GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Fahad dake tsaye ya kasa yin motsi gaba d’aya jikinsa kerrrrma yake, zuciyar sa ta shiga bugawa da k’arfin bala’i, gudun jinin ya kar’u, mak’ogwaran ya bushe bakinsa yayi masa d’aci yayinda zuciyar sa ta gama k’ek’ashewa ta bushe, a hankali abubuwa da dama suka shiga dawo masa tun daga daren auren su data hana shi kusantar Kausar da ranar data ce idan ya sake ya kusance bata yafe masa ba, da ranar dace daya ganta a bedroom d’in Kausar

, ya tuno maganganun data yake yawan fad’a akan Kausar d’in ya tuno yadda take kallan Kausar da yadda take rungumarta, da kalaman datake yawan fad’a akanta, ya kuma yuno maganganun da Hajiya Rabi ta fad’a yau da safe a ransa yace ” hakan na nufin my mother she is still lesbian, after my sister, my Mom, my sister and my brother they are all want make sex with my own wife, take yaji numfashinsa ya d’auke cak, idanuwansa sun kakkafe masa, jiri ya d’ebe shi ya fad’i k’asa luuuuuuuuu……….

MOMYN ZARAH

[29/01, 11:44] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

43

Da k’arfi Kausar ta fasa k’ara had’i da nufarsa a gigice cikin matsananciyar kid’ima, tama manta da wani ciwon dake jikinta, fad’awa tayi kansa ta shiga jijjiga shi, tana kiran sunansa cikin matsanancin kuka, kai Sanata Sambo ya dafe ya shiga fad’ar ” Innalillaihi wa’inna ilaihirraji’un, a gigice Sheemah tayi kitchen ta d’auko ruwa ta zubawa Fahad, da k’arfi ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin kuka ya farka, a rikice Kausar ta rungume shi itama tana kukan bak’in ciki.

Dakyar Haidar da Ummi suka rik’e Hajiya Lailah yayinda take ta fusge-fusge tana surutai ta shiga fad’ar abubuwan da tayi a rayuwarta tun daga farko har k’arshe kaf, tun daga ranar dataje gidan Hajiya Rabi nemar shawara har zuwa lokacin data fara lesbian da Ummi, har irin bad’alar da suke aikatawa, da lokacin dataga Kausar da irin mahaukacin so da fitinanniyar sha’awar da take yi mata, da dalilin dayasa ta aurawa Fahad ita, da labarin Boka Jimrau duk babu abinda bata fad’a ba, Ummi najin an tuna mata asiri ta fasa kuka tace ” wallahi Allah kwad’ayi da san abin duniya ne yasa na amince mata amma wallahi ban tab’a yin lesbian ba sai akanta da Sheemah, “what!! Haidar yace da k’arfi, Fahad na zaune Kausar ta rungume shi a jikinta, ta kwantar masa da kansa a k’irjinta, in banda matsanancin kukan bak’in ciki babu abinda Fahad keyi, da ido kawai yake bin su ya kasa cewa komai dan shi ya kasa tantance a duniyar da yake, shin a raye yake ko a mace.

“Kina nufin kina lesbian da uwa da ‘ya, kuyi lez da Sheemah sannan kuma kiyi da mahaifiyar ta? Haidar ya fad’a razane yana kallan Ummi, cikin matsanancin kuka Ummi tace ” wallahi duk su suka kawo kansu bani na neme su ba, itama ta bada labari tun daga ranar da Hajiya Lailah ta neme ta har irin abubuwan da suke aitawa ta fad’an musu har group lez sukeyi, har zuwa ranar da Sheemah ta neme ta, cikin kuka Sheemah tace ” wallahi nima sharrin shaid’an ne da kuma bin shawarar k’awaye a koda yaushe shine ya jefani a halaka, da kuma rashin tsayayyun iyaye na gari masu kula da yaransu da harkokin su a koyaushe, ni rashin iyaye na gari ne ya jefani a halaka dan Allah yasani tunda na gama secondary school naso yin aure, amma kasancewar bani da tsayayyun iyaye sai na bi shawarar k’awaye.

