
K’arfe 1:20pm na rana Mannir ya dira a Amin Kano international Airport, yana fitowa ya hangi direba na jiransa batare da b’ata wani lokaci ba ya shiga cikin motar suka nufi gida, kasancewar sun san Dady na kan hanya yasa suka gyara gida tsaf had’i da shirya dinning table, suna jin k’arar tsayawar motar da gudu suka fita suna rige-rigen isa gare shi da sauri shima cike farin cikin ganin yaran nasa ya k’araso gare su da sauri ya d’aga Zarah sama yana juyi da ita jin k’arar buga k’afa yasa shi juyawa Ikram ya gani tsaye ta kwab’e fuska tana k’ok’arin yin kuka da sauri ya sauke Zarah ya nufi inda Ikram tana itama d’agata sama yayi yana dariya yace ” haba Ikram meyasa kin fiya rigima da yawa ne, cikin shagwab’a tace “bakune kai da Momy sai kuyi ta nuna man san ka ba, dariya yake yana shiga cikin gidan tsaye ya iske Zainab taci uban kwalliya tana sakar mishi murmushi, da sauri ya k’arasa inda take yana dire Ikram a k’asa, cike da d’okin ganin juna ya rungume a k’irjinsa yana mayar da numfashi ganin yaran su na tsaye yasata janye jikinta daga taja hannunsa zuwa bedroom, sai da yayi wanka yayi sallah sannan suka fito dinning area gaba d’ayan su har yaran suke cin abincin cikin raha.
Bayan sallar magrib bayan yayi sallah suka nufi gidan El-Mustapha, a parlor suka iske Momy zaune tana lazimi, sai da ta k’asa sannan ta mik’e cike da fara ta nufo su, har k’asa suka durk’usa suka gaida ita, sannan ya tambayi Dady da Naseer, ” suna masallaci Momy ta bashi amsa cike da kulawa jin an kira sallar ishsha ne yasa mik’ewa ya fiya zuwa masallaci, bayan idar da sallah tare suka shigo da Dady da Naseer suna raha abin sha’awa kasancewar Dady shi mutum ne mai sauk’in kai da wasa da dariya, direct dinning suka wuce kasancewar acan suka hango Momy da Zainab zaune.
Abincin suke ci hankali kwance, Mannir ya kalli Naseer yace ” kai ka fiye ci wallahi haba ka rink’a ci a hankali mana, kafin Naseer yayi magana Dady yayi saurin cewa ” ah Mannir kafa daina wasa da Naseer karya rainaka dan ya kusa zama sirikinka yayi maganar yana kallan fuskar Zainab, Mannir da bai gane abinda yake nufi ba yace ” sikina kuma Dady? yama nemi sirinsa tun wuri, itako Zainab datasa maganar gabanta ne yayi muguwar fad’uwa a firgice ta d’ago kai tana kallan Dady ganin ita shima yake kallo yasata yin yak’e had’i da sunkuyar da kanta bata k’ara kai komai bakinta ba cukalin kawai take juyawa Dady da gaba d’aya halinsa yana kanta yayi murmushi gami da amsa tambayar Mannir “‘yar ka yake so Zarah zaka bashi?
Ruwan da Mannir ya k’urb’a bai kai da had’iyiwa bane ya fito dan ba hanyar da zai wuce take ya kware ya shiga tari, daga Momy har Dady kallansa kawai suke babu wanda yake k’ala ba, Zainab da hankalinta yakai k’uloluwar tashi kasa motsi tayi, cikin tashin hankali Mannir yace ” what? a razane had’i da cewa wacce Zarah? Murmushi Dady yayi irin nasu na manya yace ” FATIMA MUHAMMAD DAURA hope yanzu ka gane wacce nake nufi?
Kallan Zainab Mannir yayi karaf suka had’a ido ganin yanayinta ne ya ganar dashi manufarta, mayar da kallansa yayi ga Dady yace ” haba Dady yama za’ayi Naseer ya auri Zarah, hakan ma bazai tab’a yiyuwa ba, Naseer zayyi magana Dady yayi saurin dakatar dashi da hannunsa ba tare daya kalli inda Naseer yake ba idansa nakan Mannir yace ” meyasa hakan bazai yiyuba?
“Dady dat is impossible ace Naseer zai auri Zarah, a tsawace Dady yace ” nothing is impossible, gaya min abinda zai hana yiyuwar hakan, shin addini ne ya haramta aure a tsakanin su ko al’ada? bani Hadith ko ayar data zo akan ba aure tsakanin Naseer da Zarah, sannan ka fad’amin dalili guda d’aya wansa Naseer bai cika ba acikin sharudd’an aure, ko ka gayamin rashin nagartarsa dazai hana a bashi aure, ni dai a iya sani na ban haifi mazinaci, d’an shaye-shaye ko d’an gay ba, dan Allah ya tsare ni, gaba d’aya maganar da yakeyi da Zainab yake yi dan yaga lokacin da Mannir ya kalle ta, yana dai fakaicewa ne kawai da Mannir,Dady yaci gaba.
