GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da ta dawo hayyacinta sosai sannan ta fara bin ko’ina na parlor da kallo cikin rashin fahimta, ajiyar zuciya d’aya daga cikin malaman ya sauke had’i da cewa ” Alhamdulillah ta dawo hayyacinta yanzu tana cikin hankali da nutsuwarta, a hankali Sanata Sambo ya kalli Ummi yace ” maimaita abinda kikace d’azo, cikin kuka Ummi bayanin komai a gaban Hajiya Rabi da mijinta da sauran jama’ar dake wajen, kuka Hajiya Rabi ta fasa had’i da mik’ewa tsaye tace ” ni zakiyiwa sharri Ummi, me nayi miki a raywarki ta duniya da kike nemana da wannan mugun sharrin? tsakani na dake Allah ya isa bazan tab’a yafe miki ba, ta k’arasa maganar tana matse-matsen hawayen munafurci.

Haqaye na zubowa Hajiya Lailah ta fara magana batare data kalli inda Hajiya Rabi take ba ” a’a Rabi lokaci yayi daya kamata mu fara girbar abinda muka shuka, lokaci yayi daya kamata mu san me mukeyi mu dawo cikin hayaci da hankalin mu,, muna yara da mazajen auren da sune sanadiyyar jefamu cikin hakala, karki k’aryata Ummi domin duk abinda ta fad’a gaskiya ne, babu k’arya ko sharri aciki sai ma wasu abubuwan data rage wanda ita bata sani ba, amma ke kin san da hakan kuma nima na sani ta k’arasa maganar tana kallan Hajiya Rabi tana zubar da hawaye, tsayawa cak Hajiya Rabi tayi ta rasa abinda keyi mata dad’i a duniya.

Hajiya taci gaba ” duk abinda kikaga Ubangiji yayi to akwai dalili dan Allah baya tab’a yin abu babu dalili, haka duk wanda kikaga yana aikata laifi irin namu asirinsa ya tuno ya kunya a idon duniya ya tuzarta d’aya, Allah yayi hakan ne dan yana san sa da rahamarsa, ma’ana dan mutum ya shiryu ya nutsu ya tuba ya koma ga Allah, amma duk wanda kikaga yana aikata laifi amma asirinsa bai tuno ba, bai kuma tuba ya koma ga Allah ba wannan Allah ya barshi, ya kuma rufa mana asiri ne har sai izuwa ranar sakamako sannan zai girbi abinda ya shuka, ya kunya a ranar lahira, wanda mu bazaso hakan ba, dan gwamma kunyar duniya sau 1000 akan ta lahira, duk wannan abu daya faru kece sila, kinga gaba kika k’ara ganin wani zai tunawa wani asiri dan yana aikata mummunan aiki kya hana shi, saboda tsakanin sa da mahaliccinsa ya kuma fiki sani amma ya rufa masa asiri, saboda duk wanda zai aikata laifi b’oya yake a inda yasan babu mai ganinsa saboda shida kansa yasan ba abu mai kyau zai aikata ba, mazinata da ‘yan lesbian da sauran manyan laifuka sai sun shiga d’aki sun rufe suke aitawa, wasu sai cikin dare ma, haka Annabi yace ” idan kaga wani bawa yana aikata aiki irin na ‘yan wuta (sab’o) karka muzantashi (zagi) ko kayi saurin yanke masa hukunci dan kai ma Allah yana iya jarrabarka da irin tashi jarabawar dan jarawace.

Hajiya Lailah ta kwashe duk labarin komai ta bayyana tunda farko har k’arshe da duk irin aiyukan da suke aikatawa ta k’arashe maganar tana kuka, jikin Hajiya Rabi yayi mugun yin sanyi dan haka ta taka izuwa gaban Hajiya Lailah ta durk’usa cikin kuka tace ” gaskiya ne Kawata nayi nadama nima, ta juya ta kalli sauran jama’ar dake wajen tace ” duk abinda Ummi da Lailah suka fad’a gaskiya ne, amma Lailah bata neman maza mata kawai take nema nike had’a maza da mata.

Da k’arfi Alhaji ya runtse idansa yana jin zuciyar sa kamar zata fashe, yayinda Sanata Sambo yake jin kamar ya mutu saboda takaici, cikin takaici da nadama Sanata Sambo yace ” idan kuma kuna da laifi, amma muna da laifi dan babu manyan masu laifi kamar ni da kai Alhaji da kuma sauran mutane masu irin halin mu, da farko duk namijin daya auri mace yasan yanayinta wajen jima’i shin mai hak’uri ce ko akasin haka, ni dai duk mun san yanayin matan mu amma mukayi watsi da buk’atar su, muka fita waje suna holewar mu da sa’anin ‘ya’yan mu, abinda muka aikata a rayuwar mu ne muka fara tsintarsa tun yanzu, ni ‘ya guda d’aya tak mace a duniya amma ta zama KARUWA saboda abinda nake aikatawa da ‘ya ‘yan wasu, kai kuma matarka ta sunnah wasu mazan ke amfani da ita saboda kai ma aikata hakan da matan wasu, domin suma matan da mukayi amfani dasu sun kasance ‘ya’yan wasu, matan wasu sannan k’ananan wasu, na d’auka kud’i, abinci, da sauran kayan more rayuwa sune farin cikin iyali idan ka basu shikenan basu da wata sauran buk’ata a duniya, ashe ba haka bane, babban abinda zaka basu shine, ilimin addini su san waye Allah, su san musulci da dokokinsa, ka basu ingantacciyar tarbiyya ka kula dasu da lamuran su, Alhaji munyi kuskure a rayuwar mu ta duniya, mun tafka babban kuskuren da har mu koma ga mahaliccin mu yana bibiyarmu sai dai muyi ta istagfari ya k’arashe maganar yana matsanancin kuka.

