
MOMYN ZARAH
[31/01, 00:11] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
45
Cikin ranta ta fara magana ” wato Naseer tanan ya biyo, idan na fahince shi so yake ya lalamin ZARAH, to idan kuma da gaske yafa? ta yiwa kanta da kanta tambayar take taji gabanta yayi muguwar fad’uwa dan tasan matuk’ar Naseer da gaske yake to bata isa ta hana shi auren ba musamman ma idan ita Zarah na sanshi, idan kuma hakan zata kasance ta san dole sai Zarah yasa ba itace ta haife ta ba, idan kuma da abinda tafi tsana a rayuwarta shine Zarah tasan ba ita ce mahaifiyarta ba, tasan kuma dole wata rana zata sani komai daran dad’ewa, kodan ma ta rink’a yiwa mahaifiyarta addu’a, ganin shirun datayi yasa Zarah cewa ” Momy kinyi shiru bakiyi magana ba?
Murmushi yak’e Momy ta k’ak’aro gami da cewa ” idan da aure a tsakanin ku ke da Uncle Naseer zaki iya auren shi? murmushi Zarah tayi had’i da sunkuyar da kanta k’asa, hakan da tayi ya tabbatar wa da Momy cewa eh take nufi, take gumi ya fara karyo mata tako’ina gabanta ya shiga fad’uwa yayinda k’irjinta ke harbawa, cikin k’arfin hali tace ” karki sake ki fashi fuska, karki kula shi ki rabu dashi duk ranar daya kuma yi miki magana kice yayi min da kawai, “to kawai Zarah tace tana mamakin abun.
ZARAH irin matan nan ce da kira hurul in na duniya dan duk yadda mace takai da kyau na jiki dana fuska bazafi Zarah ba, dan kyakykyawa ce ajin farko, fara ce sol doguwa ‘yar duma -duma mai faffad’an k’ugu da hips ga na shano a wadace kasancewar cikinta kamar zai had’e da bayanta a shafe kamar bata cin abinci ya k’ara fito mata da k’irarta ta coka-cola sharp, fuskarta doguwa mai d’auke da tsukekken baki wanda Allah ya jerawa fararen hak’ura masu kyau, sai dogon hancinta had’i da dara’daran idanun ta masu d’aukar hankali, gashin kanta yalwatacce har gadan bayanta mai tsantsin gaske, a ko’ina a cikin fad’uwa duniya sai an kira da mai kyau.
Naseer su dama asalin su ba ‘yan Nigeria bane kwarori (larabawa) ne daga k’asar Malaysia kakansu da kakar su suka zo, to kunga tsayawa fad’ar kyansa ma b’ata lokaci ne, lokuta da dama idan ya fita k’asashen waje mutane idan suka ganshi suna kiransa da SALMAN KHAN dan suna tsananin kama, ga shi da aji dan kwata-kwata bai fiya magana ba shiyasa mutane suke ce masa mai girman kai, dan idan kaga yana magana harda dariya to yana tare da Zarah’n sane amma ko a gidan su baya magana sosai akwai shi tsare gida sab’anin Zarah da take da suturu da shegen san hira sai dai tana da yanga da cikekkiyar nutsuwa, tana da san barkwanci hakan da Naseer ya lura dashi yasa kullum suna tare yana bata labarai masu saka dariya ita kuma taita zuba masa surutunta data sama, tunda Naseer bai tab’a yin budurwa bai ma tsaida mace ba saboda tun Zarah na yarinya ya kwallafa ransa a kanta, shiyasa baya ganin kowacce mace a matsayin mace idan ba Zarah sa ba.
Mata da yawa ‘ya’yan manya sun sha cewa suna shansa amma yana wulak’anta su, Naseer nutsetstse ne kamilin mutum mai cikekkiyar tarbiyya dan bashi da wani mummunan hali sai ma kyawawan halaye da yake dasu.
Kullum Naseer a d’akin Zarah yake raba dare sosai, dan wani lokacin ma sai tayi bacci yake gyara mata kwanciya ya tafi, muguwar shak’uwa ce ke tsananin Naseer da Zarah sun yi mugun sabo dashi, da rana kuwa kullum basa gida suna park, duk Family an san da abinda ke tsakanin Naseer da Zarah, su Zarah na zaune a parlor da Ikram da Naseer harda Momy Dady ya shigo zama yayi a tsakiya yana dariya yace ” Momyn yara ana tsakiyar su, dariya tayi itama tace ” idan ban zauna dasu ba dawa zan zauna?
