
El-mustapha family gaba d’ayansu manyan ‘yan boko wayayyo ne,, masu ji da kud’i da aji, ga kyau kamar su sukayi kansu, akwai baiwar da Allah yayi ta duk d’an da aka haifa a family su yana da CINDO, gaba d’aya familyn babba da yaro babu Wanda bashi da cindo matuk’ar kai jinin su ne, koyaya kuka had’a jini to kana da wannan cindon, Mannir mijin Aunty Zainab ba k’aramin kyakykyawan gaske bane, amma duk kyansa Naseer ya gishi dan Naseer kamar su d’aya sak da salman khan sanda yana matashin sauri ba yanzu daya tsufa ba, ana auren Aunty Zainab ta samu ciki, murna a wajen Mama na da Familyn El-mustapha ba’a magana, cikin Aunty Zainab yana da wata biyu, tafiya ta kama Zuwairat ba k’aramin kashedi tayi masa akan karya sake ya kwana da Mama na ba.
Dan duk yadda kake tunanin Zuwairat ta mallake Abba na abin ya wuce nan, cikin ladabi da biyayya ya amsa mata, tana tafiya ya koma part din Mama na dan har a lokacin yana jin santa da tausayin ta a ranshi dan dai babu yadda zayyi da Zuwairat ne, cikin ikon Allah Mama na ta samu ciki na, Zuwairat bata dad’e da dawowa ba ciki na ya bayya a lokacin cikin Aunty Zainab yana da wata uku na mama kuka wata d’aya, duk da an gama mallake Abba hakan bai hana shi nuna murna da farin cikinsa a fili ba, dan kamar zayyi hauka, fad’ar halin da Zuwairat ta shiga b’ata lokaci ne take hankalinta yayi mummunan tashi ta shiga damuwa, ta kuma k’ara zage dantse da d’ammarar asiri ta dage ta ko’ina bankawa Abba asiri take baji ba gani, dan taso a zubar da cikin amma duk bokan data jewa da wannan maganar sai yayi ihuuuu sannan yayi mata kashedin matuk’ar tana san ranta tabar maganar zubar cikin, ganin gaba d’aya komai ya k’ara jagulewa ne yasa iyyen Abba na da Mama na tashi ttsaye da addu’a bani ba gani dare da rana, kullum aciki neman taimakon Allah suke suna bayar da sadaka.
Sannu bata hana zuwa, yau Aunty Zainab ta tashi matsananciyar nak’uda ana kaita asibiti bata fi 1hr ba ta haifi d’iyarta mace, wacce akayi niyyar sawa sunan Mama na amma ta hana tace ” a sunan kaka ta tawajen uba HAFSAT ana kiranta da IKRAM, bayan wata d’aya Mama ta tashi da matsananciyar nak’uda itama takai wajen kwana biyar tana nak’udar a asubiti, amma haihuwa shiru hakan yasa aka yanke shawarar yi mata CS bayan ta gama shan bak’ar wuya ta fita a haiyacinta ko mutane bata iya ganewa, ana ahirin shiga da ita theater room ta haifeni, tunda ta haifeni cewa ya k’ara tsananta sosai, cikin haka Abba na ya shigo d’akin dakyar Mama na ta neme shi shafiya yana kuka yace ya yafe mata itama cikin kuka tace ta yafe masa, Mama tana jikin Abba ta mutu bakinta yana furta kallamar shahada.
Fad’ar tashin hankalin da zuri’ar mu tashi ma b’ata lokaci ne musamman Zainab da Abba nah, dan Zainab hauka ta rink’ayi tuburan tana sambatu kamar mahukaciya dan sai rufeta akayi a d’aki dan sosai take mahaukacin ihuuuu, Abba na kuwa tun da akayi mutuwar ya rufe kanshi a d’aki yana aikin rusgar kuka dare da rana ba ji ba gani, tun da aka haifeni Aunty Zainab ke rungume dani ta hana kowa d’aukata, bayan sati d’aya da rasuwar Mama aka had’a Family meeting har lokacin Abba yana d’aki yak’i fitowa, sai dakyar kakana Alhaji Abdullahi ya matsa masa ya fito, duk ya rame ya k’ek’ashe ya fita kamanninsa.
Aunty Zainab na rungume dani tana aikin rusgar kuka, Kakana Alhaji Abdulahi wanda muke kira da Alhajin sama yayi gyaran murya yara magana da nasiha sosai, sannan ya cewa Abba na yayi min hud’uba amma Abba ko tari bayyi ba, Alhjin Sama ne yayi min hud’uba da sunan Mama na FATIMA ana kira na ZARAH, yin duniya Abba yayi magana amma yak’i babu abinda yake sai rusa kuka, Zuwairat na hakince akan kujera hard’e da k’afa tana ta fama girgiza tana yiwa duk jama’ar dake wajen kallan banza ciki kuwa harda kakanni duka hud’u, cikin tak’amar ta gama gamawa da Abba nah, sai da Alhajin Sama ya had’a shi girman Allah yayi magana, maganar ta farko a lokacin itace Zuwairat na sake ki uku.
