yadda mukayi zakaji ni, ta fad’a tana surar hand bag da mayafinta, a parlor ta kuma iske Hajiya Lailah ita kad’ai dan Ummi da wata k’anwarta suna asibiti wajen jiyar Haidar da Sheemah, da sauri Hajiya Lailah ta mik’e tana cewa ” ina kikaje ne k’awata bako sallama na fito ban iske ki ba, sai mai gadi ne yake sanar min kin fita, murmushi Hajiya Rabi tayi had’i da zama akan sofa ba tare data ce komai ba, yanayin ta Hajiya Lailah ta kalla ta fahimci akwai damuwa dan na gani tana cikin matsala.
A hankali Hajiya Lailah ta zauna a kusa da ita tare da dafa kafad’arta tace” kawata ya akayi ne, na fahimci kina cikin damuwa da tashin hankali, rik’o hannunta Hajiya Rabi tayi cikin nata ta kalle ta face ” kawata ai dole ki ganni a cikin damuwa dan mun had’a abinda muke tsananin so, cikin rashin fahimtar abinda Hajiya Rabi ke nufi Hajiya Lailah tace”kamar ya bangane ba?
A hankali ta sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da k’ara rik’o hannunta cikin nata tace ” eh abinda duk muke haukan so ni da ke d’aya ne wato KAUSAR, da sauri Hajiya Lailah ta zame hannunta daga cikin na Hajiya Rabi gami da mik’ewa tsaye a razane tace ” what?
A hankali Hajiya Rabi ta mik’e tsaye tana fuskantar Hajiya Lailah tace ” eh k’awata yarinyar dana dad’e ina baki labarinta ba wata bace illa Kausar matar Fahad, a kid’ime Hajiya Lailah ke kallan Hajiya Rabi can kuma ta tuntsure da dariya tare da cewa ” haba k’awata nasan ma wasa kike min bada gaske kike min ba ko?
Dafa kafad’arta Hajiya Rabi tayi tace ” no k’awata bada wasa nake miki ba, da gaske nake miki nasan kuma kin san yadda kike san Kausar haka nake santa nima, zamu iya yin had’a wajen biyawa kan mu buk’ata da ita nasan bazaki tab’a juya min bay…… da sauri Hajiya Lailah ta dakatar da ita had’i dasa hannu ta zame hannun Hajiya Rabi dake kafad’arta ta kalleta ido cikin ido tana murmushi tace ” kin ki kuskure da kike tunanin zan iya yin had’aka da wani mahaluk’i a duniya akan Kausar, Kausar tawa ce ni kad’ai mallaki nace, ko d’an na ciki na hana shi ya mallake ta a matsayin matarsa, ko Fahad ban yarda wani abu ya shiga tsakanin sa da ita har yanzu ba, kin san meyasa? ta tambayi Hajiya Rabi, “hmmm saboda ina mahaukacin santa, ke bari kiji Rabi bazan tab’a iya yin had’aka da Kausar da kowa ba, a kanta zan iyayin komai, kin san irin wahalar dana sha akanta, kin lokacina dana b’ata, kin iyacin mak’udan kud’in dana kashe, kin sa abubuwan danayi duk akanta sannan kizo min da wata banzar magana irin taku ta tsofaffun ‘yan bariki, ni zakiyiwa makirci daga ganin yarinya kice itace wacce kike so, dama ace ban san ki bane, ni da ke karta san kar.
“Kwaryar sama ce data k’asa dan haka fice min daga gida ta fad’a tana nunawa Hajiya Rabi k’ofar fita, a hankali Hajiya Rabi ta matso daf da ita tace ” haba k’awata ki tuna tsawon shekarun da muka d’auka numa tare, ki tuna lokacin da muka d’auka muna harkokin mu muna rufawa kanmu asiri ba tare da kowa ya sani ba, karmu bari lokaci d’aya wani k’ank’anin abu ya raba mu ya shiga tsananin mu, dan Allah k’awata, a fusace Hajiya Lailah tace ” k’ank’anin abu fa kikace? a wajenki yake k’ank’anin abu, ke kika d’auke shi k’ank’anin abu amma ni a wajena babban abu ne wannan, Hajiya Rabi ta bud’e baki zata kuma magana Hajiya Lailah ta dakatar da ita da sauri had’i cewa ” get out please, ki fita nace miki, ganin bata niyyar fita yasa Hajiya Lailah hankad’ata har farfajiyar gidan ta tako gaban ta cikin b’acin rai ta nuna ta da yatsa tace ” kuma karki manta kamar yadda kika ji nace miki zan iya yin komai a kanta to ina nufin komai.
Murmushi Hajiya Rabi tayi had’i da girgiza kanta ta kalli Hajiya Lailah tace ” kin tafka babban kuskure Lailah, amma zakiyi nadamar abinda kikayi da kanki, nayi miki alk’awarin hakan tana kaiwa nan ta shige motarta cikin matsanancin takaici da mamakin abinda aminiyarta tayi mata, tun a mota ta kira Boka Jimrau ta zayyane masa duk abinda ya faru tsakanin ta da Hajiya Lailah, bayyi mamakin hakan ma dan yasan irin san da take yiwa Kausar, akanta zata iyayin fiye da haka ma, dariya yayi yace ” ki kyale ta tunda an bita ta laluma ta nuna ita cikekkiyar ‘yar akuya ce, yanzu zan karya aspirin dake tsakanin Kausar da Fahad sauran aikin kuma naki ne, amma ki tuna babu abinda zai karya asirin illa saduwar aure tsakanin Fahad da Kausar.