
Daga k’arshe ya rufe taro da addu’a suka fita, bayan sun fitane Alhaji ya nunfasa yace ” Sanata ina da shawara, da sauri Santa Sambo yace ” wacce irin shawara? “tunda duk mun gane kuranmu mun tuba mai zai hana mu had’a Sheemah da Farouk d’an waje na aure juma’ar nan mai zuwa, da sauri Sanata Sambo yace ” kai Masha Allah amma ka jawo shawara mai kyau, amma kana ganin zai yarda? “mai zai hana ya yarda shi aka san me yake aikatawa, sannan Haidar ma ya fita da matar da yake so a had’a ayi auren lokaci d’aya, cikin sanyin jiki Haidar yace ” ni bani da zab’i, na baku zab’i, murmushi Sanata Sambo yayi yace “zan nema maka auren k’anwar Kausar MEENAL, da sauri Fahad ya d’auko yana kallan Kausar dan yaga reaction d’in da zatayi, aiko a firgice ta d’ago kai tana kallan Sanata Sambo a hankali ta mayar da kallan ga Fahad wanda shima ita yake kallo, “Alhamdulillah Alhaji yace daga nan aka sallami kowa.
Da sauri Kausar tabar wajen tana shiga part d’inta ta wuce bedroom ta fad’a kan had’i sakin kuka tana cewa ” wallahi bazan tab’a bari Meenal ta shigo wannan baud’ad’an gidan ba, ni dai da Allah yasa K’ADDARA TAH ce hakan to na karb’e ta, tun da ta shigo shima ya shigo ya zauna a kusa da ita batare data sani ba, jin abinda Kausar tace yasashi sake fashewa da matsanancin kuka, kukan shi data jine a kusa da ita ne yasata d’agowa, ganin yadda yake kuka kamar k’aramin yasa zuciyarta karaya, cikin kuka Fahad yace ” nasani Kausar, damma Allah yasa ke mai hak’uri ce shiyasa, amma ki sani ina sanki ina miki mugun son da ba kowanne namiji ne yake yiwa mace irinsa ba, tun ranar dana fara d’ora idona akanki Allah ya jarrabeni da muguwar k’aunarki, da sauri Kausar ta tsaya kukanta cak had’i kallansa a razane ganin yadda tayi ne yasashi yacewa ” yes Kausar I LOVE MADLY & DEADLY, I LOVE YOU SO MUCH WITH ALL MY HEART & EVER END.
Koda ke zaki iya rabuwa dani saboda wannan dalilin ki sani ni komai za’ayi, koda bakin bindiga bazan tab’a iya rabuwa dake ba, a hankali ya zame yayi kneel down yana kuka yace ” please Kausar karkice zaki rabu dani idan kika rabu dani mutuwa bazan iya ci gaba da rayuwa, wallahi ko yanzu abin yayi min yawa ni kunyarki ma nakeji akan abubuwan nan, gaba d’aya jikin Kausar yayi mugun sanyi, tausayin mijinta ya kamata, tasan yanzu ne zata nuna masa ita mace ta gari ce, yanzu ya kamata su raba bak’in cikin sa tare, a wannan lokacin ne ya kamata ta jawo shi jikinta ta kula da mijinta ta rarrashe ni ta bashi kulawa, tasan yanzu idan ta nuna masa damuwarta abin zayyi masa yawa ya kamata ya samu sauk’i da sassauci daga gurinta, a hankali ta rungume shi tana kuka itama, cikin kuka tace ” I love you too, i love you so much, goge hawayenta tayi sannan ta shiga rarrashinsa tana baashi hak’uri, tana nuna masa wannan jarabawa ce yayi k’ok’arin cin tasa jarabawar, sa da taga hankalinsa ya kwanta sannan ta mik’e tace ” bari naje nayi mana girki, jawo ta jikinsa ya kuma yace “a ‘a nafisan najiki a jiki na, cikin shagwab’a tace ” ni dai bana san na barka da yunwa karka ulcer ta kamamin kai, murmushi yayi yace ” idan ina tare dake yunwarma bazata zo ba, zata kuma yin magana yayi saurin had’e bakin su.
Washe gari Fahad da Kausar suka je gidan su Aisha, dakyar iyayenta suka yafe masa sannan yayi musu alkhairi mai yawa bayan ya biya diyyarta ya had’a musu da 5 million, cikin farin ciki suka dawo gida dan ji yayi kamar an sauke masa dala da gwauran dutse daga kansa, daga nan direct gidan su Kausar suka wuce, suka yini anan iyayen ta suke sanar mata su Sanata Sambo sunzo neman auren Meenal murmushi had’i dayi musu addu’ar sanya alkhairi, daga nan suka wuce gidan Ni’ima wacce take d’auke da cikinta cikin murna suka tari juna, basu baro gidan ba sai 10:10pm.