Hannu ta d’ora aka tana ihuuu da kuka ta durk’usa a gabansa tana bashi hak’uri amma ko kallanta bayyi haka taje gaban kakanni na tana basu hak’uri amma babu wanda ya saurare ta, kaka ta taso k’arb’a ta tarik’e ni amma fafur Zainab ta hana kowa ni, tace zata had’a ni da Ikram ta shayar dani, da wannan uzurin kowa ya yarda, tun daga lokacin rik’o na ya koma hannun Aunty Zainab k’anwar Mama, ta had’ani da Ikram take shayar damu.
Tun rasuwar Mama Abba ya koma so silent ba ruwanshi da kowa, ba ruwanshi da mata kwata-kwata ma shi tsoran su yake ji, tunda rik’o na ya koma hannun Aunty Zainab wacce muke kira da Momy take yi min mugun so fiye da Ikram dan ko kuke mukeyi ni take fara d’aura, kai komai zatayi nice akan gaba, har Allah yasa muka fara girma mukayi wayo sosai, bayan Aunty Zainab ta yaye mu babu yadda Mannir bayyi akan ta raba d’aki damu ba amma taki tace yarda dole ya hak’ura, muna 4yrs aka saka mu a primary school nida Ikram dan komai namu tare ne kamar ‘yan biyu babu wani banbanci a tsakani, dan bak’aramin so Aunty Zainab keyi min ba akaina babu abinda bazata iyayi ba, yayinda shak’uwa mai k’arfi ke shiga tsakanina da NASEER k’anin Dady mijin Aunty Zainab, sosai Naseer ke ji dani dan kusan kullum yana gidan, daga k’arshe ma kwaso kayansa yayi ya dawo gidan mu da zama, yayinda Dady ke ji damu kamar ransa, dan tun daga kan Ikram haihuwar Aunty ta tsaya cak, a haka muka yi ta girma har muka kai JSS 3 a lokacin duk wasu halittu na ‘yan matanci sun fara fito mana, yayinda muke wasa ko wanne iri da Naseer, wata rana Aunty Zainab bata nan ta fita unguwa ta dawo ta iske Naseer yana min wasa da nono, iya tashin hanakali Momy ta shige shi, tunda nake bata tab’a ko harara ta ba amma ranar nasha duka, sannan ta mayarda Naseer gidan su dan a lokacin shi ya girma sosai Naseer bai dad’e da komawa gida ba ya tafi Halland dan k’arasa karatunsa, tun daga lokacin Momy ta sa mana ido sosai ni da Ikram
Lokacin d’aya muka gama secondary school da saukar Alqur’an a laocin duk wata halitta ta mace ta gama bayyana a jikin mu, dan muna da 17yrs mukayi Candy, a lokacin Abba nah yana da yara shida mu uka mata maza hud’u idan aka had’a mu bakwai kenan, wanda dakyar da jibin koshi aka aura masa NA’IMA k’anwar Mama wacce daga ita sai Aunty Zainab.
Bayan mun kammala secondary school da sati d’aya Naseer ya dawo bayan ya gama masters d’in shi, wanda har a lokacin ban san Dady da Momy ba sune suka haifeni ba, amma muna yawan zuwa gidan Abba da Alhajin sama sosai, bayan Naseer ya dawo ya fara nuna min wasu abubuwa wanda na kasa gane masa, daga k’arshe na yameni ya sanar dani yana so, nayi masifar shiga tashin hankali dan ni nasan Naseer ganin Dady ne kuma a iya sani na ba aure a tsakanin mu, hakan yasa na naje na samu Momy a parlor ina yi mata tambayoyi.
“Momy dama akwai tsakanin k’anin mahaika da kai,? abin ya bawa Momy mamaki cikin mamaki tace ” a’a, yawwa Momy kenan ba aure a tsakani na da Uncle Naseer ko? gaban Momy yayi masifar fad’uwa, cikin rawar baki tace ” eh a babu, ya akayi? ” to amma Momy Uncle Naseer yace ” yana so na zai aure ni?
Cikin firgice Zainab ta juyo yayiwa Zarah wani irin kallo, a tsorace tace ” cewa yayi yana sanki? “Eh Momy wai aure na yake san yi, nan da nan gaban Momy ya shiga fad’uwa yana dukan uku-uku dan bazata tab’a manta ranar data kama Naseer yana wasa da nonon Zarah ba…….