
Bayan kamar shekaru bakwai kasuwanci ya hab’aka sosai dan yanzu idan aka saro kaya zama akeyi ayi lissafi a raba ribar duk yawanta gida uku anan take Alhaji Abdullahi zai d’auki kaso biyu cikin uku ya bawa mahaifina kaso d’ayan, kafin wani lokaci mahaifina ya fara amsa sunansa shima da kansa ya soma shahara, bai tsaya wasa da almubazaranci ba ya soma tanadarwa kansa kadarori da k’ara fad’ad’a kasuwancimsa, duk wata harkar kasuwanci data samu koda badaga b’angaren Alhaji Abdullahi bane sai mahaifina ya sanar dashi yayi masa tayinta, saboda mahaifina mai sa’a ne, idan kuma akayi harkar sai Allah yasa a dace a samu riba mai tsoka, hakan ya kuma k’arawa Alhaji Abdullahi so da k’aunar mahaifina a zuciyar sa, babu wanda Alhaji Abdullahi ya yarda dash gida da waj sama da mahaifina.
Alhaji Abdullahi da kansa ya fara sh’awar mahaifina ya zauna kusa dashi har abada, dan haka da kansa yayiwa mahaifina maganar ya kamata ya samu gida ya siya ya dawo da iyayensa da k’annansa kusa dashi suma ya bud’a musu su samu na kansu dan nan gaba da zarar an k’ara wasu shekaru nauyin zayyi mishi yawa, kuma shim ya kamata ya fara k’ok’arin mallakar mallakar gidan zama nashi na kansa, ba musu mahaifina ya amince,kasancewar akwai kud’i a kasa yasa batare da b’ata wani lokaci ba aka fara neman fili anan kusa da Alhaji Abdullahi, cikin sa’a a kasamu wani makekken fili gari guda zan za’ayi iyayin primary school, take aka siyi filin aka fara gina matafaren estate, dan so yake yayi family hause babba sosai.
Yayinda daga b’angaren d’aya sabo da shak’uwa ya fara kid’ewa yana komawa soyayya mai k’arfi tsakanin mahaifina da kuma Fatima ‘yar Alhaji Abdullahi, ana cikin haka Allah ya k’ara bawa matar Alhaji Abdullahi k’aruwar haihuwar d’iya mace aka saka mata suna ZAINAB, yayinda tuni an fara gina katafaren filin mahaifina harma an kusa gamawa dan sosai ake yin ginin ba wani b’ata lokaci, b’angaren iyayensa aka fara gamawa dan haka yaje har Daura ya sanar dasu cewa nan da sati d’aya zasu koma kano da zama gaba , kin amincewa sukayi da farko, sai dakyar Abban mu ya shawo kansu suka amince, sati na zagayowa shi da kanshi yazo ya z’auke, sunyi murna da farin ciki sosai ganin makeken gidan ga kyau da had’uwa.
Bayan iyayensa sun dawo ba’a jima ba aka gama ginin gidan kaf kusan part 16 ne a gidan banda filin ball da filin wasa dana motsa jiki, ganin an gama gidan yasa yiwa Alhaji Abdullahi maganar Fatima wanda dama shi tuni yasan da maganar ba tare da wani b’ata lokaci ba akayi biki aka kai mahaifiyata gidan ta.
Duk wani burin duniya mahaifina ya d’auka ya d’ora shi akan matarsa Fatima bashi da wani burin dayafi ya faranta mata ranta duk wani da take so matuk’ar baifi k’arfinsa ba yana yi mata shi, sosai yake bata kulawa, shekara biyu da auren su amma ko b’ari Mamana bata tab’a abin ya dame su sosai amma Abba na ya danne tashi damuwar yana rarrashin Mama na, sunje asibitoci da dama amma duk inda sukaje maganar d’aya ce lafiya lau Allah ne dai bai kawo lokaci ba, ganin halin da Mama na ke ciki yasa Abba na rok’ar sirikinsa Alhaji Abdullahi akan a basu Zainab , ba musu Alhaji Abdullahi ya amince dan babu abinda Abba na zai tambaya a hannunsa ya iya hana shi matuk’ar yana dashi, Zainab nada 2yrs ta koma hannun yayarta mahaifiyata, tun daga ranar Mamana bata k’ara bak’in ciki ko damuwa akan rashin haihuwa ba, dan ta d’auki Zainab k’anwarta kamar ‘yarta ta cikinta.
Ana cikin haka Fatima da kakata mahaifiyar Mamana da Alhaji Abdullahi suka dame Abba na akan dole sai ya k’ara aure dan kar ganin Fatima ‘yar su ce yasa shi kuma ya cuci kansa, amma fir yak’i ganin haka yasa Fatima fara yi masa akan dole sai ya k’ara aure amma fafur yak’i dole suka hak’ura suka kyale shi.