In banda ” Innalillaihi wa’inna ilaihirraji’un babu abinda Sanata Sambo ke maimaitawa, yayi masifar shiga mummunan tashin hankali, wai duk wannan bad’alar da badak’alar a gidansa ake aikatawa, lalle ya aikata babban kuskure a rayuwarsa ta duniya shi da kansa ya tarwatsa gidansa da ahlinsa dan shi kansa yasan ba wani bane yayi sanadiyyar fad’awar Hajiya Lailah da yaran sa hakala ba sai shi da kansa, saboda ya d’aukaki harkokin siyasarsa fiye da komai a rayuwa, ya d’auke kud’i da arziki sunfi komai fahimmanci, ya d’auka idan ya bawa iyalansa kud’i kamar ya gama basu duk wani farin ciki da cikekkiyar kulawa ta duniya ashe ba haka bane, ‘yarsa guda d’aya tilo da matarsa ta suna aikata mafi girman laifin wajen Ubangijin talikai.

Dan tunda aka kafa duniya bai tab’a jin an kifar da duniya saboda k’arya, shaye-shaye ko zina ba, amma an kifar a zamanin Annabi Lud’ saboda lesbian & gay, (Luwad’i) ya kasance laifi mai girman gaske a wajen Allah, ko sunan shi aka kira sai sammai da k’ai sun girgiza Ubangiji yayi fushi sai mala’iku sun karanta suratul iklas, amma yau an waye saboda sakacin sa matarsa ta sunnah da ‘yarsa ta cikinsa abinda suke aitawa kenan take yaji wahayen takaici na gangarowa daga idansa, cikin matsanancin bak’in ciki ya kalle Haidar yace ” ku saka ta a d’aki ku rufe zan kira malamai su zo suyi mata addu’a wata k’ila Allah yasa a dace tunda aikin sihiri ne, da kyar Sheemah da Haidar suka danna Hajiya Lailah a d’aki suka rufe, Sanata Sambo ya fita waje yana waya, mijin Hajiya Rabi ya kira yace ” komai yake yazo gidan shi yanzu shida matarsa yana fad’a bai jira abinda zai ce ba ya kashe wayar, direct wajen limamin unguwar ya nufa, ya sanar dashi halin da ake ciki, limamin yace bakomai zai kira mutane 5 mu had’u zasu zo in sha Allah bayan sallar la’asar

A tare malaman da su Hajiya Rabi suka shigo lokaci d’aya, da sauri Alhaji mijin Hajiya Rabi ya k’arasa inda Sanata Sambo ke magana da malaman,Hajiya Rabi kuwa tunda taji kiran gabanta keta fad’uwa yana dukan uku-uku ta rasa mai yasa kwata-kwata hankalinta yak’i kwanciya, hannu Alhaji ya fara mik’awa masa suka gaisa, umarni Sanata Sambo yayi musu dasu shiga gidan gaba d’aya.

Fahad na inda yake ko motsawa bayyi ba yadda Sanata Sambo ya fita ya barshi haka ya dawo ya iske shi acikin mawuyacin hali, yayinda Kausar ta mannashi da k’irjinta tana zubar da hawaye, murmushin k’eta Hajiya Rabi tayi ganin halin da Fahad ke ci ya tabbatar mata da hak’onta ya cimma ruwa, bayan duk sun zauna a babban parlor Sanata Sambo ya umarci Sheemah da Haidar akan su fito da Momyn su, cikin mutuwar jiki suka mik’e, Hajiya Lailah na rik’e a hannunsu suka shigo parlor tana fisge-fisge da sambatu tana ci gaba da fad’ar abubuwan da sukayi ita da Hajiya Rabi,a razane Hajiya Rabi ta mik’e tace ” Haukacewa Hajiya Lailah tayi?

Ai Hajiya Lailah nayi arba da Hajiya Rabi tayi kukan kura tayi kanta a haukace, kasa motsawa daga inda take tayi, sai su Haidar ne suka tare ta da sauri, dakyar sukayi controlling d’inta sannan malaman suka fara aikin su, Fahad ya kasa komai sai binsu da ido kawai da yakeyi kamar zararre, sai aka d’auki lokaci mai tsayi ana addu’a da karatun Qur’an sannan aka samu bak’in aljanin yayi magana inda yayi banin turo shi akayi ya shiga tsakanin Fahad da Kausar ya hana su kwanciyar aure, bayan sunne ya koma jikin Hajiya Lailah, dakyar aka samu ya fita daga jikin ta ta dawo hayyacinta bayan tayi attishawa sau uku, had’i dayin kallamatus shahada, shi kuma aljanin ya koma jikin Boka Jimrau bayan yayiwa Malaman bayanin idan ya koma jikin Boka Jimrau bazai tab’a fita har abada, zai kasance a cikin hauka har ranar mutuwarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button