GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

MOMYN ZARAH
[31/01, 00:11] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

46

Cikin kakkausar murya tace ” what a matuk’ar razane “neme kake a bedroom d’in Zarah, in da in da Nasir ya fara yi yana kame-kame, ido Aunty Zainab ta k’ara zarowa waje kamar zasu fad’o k’asa take idanta suka kad’a sukayi jajir kamar gauta, a zuciye taci kwalar rigarsa cikin rawar murya tace ” Naseer me kayiwa ‘yata? ta fad’a a tsawace, cikin rawar baki yace ” ummmm hmmmm da da da da dama bacci sukayi shine na kai su bedroom d’in su, ganin yadda yake magana cikin rawar murya da tsoro ne yasata k’in gaskata abinda ya fad’a mata, da sauri ta bangaje shi ta wuce d’akin Zarah’n dan gano ta.

Kwance ta iske ta tana ta baccinta hankali kwance babu alamar akwai wani abu ko faruwar wani abu dan kamar Naseer ya sani ya tsaya ya gyara ta sosai sannan ya fita ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske had’i da cewa “Alhamdulillah tana goge gumin dake zubo mata, a parlor ta iske Naseer tsaye inda ta barshi duk a tsoroce Naseer yake kamar kace masa k’et ya zunduma da gudu, kallansa Aunty Zainab tayi ita dai har a lokacin hankalinta yak’i kwanciya dan kwata-kwata bata yarda da Naseer d’in ba, haka kawai taji zuciyar ta na bugawa gabanta naci gaba da fad’uwa, a ranta tace ” dole na sakawa Naseer ido sosai akan Zarah, a fili kuma ga mamakin Naseer yaga ta sakar mishi murmushi tace ” am so sorry little bros, sai ta kansa Naseer yayi had’i da sauke ajiyar zuciya a hankaki ba tare data ji ba yace ” haba Aunty Zainab kina tunanin faruwar wani abu ne a tsakani na da Zarah, ita fa k’anwa tace dan da ita da Ikram duk d’aya na d’auke na rasa meyasa kike tsoro na akanta, cikin dakewa take kallanshi har ya dasa aya batare data ko k’ifta idanta bane tace ” ba haka bane Naseer akan yara na zan iyayin komai saboda ina matuk’ar san yarana.

” Babu abinda na tsana kamar lalacewar tarbiyyar yara na zan iya yin yak’i akan duk abinda zai lalata min tarbiyyar su, Naseer abinda yasa kaga ina taka tsan-tsan akan ka sabonda bana san lalacewar zumuncin dake tsakanin ahalinku da namu ne wanda tun kafin a haifemu akayinsa k’ara matsowa gaf dashi ta kuma yadda suna iya jiyo numfashin juna idanta cikin nasa tace ” kamar yadda kaji nace zan iya yin komai aka su to ina komai zan iya yi ciki kuwa harda kisan kai, da bada rayuwa ta, zan iya tsinke numfashin duk wanda yake neman datse min tarbiyyar yara, gaba d’aya jikin Naseer ya d’auki kerrrrma had’i da rawa dan ya gane hannunka mai sanda tayi masa, bai iya cewa komai ba sai murmushin yak’e dayayi mata kawai ya fita, bayansa tabi da kallo tana ayyana abubuwa da dama a ranta.

Ranar kwata-kwata Naseer bai runtsa ba dan yadda yaga rana haka yaga dare sai juye-juye kawai yake ya kasa komai sai tarin tunaninnika iri-iri dasuka addabi zuciyarsa, Allah Allah kawai yake gari ya waye saboda yadda ya matsu yayiwa Dadyn sa maganar auren shi da Zarah, wajen k’arfe 10:30am ya fito cike da damuwa ya samu duk ‘yan gidan su a dining area, shima zama a d’aya daga cikin kujerun cikin damuwa, Momyn sa ce ta lura da halin da yake cikin dan haka tace “autan Momy da Dady ya akayi ne? na ganka cikin damuwa, murmushi yayi kawai ya kasa cewa komai, a hankali Dady ya d’ago yana murmushi idansa nakan Naseer yace ” kema kin san halinsa rigimamme ne, halin nasa na rigimar zai d’an tab’a.