“Yanzu a ganin ku kunyiwa Zarah da mahaifiyarta adalci kenan? da sauri Zainab ta d’ago kai tana kallan Dady dan babu abinda tafi tsana arayuwarta irin tayi musu laifi, da mamaki take kallan Dady batare da tayi magana ba, shima ita yake kallo ido cikin yace ” yes Zainab abinda make nufi kenan, duk kun san Zarah kad’ai mahaifiyarta ta haifa, amma kunk’i sanar da ita gaskiya kodan ta rink’a yiwa mahaifiyarta addu’a, shin tun haihuwar Zarah har kawowa zuwa ta tab’a yiwa mahaifiyarta addu’a ko sau d’aya ne tak arayuwarta, kun san darajar addu’a d’a ga iyayen su musamman mamata, take jikin Zainab yayi mugun sanyi ta fara zubar da hawaye dan bata tab’a tunanin haka a rayuwarta ba, Dady yaci gaba ” har zuwa yaushe zaku sanar da ita gaskiya ko mahaifiyarta zata rink’a samun addu’ar tilon ‘yarta d’aya jal a duniya, shin yaushe ne Zarah zata san cewar ita marainiya ce danta rungumi maraicinta ta tallafawa mahaifiyarta da addu’a, kun san meye amfanin haihuwa a duniya?
“To idan baku sani ba yau ku sani wannan yana daga babban dalilin haihuwa, tunda Fatima ta rasu bata tab’a riskar addu’ar Zarah ba, shin kuna tunanin da zata dawo duniya zata yi farin ciki da hakan? sosai kukan Zainab ya k’ara har ya fara yawa hakan bai hana Dady ci gaba da magana ba ” Zarah macece duk tsiya gidan wani zata idan ma bata auri Naseer ba dole wani zata aura, kuma komai daren dad’ewa wallahi Allah Zarah sai ta san bakune asalin iyayen ta ba, duk ranar data san hakan badaga gare ku zaku fahimci abinda nake nufi, dan matuk’ar wani ne ya sanar da Zarah gaskiya zaku shiga mummunan tashin hankali dan sai tayi muku boye akan rashin adalcin da kukayi mata, tana iya jin ma kun fita a ranta.
Dan haka ina baku shawara akan tun wuri tun kan dare yayi muku ku gaggauta sanar da Zarah gaskiya da kanku koda bazaku bawa Naseer aurenta ba, kuma bawai ina yin maganar akan Naseer bane ina yin maganar ne saboda ku kan ku da kuma gaskiya na dad’e inasan baku shawara akan haka, cikin tsananin kuka Zainab ta mik’e ta nufi gaban Dady ta durk’usa dakyar ta iya sausauta kukan tace ” nagode, nagode sosai Dady da nusar dani abin da ban sani ba, ko na manta, idona ya rufe daga ganin gaskiya, kuma nayi hakan ne saboda bana san Zarah ta shiga damuwa kota san zafin maraici bayan ni mahaifiyarta ta rik’e ni tsaka ni da Allah, murmushi Dady yayi yace ” Zarah ba marainiya bace matuk’ar tana da uwa irinki Zainab, da sauri ta d’ago ta kalli Dady, murmushin sa yaci gaba sayi” eh Zainab kowa yasan irin so da gatan da kikewa Zarah fiye da ‘yar cikin ki, kuma har gobe Zarah bata da uwar data fiki a duk fad’in duniya saboda ke k’anwar mahaifiyarta ce uwa d’aya uba d’aya, kuma shi kanshi mahaifin Zarah kamar d’a yake ga mahaifinki Alhaji Abdullahi, kuma shiya rik’e ki sannan yadda zakiyiwa Ikram baki ya kamata haka zakiyiwa Zarah ma ya kamata saboda kin shayar da ita, cikin kuka tace ” in dai nice mahaifiyar Zarah na bawa NASEER AURANTA.
Nasa ranar auren da kai na nan da wata biyu, da saboda tsananin farin ciki Naseer mik’ewa yayi ya d’auki Zainab cak yana zaga parlor da ita , yak’e Mannir yayi yace ” kai aje min mata karka karya min ita kasani k’ara aure ban shirya ba, harara ta wurga mai, gaba d’aya akayi dariya, hawayen fuskarta Naseer ya shiga goge mata yana rarrashinta, a hankali ta Zainab ta kamo hannun Naseer cikin nata tana kallansa hawaye na zuba tace ” Allah ya sani nafi san Zarah fiye da komai a rayuwa ta bana iya had’a santa da komai, Naseer Allah da mala’iku da Dady, Momy, Mannir suna shaida na baka AMANAR ZARAH har abada har iyakar rayuwarku ta fad’a tana kallan fuskar Naseer da take ta fara zubar da gumi zuciyarsa na bugawa da tsananin k’arfi k’irjinsa yayi masa mugun nauyi, k’ara rik’e hannunsa tayi gam cikin nata ta mayar da gaba hankalin ta kansa tace ” ka karb’i amanar dana baka?