Ranar juma’a aka d’aura auren Sheemah da Farouk Meenal da Haidar, amare suka tare a gidajensu, yayinda Fahad ya giniwa iyayen Kausar makeken gida ginin zamani, Haidar kuma ya bawa Malam jari mai yawa had’i sabuwar mota, Sanata Sambo yakai iyayen su Kausar Hajji da Umara.
BAYAN SHEKARA BIYU
Tun daga wannan rana su Hajiya Lailah suka shiryu suka daina duk wasu mugayen aiyukan da suke yi, suka tuba tsakanin su da Allah suka shiga yin azumi da istigfari suna aiyukan alkhairi a duniya domin neman yafiyar mahaliccinsu, haka ma Alhaji da Sanata Sambo sun daina komai sun nutse sun maida hankulansu kan iyalansu kun koma ga Allah sosai basu da wani aiki taimakawa al’umma da dukiyar su suna istigfari, sosai tsoran Allah ya shiga zuciyoyinsu, haka ma Sheemah da Haidar.
Allah ya bawa Kausar haihuwar yaronta d’aya sai da tana d’auke da wani tsohon cikin, Ni’ima kuwa tana da yara biyu mace da namiji, yayinda Meenal keda yarinyarta mace mai sunan Kausar, bayan Abdul ya dawo hutu Nigeria da Yasmeen da yaransu daya tashi komawa Holland Fahad da Kausar suka bisu dan acan ta haifi d’iyarta mace.
A hankali Kausar ta kalli Basma da Zarah tace ” to kunji labari na, ajiyar zuciya suka sauke dukansu suka kasa cewa komai saboda duk tsiya Hajiya Lailah mahaifiyar Fahad ce kuma dole suyi masa kara, cikin mutuwar jiki Basma ta kalli Zarah tace ” Bismillah, a hankali Zarah ta kalli Naseer yayi mata alama da eh, gyaran murya tayi had’i da sauke ajiyar zuciya sannan ta fara.
LABARIN ZARAH
MOMYN ZARAH
[29/01, 11:44] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
44
LABARIN ZARAH!!!
cikekken sunana Fatima Muhammad, ana kira da ZARAH ne kasancewar sunan mahaifiyata aka mayarmin, mu ‘yan asalin garin Daura, amma ni haifaffiyar garin kano ce, mahaifina Alhaji Muhammad Daura cikekken mutum ne kamili mai ingantacciyar nutsuwa da kamala dattijo ne mai nagarta, wanda asali kasuwanci da neman nakai ne yasa ya baro tushensa, danginsa da iyayensa ya shigo garin kano, a lokacin yana d’an matashin sauri dan bazai wuce shekaru sha takwas ba, dan a lokacin yana ji k’arfi na samartaka da k’uruciya ya shigo garin kano, cikin ikon Allah yasa ya shigo garin kano da k’afar dama dan Allah ya had’ashi da wani attajirin mai kud’i d’an kasuwa Alhaji Abdullahi, d’an kasuwa ne shahararre a zamanin sa, mahaifina ya fara zama yaron gidan Alhaji Abdullahi kamar Almajiri, yana yi musu aikace-aikace gami da aike, a hankali Mahaifina ya fara shiga ran mutanan gidan yana k’ara samun kusanci dasu kasancewarsa mutum mai gaskiya da amana.
Dan duk aiken da zakayiwa mahaifina ko aikin da zaka sakashi zayyi maka shine bisa gaskiya da amana, hakan yasa lokaci d’aya ya samu shiga sosai a gidan da zuciyar Alhaji Abdullahi, ya wuce duk sauran ma’aikatan gidan, Alhaji Abdullahi ya kasance mutum ne nagari kamili mai yawan kyauta gami da adalci gashi kwata-kwata bashi da mugunta balle bak’in ciki hakan yasa Allah yake k’ara bashi nasara akan dukkan harkok’insa, Alhaji Abdullahi yana da matar aure d’aya tal tunta ladan noma, suna yara biyar biyu mata uku maza, Fatima wacce itace ‘ya ta biyu a cikin yaransa jininsu ya had’u sosai da mahaifina dukda tana k’aramar yarinya sosai a lokacin da bazata wuce shekaru biyar ba, gaskiya da amanar da mahaifina ya rik’e itace silar d’aukakarshi zuwa babban matsayi a rayuwa, nagartarsa da Alhaji Abdullahi ya gani ne yasa ya mayarda dashi kasuwa wajen kasuwacinsa, lokaci d’aya kasuwanci ya k’ara hab’aka yana ci gaba hakan bak’aramin k’ara d’aukaka darajar mahaifina yayi a wajen Alhaji Abdullahi ba har zuwa wajen abokansa da jama’ar gari dan duk inda Alhaji Abdullahi ya zauna bashi da wata magana sai ta gaskiya da amaar yaronsa Muhammad, sosai Alhaji Abdullahi ya aminta da mahaifina harta kai daya d’orashi akan harkokin kasuwancin sa sosai saboda babu kyashi a zuciyar Alhaji Abdullahi ko takurawa, sosai ya d’agawa mahaifina k’afa ta yadda idan aka fita saro kaya shima zai samu nashi.