GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin kuka Mama tace ” wacce irin damuwa da bak’in ciki ne wannan da har zaka salwantar da tarbiyyar dana Baja, wacce irin damuwa ce dabazaka zameni a matsayin mahaifiyar ka ka fad’a min ba, wanne irin bak’in ciki ne da bazaka iya samun d’an uwanka kuma amininka ka fad’a masa ba.

Umar ka bani mamaki, kasa na kasa ganin kaina a matsayin cikekkiyar uwa, wacce zata iya amsa sunanta uwa a ko’ina a gaban kowaye, kasa na raina tarbiyyar dana baku, kasa naga gazawata, Umar na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kai na da kuma ‘yan uwanka, haba Umar mai yasa haka? ta fad’a tana matsanancin kuka, gaba d’ayan su kukan suke Abdul ya kalle shi yace ” kaji dad’i kasa mahaifiyar ka, da ‘yan uwanka wallahi Umar inda ba da ido na naganka ba, na kuma ji da kunne ba dako kashe ni za’ayi bazan tab’a yarda ba, idan ko wani ne ya tare ni ya fad’an wallahi sai inda k’arfi na ya k’are, cikin kuka Umar ya mik’e yace ” shikenan tunda ba wanda zai karb’i uzurina, zan fita daga rayuwarku, zan koma can gefe naci gaba da rayuwa bana san na zame muku matsala, amma duk inda zani ku sani zuciyar Umar na tare daku, har abada zaici gaba da amsa sunan d’an ku kuma d’an uwanku, Umar na kune kuma yana k’aunar ku, ya mik’e zai fita wani wawan mari yaji an sauke masa har hud’u.

Mama ta k’ara d’aga hannu zata sake marinsa yayi saurin rik’e hannunta yace ” Mama karki ji ciwo, idan zaki dage ni madoki ya kamata ki samu, wallahi Mama ki ko kashe ni zakiyi bazan tab’a yi miki musu ba, ya fita ya samu icca ya mik’a mata yace ” mama ki dake ni idan hakan ne zai sama miki sauk’i a zuciyar ki, ki dake ni Mama ya k’arasa maganar yana kuka ya rik’o hannunta, yarda iccan tayi ta rungume shi tana kuma.

” mai yasa kake tunanin barin mu, ashe zaka iya barin mu, zaka iyayin rayuwa cikin farin ciki ba tare damu ba?

“A’a Mama zan yi nesa daku ne zan samawa zuciyar ku sauk’i, amma wallahi nasan bani da sauran jin dad’i idan bana tare daku, “daga yau kome zai faru karka k’ara k’ok’arin barin mu, mu naka ne kai namu ne har abada.

Dariya yayi yana hawaye yace ” in sha Allah Mama, ta baya ya mik’awa Abdul hannu ya kauda kai, kallon Mama Umar yayi yace ” Abdul har yanzu bai huce ba, fushi yake dani, Mama ta kama hannunshi takai shi har gaban Abdul, Umar na zuwa ya rungume Abdul yana kuka yace ” kayi hak’uri d’an uwana, in sha nadai na, sosai Abdul ya rumgume shi yace ” laifinka d’aya ne na barin mu da kake k’ok’arin yi, laifin barin mu har yafi wanda ya aikata.

Gaba d’aya sukayi dariya amma banda Ramlat wacce a lokaci d’aya taji ta tsani Umar bata ko k’aunar ganin shi, tana yi masa kallon wani Monster ne, ya lura da yanayin Ramlat dan haka ya mik’e ya nufi inda take zaune ya durk’usa a gabanta, yace ” please kiyi hak’uri ban kumawa, ko kallansa batayi ba tace ” kama kuma mana ni ina ruwa na.

Wata muguwar fad’uwar fad’uwa gaban Umar yayi dan ba k’aramin so yake yiwa Ramlat ba, dan shi gani yake kamar itace rayuwarsa, akanta yana iyayin komai, ” please kiyi hak’uri ma….. bata bari ya k’arasa ba ta d’aga masa hannu tace” please ka rabu dani, ka fita harka ta da rayuwa ta please, dariya yayi dan shi a tunaninsa b’acin rai ne yasa ta haka yace ” bakomai idan kin huce mayi magana, ” na huce me?

“Aini na gama magana wallahi Allah ko maza sun k’are bazan tab’a auren ka ba Umar, wallahi koda kuwa zan mutu ba aure, wallahi dana yi rayuwa dakai a matsayin miji gwamma na mutu, wata k’ara Umar ya saki ya mik’e ya dafe kansa da duka hannunsa biyu, ya nufi Abdul, wanda shi hakan da Ramlat tayi bak’aramin dad’i yayi masa ba, ransa yake godewa Allah a haukace Umar ya kalli Abdul yace ” kaji me take cewa?