Dariya yayi yace ” to Maman yara ni ba wannan ba, yanzu na samu sak’o ta email d’ina zanje Paris yin wani cos na wata uku, da sauri Momy ta mik’e had’i da komawa kusa dashi tana cewa ” nadai wannan program d’in daka dad’e kana nema ne ya fito ba? yana murmushi yace ” eh shine, ” kai Alhamdulillah amma nayi farin ciki sai dai kuma zanyi missing d’ina harna 3 months, ido ya zaro had’i da cewa kamar ya? wai kina nufin ba tare zamu tafi ba? ” kai ma fa kasan bazan bika ba gaskiya, rai ya b’ata had’i da cewa “mai yasa? “saboda tarbiyyar yara na, kasan dai yadda rayuwa turai take ko? kafin Dady yayi magana Naseer yayi saurin cewa ” gaskiya Aunty Zainab kina da gaskiya dan duk yadda ka tarbiyyici yaranka da zarar su fara fita k’asashen k’etare sai dai kariyar Allah, jikin Momy yayi mugun sanyi dan babu abinda ta tsana a rayuwarta irin lalacewar tarbiyyar yaranta datayi shekaru tana ginawa, ta d’ora burin basu ingantacciyar tarbiyya irin yadda addinin musulunci ya koyar, ido ta zaro had’i da cewa ” ka ji ko ta fad’a tana kallan Dady, shiko Naseer saboda kar a tafi da Zarahn sa yasa shi fad’ar haka, saboda a halin yanzu babu abinda yafi tsana a rayuwarsa irin abinda zai raba shi da Zarah, ganin ya fara cin nasara akanta yaci gaba “yaran turawa ko Aunty, da sauri ta kalle had’i da girgiza kai , tab’a fuska Naseer yayi yace ” abin kyankyami dan kwata-kwata basu da tarbiyya basu da kunya basa ganin mutuncin iyayen su, yanzu zasu kai iyayensu k’ara, shiyasa mutane da yawa basa fita da yaransa saboda gurn’acewar tarbiyyar su, ajiyar zuciya ta sauke had’i da cewa ” aiko babu inda zamu iyakacin mu airport, dariya sukayi gaba d’ayan su har Dady dan sun san wayo Naseer yayiwa Momy.
Babu yadda Dady bayyi akan Momy ta bishi ba amma fir tak’i binsa, ranar tafiya har Airport suka raka shi agaban su yahau girji sai da jirginsu ya d’aga a gaban idan su sannan suka bar Airport d’in, basu koma gida direct ba sai da Naseer yayi yawo dasu sosai sanna suka koma gida, sai washe gari Dady ya isa tun a airport Dady ya kira su video call rige-rige akayi rink’a yi wajen d’aukar wayar yayinda Ikram ke cewa ita zata fara magana da Dady Zarah ma na cewa ita zata fara, k’arb’ar wayar Momy tayi tana dariya ta d’aga, “hello my dear nayi missing d’inka sosai acikin kwana d’aya kawai hararta yayi gami da cewa “kamar gaske, “da gaske ne mana, “idan da gaske kike meyasa baki biyo ni ba? kawar da maganar tayi ta hanyar cewa “ya hanya? dariya yayi dan ya gane manufarta yace ” ina yara na? Zarah ta fara mik’awa wayar cikin shagwab’a tace ” Dady we miss you so much, dariya yayi had’i da cewa ” I miss you too, “Dady yaushe zaka dawo? Momy dake gefe tace ” daga tafiya jiya har kun fara tambayar yaushe zai dawo? Ikrama ta karb’i wayar tana cewa ” kaji Momy ko Dady cike da shagwab’a tayi maganar, “ku rabu da ita kunji bazan dad’e ba zan dawo, tsalle suka farayi suna murna.
Mik’ewa Momy tayi had’i da karb’ar wayar ta shige bedroom tana magana dashi, Zarah da Ikram na ta kokoyi a parlor da jefe-jefe pillows Naseer ya shigo faskarsa d’auke da murmushi ya kalli su yace ” yaushe zaku girma ne? cikin murna suka rugo da gudu jikinsa hannu yasa ya matse Zarah gam a k’irjinsa yana sauke ajiyar zuciya , a hankali suka zame jikinsu daga nasa suka ce ” Uncle zaka kai mu cin shawarma da ice cream yau? shiru yayi yana tunani dan ya tsokane su, ruk’ansa suka shiga yi akan ya kai su, murmushi yayi yace “kuje ku shirya, tsalle suka fara cike da matsanancin farin ciki suka shige bedroom dan su shirya, kasancewar basa fita babu hijab yasa su zumbula hijab har k’asa amma a cikin gida duk shigar da suke so suke yi dan sunfi zama da k’ananan kaya, sai da suka fad’awa Momyn su sannan suka fita, basu dawo ba sai gaf da magrib, suna dawowa kowacce ta fad’a toilet dan yin alwala, shima Naseer ya wuce masallaci, bai dawo ba sai da akayi sallar ishsha, a dinning table ya iske su shima zama yayi a kujerar dake fuskantar Zarah, suna cikin cin abincin Dady ya kira da number sa ta Paris yace ga number sa ta Paris nan, sai da suka sha hira sosai sannan sukayi sallama.