GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan kenan

Wajen k’arfe 11:00pm na dare Kausar na kwance a d’akinta tayi d’ai-d’ai akan bed sanye da kayan baccinta hankalinta kwance dan yanzu bata fargabar komai, a hankali taji an hawo gadon an matso daf da ita, a zaton Kausar Fahad ne shiyasa bata yi yunk’urin komai ba ta k’ara bajewa sosai a jikinta dan ta tabbatar yanzu babu mai shigo mata d’aki tunda daga Haidar har Sheemah suna hospital.

Cikin nutsuwa taji an fara shafa mata ko’ina na jikinta cikin salo da kwarewa idanta ta k’ara runtsewa fuskarta d’auke da murmushi takai hannu danta shafo fuskarsa caraf taji an rik’e mata hannunta da sauri, had’i da kaiwa hannun sumbata ta ko’ina, d’aya hannun takai ta shafo kan ta zuwa fuskarta jin kamar ba Fahad yasata bud’e idanta da sauri kasancewar d’akin ba haske ya hana Kausar ganin kowaye amma ta tabbatar ba Fahad bane, cikin firgici ta bud’e ta fara k’ok’arin mik’ewa amma taji an danne ta da k’arfi had’i da rufe mata bakinta, da k’arfi tasa hak’orant ta gantsawa hannun cizo, washhhh Hajiya Lailah tace jin rikitaccen zafin cizon ya ratsa mata har kwakwalwarta, a razane ta shiga yarfa hannun, murya Kausar ta bud’e iya k’arfinta ta shiga tsala ihuuuuuuuu tana kiran sunan Fahad da k’arfi.

A gigice Fahad ya ya fito daga d’akinsa dai-dai lokacin da Hajiya Lailah ta fito daga d’akin Kausar a guje, kasancewar shigar maza Hajiya Lailah tayi yasa Fahad bai fahimci mace bace ita, a sukwane yabi bayanta da gudun bala’i yana san kamata, cikin sa’a Fahad ya rik’o hannunta komawa suka shiga sosai, shi yana k’ok’arin cire mask d’in data ta rufe fuskarta ita kuma tana k’ok’arin kwace kanta, Fahad na gaf da cire mask d’in yaji Kausar ta kwala mashi a gigice cikin matsanancin firgici da sauri ya saki Hajiya Lailah ya nufi cikin part d’in su a parlor sukayi kacib’us dashi da sauri ta fad’a jikinsa tana sakin kuka.

Duka hannayensa ya saka ya k’ara matseta da jikinsa.

Washe gari da safe bayan sun gama breakfast Kausar na zaune akan sofa yayinda da Fahad ke zaune a gefenta yayi zufi acikin tunanin wanda yake shigo musu gida yanzu, a hankali ya d’ago da kansa ya kalli ya Kausar cikin sanyin murya yace ” nayi tunani mai zurfi dan gano wanda yake shigo mana gida amma na kasa saboda kinga Sheemah da Haidar dai basa nan suna hospital har yanzu ba’a sallamo su ba, haka Dady bayanan, da sauri Kausar ta rufe masa bakinsa had’i cewa ” ka daina ma zaka Dady acikin maganar nan dan na tabbatar bazai tab’a yin haka ba, kallan ta ya kuma yi yace ” to waye?

Daga k’ofar parlor d’in su yaji yaji ance ” wacce tafi Sheemah da Haidar shaid’anci da hatsabibanci ce, wacce tafi kowa kusanci dakai ce, da sauri Fahad da Kausar suka mik’e had’i da kallan bakin k’ofa a tsaye suka ga Hajiya Rabi tana kallan su fuskarta d’auke da murmushi…….

MOMYN ZARAH
[28/01, 06:48] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

42

A firgice Fahad ya kalle ta had’i da nunata da hannunsa yace” idan na fahimci abinda kike nufi means kin san wanda yake shigo min gida, murmushi taci gaba dayi masa had’i da cewa ” eh sosai ma, kuma kaima ka san ni, cikin rashin fahimta ya kalle yace ” kamar ya?

” Kaga ni yanzu bani da abinda zan iya ce maka tunda kona gaya maka wanda yake shigo maka gida ba lalle ne ka yarda ba, saboda tunaninka bazai tab’a kaiwa nan ba, amma zan baka shawara sannan zan sanar dakai mafita matuk’ar kana san k’aucewa wannan shaid’aniyar matar sai ka kusanci matarka dan a gobe duk wani shirin ta zai kammala, gobe ne zaku cika wata uku cif da aure kuma a gobe burinta zai cika akan Kausar ta fad’a tana kallan Kausar d’in, wallahi wallahi Allah idan har bakayi k’ok’ari ka kusanci matarka a daren yau ba, zakayi danasani mai girma har izuwa k’arshen rayuwarka, sannan idan ka kasance ta karka sake ka fita daga d’akin har fitowar alfijir.