Murmushi Abdul yayi yace ” naji kuma hakan ya faranta min rai, wallahi nima koda zan rasa raina bazan tab’a bari Ramlat ta auri d’an fashi ba, hakan ma zai fiye mana kwanciyar hankali kowa ya fita waje ya nema yayi auren sa kawai.

Zumbur Umar ya mik’e ya saki wata mahaukaciyar dariya yace “………..

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:11] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)

      ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

7

” wallahi k’arya kikeyi kina sons kamar yadda nake san ki, bazaki iya rayuwa ba ni, Ramlat ta bud’e baki zatayi magana, Abdul ya mik’e ya dafa kafad’afar Umar yace ” kayi hak’uri kaje waje ka nemo mata, itama taje waje ta nemo miji, Mama ta kalli Abdul tace ” me yasa, cikin fushi yace ” haba Mama kina jin halinsa fa , wallahi wallahi Allah bazan tab’a yarda Ramlat ta auri Umar ba, koda zan kuwa zan rasa rai na.

Murmushi Ramlat tayi tace ” nagode Yayana ina alfahari dakai nagodewa Allah daya bani kai a matsayin wa, murmushi Mama tayi tace “Allah ya shige mana gaba ya zaba mana mafi alkhairi, gaba dayan su suka ce “Amin.

A gaban Mama Umar ya durk’usa yace ” nayi alk’awari akan duk hukuncin da kuka yanke akaina zan kasance mai yi muku biyayya, kuma inshallahu zanyi bibiyya agareku km zan nesanta kai na da Ramlat zan koma mata ainahin wa, zan kuma kasance mai kare mata mutuncinta a ko ina.

Tun daga ranar Umar ya koma mutun kirki sannan mutum kwarai baya tab’a sakewa ya rabu da Abdul, haka zalika kuma aka daina kawo k’arar sa, kowa ya koma yabansa, idan har ba masallaci ba babu abinda yake fitar dashi daga gidan idan Abdul baya nan, haka kuma a b’angaren Ramlat bai kuma nufarta da wata maganar soyayya kota aure ta ba, ya d’auke ta ne a matsayin k’anwarshi, yanzu babu wata alak’a a tsakanin su, yayinda Abdul da Yasmeen suke cigaba soyayyar su.

Gida ya zamana basu da wata matsala a rayuwar su, a na cikin haka wani saurayi ya fitowa Ramlat, Umar yaje ya samu ya gabatar da buk’atar sa, Umar da kanshi ya kawo shi wajen Mama da Abdul duk sun yaba da saurayin, haka ma a b’angaren Ramlat, cikin k’ank’anin lokaci soyayya mai k’arfi tashiga tsakaninsu, dan haka su Abdul suka nemi yaron ya turo iyayensa, ba’a wani b’ata lokaci ba aka saka rana.

Ranar asabar Ramlat ta tashi da mummunan labarin mutuwar saurayinta sakamakon had’arin mota, sosai mutuwar ta shege ta, duk dangi da ‘yan uwa sun tausaya mata, sosai jikinta yayi mugun sanyi, Umar ne yake lallashinta had’i da kwantar mata da hankali.

Bayan wata d’aya wani abokin Abdul da suke karatu a jami’a yazo gidan yaga Ramlat,din take ya tsinci kansa da fad’awa tarkon sonta, aiko sosai Abdul da Mama suka ji dad’i, haka ma Umar dan a cewarsa idan Ramlat tayi aure shima zaifi yi, sosai suka fad’a soyayya da idris, shima ba’a wani b’ata lokaci ba aka saka rana, hankali kwance suke gudanar da soyayyar su.

K’addara ta rigayi fata, da sassafe aka kira Abdul ake shaida masa mutuwar, Idris sakamakon matsanancin ciwon cikin dayayi fama dashi jiya da dare, sosai hankalin Ramlat yayi masifar tashi, ta razana sosai, saboda a daren jiyan har 10:00 suna tare, wannan karan kowa ya tausaya mata musamman ma Umar.

Tun daga kan Idris Ramlat tace bazata k’arayin soyayya ba, ta hak’ura ta maida hankalinta gaba daya kan karatun ta dan yanzu ta shiga SS 3,ana cikin wannan yanayin ne wani Malamin su ya takura mata da maganar aure, harta ya gabatar da kansa a gaban iyayenta, fafur Ramlat tak’i yarda acewarta kar shima ya mutu a camfa ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button