K’ara tab’a fuska yayi cikin shagwab’a yace ” Allah Mom & Dad ina cikin matsananciyar damuwa seriously, cikin nutsuwa Mom da Dad suka mik’e had’i komawa kusa dashi kansa Momy ta rafa shafawa yayinda Dady ya rik’o hannayen shi cikin nashi yace ” fad’amin damuwarka Auta na, cikin shagwab’a yace “Dady AURE nake so cak daga Dady har Momy suka tsaya daga abinda suke yi murmushi Dady yace ” Alhamdulillah Auta ya girma, ka samo matar? k’eyarsa ya shafa cikin alamun jin kunya yace ” eh, “dat is my boy cewar Momy tana murmushi, Dady yace ” wacece yarinyar hope dai ‘yar mutunci ka samo mana, dariya yayi had’i da cusa hannunsa cikin kwantaccen gashin kansa yace ” Dady ai ‘yar gida za’ayi dan ‘yarku ce ma, dariya sukayi had’i da cewa wace ita?

“ZARAH yace batare da fargabar komai, cak duk suka tsaya saboda sun san halin da ake ciki akan Zarah dan har yanzu batasan suwaye asalin iyayenta ba, idan ko matuk’ar Naseer zai aure ta sai ta asalinta kuma sun san babu abinda surukar tasu Zainab ta tsana sama da hakan, cikin sanyin jiki Momy tace ” ita Auntyn taku ta sani ne?

“No Mum ku zaku sanar da ita, “ita Zarah’n ta sani ne? Dady kuma jiho masa wata tambayar “Momy & Dady tambaya haka da yawa? ” eh dole muyi maka tambayoyi saboda kasan halin da ake ciki akan Zarah da Zainab, kai kasanin kanka ne babu abinda Zainab d’in ta tsana sama da Zarah tasan ba itace mahaifiyarta ta gaskiya ba, kuka sosai Naseer yasaka harda hawayensa yana duddura k’afa,ni dai Allah kawai a bani auren Zarah in ba haka ba na fara karuwanci, dariya sukayi daga d’aya Dady yasa hannu ya mutsini bakinsa, Momy kuma ta rankwashe shi, Dady yace “karka damu Auta matuk’ar Zarah na sanka babu abinda zai hana ka aure ta in sha Allah, sai dai idan Allah bayyi matar bace.

Kiss yayiwa iyayen nasa yana cewa ” yawwa Dady thank you & I love you, tea d’in Momy ta d’auka tana saka masa a baki had’i da shafa kansa, zuciya Naseer fes ya fita bayan ya gama karyawa, shawara sosai Dady da Momy suka inda daga k’arshe suka yanke fara yiwa Zainab da Mannir magana kafin su nufi Abban Zarah kai tsaye saboda suma a basu girman su a matsayinsu na wa’yanda suka rik’e ta, washe gari Dady yayiwa Mannir waya yace kome yake yazo nan da kwanaki biyu karya wuce haka, sosai hankalin Mannir ya tashi dan haka ya kira wayar Zainab yake tambayar ta kota san abinda ya faru ” mik’ewa tayi daga cikin yaran ta koma bedroom cikin nutsuwa tace ” wallahi ban san meya faru ba d’azu dai nima Momy ta kira ni tace idan ka tashi zuwa mu taho tare, cikin sanyi jiki yace ” Allah dai yasa lafiya, “Amin kawai Zainab tace itama cikin sanyin jikin, gawar da maganar yayi ta hanyar cewa ” ina yara na? dariya tayi tare da kwala musu kira, da gudu suka shigo a tare mik’awa Zarah wayar tayi tana cewa ” ga Dady, cikin shagwab’a Ikram ta fara diddira k’ara tana cewa ” Allah Momy kin fi san Zarah a kaina komai ita kike fara yiwa ko ki bawa kafin ni, komai ita, ko kiran sunan mu zakiyi Zarah kike fara kira kafin ni, wani lokacin ma idan zaki kira sunana mantawa kike yi ki kirani da sunanta Zarah, murmushi Zainab tayi had’i da rungumo ta jikinta tace ” Ikram basazi tab’a gane dalili bane, amma kema ina sanki sosai kamar yadda nake santa, Zarah na waya da Dady amma gaba d’aya hankalinta nakan rungumar da Ikram tayiwa Momy da sauri tayiwa Dady sallama had’i da mik’awa Ikram wayar tana tureta daga jikin Momy ita kuma tana shigewa jikinta dariya Zainab tayi danta fahimci kishi Zarah keyi dan haka ta mik’e tana cewa ni karku karya ni, Naseer kuwa tunda akayi abin nan bai kuma zuwa gidan ba duk da yana cikin tsananin damuwa da cutuwa na rashin ganin Zarah’n kwana biyu, suma su Zarah sun gaji da cikiyarsa dayi masa waya dan a rana sai suyi masa sau 10 suna tambayar shi yaushe zai zo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button