Tana kaiwa nan ta juya tana niyyar fita da sauri Fahad yasha gabanta yace ” na rok’oki na kuma had’aki da girman Allah kiyi min bayani yadda zan gane, murmushi tayi masa tace ” Fahad kasan dai bana nan akayi bikinku balle na san wanne date akayi, sannan ban san ana shigo maka gida ba tunda baka tab’a sanarwa da kowa hakan ba, asalima har yau baka sanarwa da ko iyayenka ba, sannan ya akayi nasan baka tab’a kusantar Kausar ba, sai ka zauna kayi tunanin ya akayi na san duk wad’annan abubuwan, kayi tunani sosai Fahad, kai da kanka zaka gano waye, dan kona gaya maka bazaka tab’a yarda ba, kai koda duk duniya ne zasu fad’a maka bazaka tab’a gaskatawa ba matuk’ar ba kaine ka gani da idanka ba.

Harta kai bakin k’ofa ta kuma jiyowa tace ” ka tuna mafita dai d’aya ce na kuma gaya maka ita karka sake gari ya waye batare daka kusanci Kausar ba, tana kaiwa nan bata jira abinda zai ce ba ta fita.

Kallan kallo aka farayi tsakanin Fahad da Kausar, yayinda Kausar ta shiga girgiza mishi kanta hawaye na zuba, da sauri ya fita ya nufi part d’in Hajiya Lailah dan ya sanarta da ita abinda ke faruwa, ganin bata parlor yasa shi danna kai bedroom d’inta nan ma bai iske ta ba, ya kai bakin k’ofa yayi tuntub’e ya fad’i a dai-dai k’ark’ashen gado, tsaki yayi ya yunk’a zai tashi idansa ya hango wani abu a k’ark’ashen gado har zai tashi yaji gabansa yayi mugun fad’uwa a hankali ya jawo abinda ya gani da k’arfi k’irjinsa ya buga ganin kayan da aka shiga gidansa dasu a daren jiya harda mask d’in da aka rufe fuska dashi da sauri da sauri gabansa yaci gaba fad’uwa yayinda tsoro had’i da fargaba suka dirar masa take maganganun Hajiya Rabi suka shiga dawo masa a kwakwalwarsa , take jikinsa gaba d’aya ya d’auki kerrma.

Da sauri ya mayar da kayan inda ya gansu yayi saurin barin d’akin, yana komawa part d’in su ya shige bedroom d’insa ya fad’a duniyar tunanin, kwata-kwata yak’i yarda cewar d’aya daga cikin iyayen sa ke shigo masa gida dan ya tabbatar babu abinda zai kawo su, akan haka ya tsaida tunanin sa, tunowa da maganganun Hajiya Rabi yasa shi saurin mik’ewa ya nufi bedroom d’in Kausar, daga ita towel ya iske ta ta fito daga wanka, a hankali ya zauna a bakin gado, take yaji wani ya tsarga mata, yayinda Hajiya babba ta harba, idanunsa su kayi ja, a nutsu ya d’ago red eyes d’insa ya zuba mata, ya fara k’are mata kallo tun daga kanta har k’afarta, idansa ya tuntse gam had’i da kwanciya rigingine akan bed, idansa a rufen ya kira sunanta cikin mutuwar jiki.

Kausar da tun maganar da Hajiya Rabi ta fad’a take a matuk’ar tsorace dashi, musamman yanzu dataga yadda ya koma in 1 second, ta amsa a tsorace, yace ” zo, shiru tayi taci gaba da tsayiwa a inda take tsayen, yana yadda bai motsa ba yace ” nace kizo ko?

Cikin tsoro ta fara takowa harta iso bakin gadon, still idansa a rufen yana daga kwancen yace ” zauna, a hankali tad’an d’osana ta zauna d’an nesa dashi, bai motsaba yace ” shekararki nawa?

Cikin sanyin jiki tace ” 17yrs, da sauri ya bud’e idanta ya mik’e zaune had’i da cewa ” what? yanzu zaro duka idanuwansa waje, sunkuyar da kanta k’asa tayi ta tare tace masa komai ba, ” kin gama secondary school? “eh na gama a wannan shekarar, ta bashi amsa, kamar daga sama taji yace ” kin fara period? da sauri ta d’ago kanta aiko karaf suka had’a ido, saurin mayar da kanta k’asa tayi ta shiga wasa da ‘yan yatsunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button