BAYAN SHEKARU 14
Duk wanna tsayin shekarun Allah bai bawa Mama na haihuwa ba kai ko b’ari bata tab’a yi ba, hakan yasa Alhaji Abdullahi da Kakata suka matsawa mahaifiya akan dole fa wannan lokacin yayi aure ko yak’i ko yasa, dole tasa Abba nah ya yarda badan yaso ba dan shima iyayensa sun matsa masa akan dole sai yayi auren, ba’a san ranshi ba ya fara k’ok’arin neman aure a lokacin Zainab nada shekaru 16,kasancewarshi mai hannu da shuni yasa bai d’auki lokaci yana neman aure ba ya samu, duk da nan cikin kano ya auri yarinyar mai suna Zuwairat, Zuwairat ba budurwa bace bazarawa ce dan ta tab’a aure.
Zuwairat mace ce mai tarin munayen halaye, dan gaba d’aya ‘yan gidan su anyi musu tambarin rashin tarbiyya had’i tsaface-tsaface (asiri), auren ta hud’u duk inda taje mugayen halayenta kesawa a sake ta, amma akayiwa Abba na rufa-rufa akan aurenta d’aya mijinta mutuwa yayi, tun bayan auren Abba nah da Zuwairat komai ya lalace ya tab’arb’are,wacce tana shigowa ta canja komai, ta mallake Abba nah, ta canja masa halayensa da asiri yamana baya ji baya gani a kanta, ita kad’ai kawai yake sauraro, kowa yasan a al’adalce komai yana hannun uwar gida amma ina banda a gidan Abba dan komai yana hannun Zuwairat shi kanshi bai isa yayi wani abu ba sai da saninta ba, tuni ta raba shi da iyayensa da danginsa, ko d’akin Mama na bashi da ikon shiga saboda bai isa ba, matuk’ar ya sake ya shiga kuwa ya shiga uka dan ranar mak’iyinsa ma sai ya tausaya masa, duk kyawawan halaye irin na Abba na sai da aka wayi gari babu ko d’aya, ya zama marar adalci a tsakanin matansa, dan gaba d’aya hankalin sa ya karkata akan Zuwairat, duk wani abu na nashi na hannunta cikin kuwa harda kadarorinta, idan kana so kaga rashin mutunci to ka tab’a masa Zuwairat yanzu zai rufe ido yayi ta zazzaga tujara, hakan da Alhaji Abdullahi ya gani ne yasa shi mamaki, ya tabbatar da ba haka Zuwairat ta barshi ba, duk irin nagarta mahaifina Allah ya jarrabeshi da hatsabibiyar mace mara imani da tausayi.
Kasancewar Fatima baya da d’a bata jika sai Zainab yasa ta d’auki da gatan duniya ta d’orawa Zainab duk wani abu data gani burinta ta sai mata musamman yanzu data zama budurwa take da 16yrs, sosai Fatima take mugun son Zainab take nuna mata gata, dan duk abinda zakayiwa Fatima zata jure amma banda ka tab’a mata Zainab yanzu zakaga gishinta, duk wannan son da takeyiwa mata bai hana ta bata cikekkiyar tarbiyya ba.
BAYAN SHEKARA BIYU
Haka rayuwa tayi ta tafiya tsakanin Mamana da kishiyarta babu wani sausauci sai ma k’aruwa da ake samu dan kusan kullum sai Zuwairat da Abba na sun fito mata da sabon salan wulak’anci hak’uri kawai Mama na keyi, duk da wannan halin datake ciki bata tab’a zuwa takai k’ararsa wajen iyayenta ba, haka suma iayen dayake dattawan da ne akwai kara babu wanda ya tab’a yin magana, sai dai kullum suyi ta bawa Mama na hak’uri suna cewa ta dage da addu’a dan Allah ya jarrabi mijinta da masifa, Zainab ta zama cikekkiyar budurwa ‘yar shekara 18, tun shekarar data wuce ta gama secondary school, manema tako’ina sai fito mata suke amma bak’i kulasu, ana haka Allah ya had’a ta da MANNIR d’an babban aminin Abbanta Alhaji Abdullahi, suma manyan masu kud’i ne dan Abban su Mannir yayi president a Nigeria, ana kiran Family su da EL-MUSTAPHA FAMILY dan family babban family ne, Mannir su biyar ne a wajen iyayensu shine babba sai k’annensa mata sannan k’anin NASEER wanda a lokacin yake JSS 1,kasancewar Alhaji Abdullahi kakana da El-Mustapha akwai amintaka mai k’arfi yasa ba’a wani b’ata lokaci ba akayi bikin MANNIR & ZAINAB k’anwar mahaifiya ta.