Alhaji yasa magana yayi illa hawaye kawai dake zubo masa, Liman ne yayi gyaran murya yace” gaskiyar maganarka Sanata Sambo saboda mafi yawan matan da suke neman maza da aure su ko suke lesbian laifin mazan sune, kad’an daga cikin sune kwad’ayi da san abin duniya yake kai su, idan matan suna da zunubi to kuma mazan kuna dashi saboda kukuke sakin matanku da yaranku kamar dadbobi, ba tare da kunna bincikar aiyukan su ba, yanzu duniya ta lalace domin maza da yawan basa neman mata marasa aure sai masu aure, kuji tsoran Allah, ku tuna komai nisan jefa k’asa zai dawo, duk dad’ewar da zakuyi a duniya dole sai kun mutu kunje kun sameshi, ku dai na watsi da matayenku da ‘ya’yayanku, Allah yace” duk wanda baya kishin iyalinsa bazai shiga aljanna ba, sannan Allah yace ” duk wanda yayi zina da ‘yar wani sai anyi da tasa, idan bai da ‘ya ayi da matarsa, idan bai da mata ayi da k’anwarsa idan bai da k’anwa ayi da mahaifiyarsa.

Cikin kuka Fahad yace ” tabbas haka ne Malam domin alk’awarin Allah baya tashi, ni nasan ba wani abu ne ke bibiyata ba sai alhakin Aisha, yarinyar danayiwa fad’e har hakan yayi sanadiyyar mutuwarta, nasan hakk’in Aisha yayi ta bibiyar rayuwa ta kenan, nasan bazan tab’a zama lafiya a duniya ba, gashi tun a duniya na fara ganin iftila’i dan wannan babbar masifa ce, ace mahaifiyarka, k’anwarka da k’aninka su rink’a neman su kwanta da matarka ta aure, Allah ne ya nunamin ishara tun a duniya, idan ni bare nayi amfani da Aisha to gashi mahaifiya ta, da k’anena suna neman mata ta, kuma babu k’azantar data fi wannan, kamar yadda yace, Allah yace ” duk wani yayi zina da ‘yar wani sai anyi da tasa, ko matarsa, k’anwarsa da mahaifiyarsa, to gashi ni dai na gani da ido na anyi zina da k’anwa ta, anyi da mahaifiya ta, matata dana k’ara 24hrs da anyi da ita, saura ‘yata ta cikina kad’ai ya rage, cikin kuka yace ” dama nasan Allah bazai tab’a yafe min hakkin Aisha kuda na tuba ba, ya k’ara fashewa da matsanancin kuka yana cewa ” Allah na tuba, ya Ubangiji ka yafe min, Allah kai kace kana san mutane masu tuba.

Gaba d’aya wajen kowa ka gani waye yake zubarwa cikin matsanancin bak’in ciki, a hankali Santa Sambo yace ” ba kai kad’ai ne keda laifi ba nima ina da laifi domin nayi zina da ‘ya’yan wasu, shiyasa nima akayi da tawa ‘yar da mata ta, Alhaji ya kasa cewa komai sai hawaye kawai dayake zubarwa saboda bak’in ciki da takaicin rayuwarsa shi kansa yasan ya tsula tsiya a duniya gashi tun kan aje ko’ina ya fara girbar kayansa, bai tab’a nadamar abinda ya aikata ba sai yau.

Liman ya kalli su Hajiya Lailah dake ta kuka yace ” sannan kuma matan dakun san laifin da kuke aikatawa da irin azabar da Allah ya tanadarwa mataye masu irin halinku da kun dai na, kun tuba kun koma ga Allah, sosai malaman nan sukayi musu nasiha mai ratsa jiki, jini da jijiya, ya fad’a musu irin azabar da Allah ya tanadarwa masu laifi irin nasu, daga k’arshe yace ” Allah gafurur rahim ne shi mai yafiya ne a koda yaushe, ku yawaita istigfari da hailala had’i da salatin Annabi, kuyi tuba da zuciya d’aya irin wanda Allah keso, sannan ku nisanci sab’o da masu aikatashi, ya juya wajen su Sanata Sambo yace ” wannan ya isheku izna daku damasu hali irin naku, kuma sai kuyi ta istigfari ku tuba zuwa ga Allah, ku jawo iyalin ku jikinku, ku kula dasu da lamuransu, ya maida kallansa ga Fahad yace ” karka ce Allah bazai tab’a yafe maka ba domin shi mai yawan yafiya da rahama ne, ka tuba irin yadda Allah keso, kaje ka biya diyyar Aisha, sannan ka ruk’i iyayen ta yafiya, sannan kaima ka yawaita istigfari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button