GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Take jikinsa ya d’auki kerrrrrma kamar mazari ko’ina na jikinsa rawa yake, take mak’ogwaronsa yayi masa mugun d’aci, gashi idan kowa na kan sa dan haka cikin rawar baki yace ” a’a b…….. a……. n…. b’…… a, b….. a, gaba halin su yayi mugun tashin duk suka mik’e a firgice suna kallansa, da sauri ta saki hannunsa tana yi masa wani irin kallo a fusace tace “……….

MOMYN ZARAH

[02/02, 07:02] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

47

A fusace tace ” what Naseer me kake nufi? Murmushi yayi wanda ya k’ara bayyanar da kyan fuskarsa hannun nata ya sake rik’owa cikin nashi yana kallanta ido cikin ido yace ” Aunty Zainab kin tab’a ganin ambawa mutum amanar kansa da kansa? bata bashi amsa ba idanta dai na kansa, yaci gaba ” Aunty ki kwantar da hankalinki domin Zarah itace ni, ni ne ita, Zarah rayuwa ta ce, wallahi Allah babu wani abu da nake so a duniya sama da ita, tun a yarinta nake san ta, a lokacin ban san meye so ba ina dai jinta ne kawai a raina, Aunty da so da k’aunar Zarah na girma dashi na ginu a raina , in ba Zarah ba Naseer, matuk’ar ina raye bazan tab’a bari Zarah ta nemi wani abu ta rasa ba, bazan tab’a bari ta shiga halin damuwa ko k’unci ba, bazan tab’a barinta a wani yanayi marar dad’i ba balle harta kai ga ta koka.

“Aunty! Zarah ya kamata kibawa amana ta domin santa nake mata yayi yawa ya wuce tunanin mai tunani, ya wuce hasashe, ya wuce duk inda ake tsammani, Aunty akan Zarah kwata-kwata bana iya controlling kai na, idan na kanta mantawa nakeyi da kowa da komai, na manta ni kai na waye, please ina rok’on ku ku tayani da addu’a Allah ya sausautawa zuciya ta kanta, ya k’arasa maganar hawaye na gangarowa daga idansa, jikin Aunty Zainab yayi mugun yin sanyi, take zuciyarta ta karaya tausayinsa ya kamata, a hankali ta k’ara matsawa kusa dashi tana goge masa hawayen fuskarsa itama hawayen na zubo mata.

“Aunty ni garkuwa ni a gare ta, bazan tab’a bari wani abu ya sameta ba, matuk’ar ina raye, idan ko har ina raye wani abu na bak’in ciki ya same ta wallahi bazan tab’a yafewa kai na ba, ya bud’i baki zayyi magana tayi saurin hana shi, cikin farin ciki take murmushi yayinda hawaye ke zuba daga idanta, yau burinta ya cika ko yau ta mutu tasan Zarah tana hannu na gari wanda zayyi zame mata kariya kuma garkuwa, wanda zai kawar mata da maraicinta ya zame mata uwa da uba, ya bata gatan duniya da matabbacin farin ciki a duniyarta, a hankali tace ” nagode Naseer, nagode sosai, Allah ya barku cikin matsananci dauwamammen farin ciki mara yankewa, Ubangiji ya sawa auren ku albarka, Allah ya tsare ku da tsarewarsa ya kare ku, Ubangiji duk wanda zai zamewa raywarku matsala Allah ya d’ai-d’aita rayuwarsa ya tozarta shi ya wulak’anta.

Murmushin jin dad’i Naseer yayi had’i da cewa ” Amin ya Allah Momy, matsowa kusa dasu Mannir yayi yana dariya yace ” yanzu fa Naseer da Zainab an d’inke dan tunda ta baka auren Zarah’n ta ba yakai a duniya, dariya yayi yace ” to Dady yayi maganar da sigar tsokana, dariya sukayi gaba d’ayan su had’i da cewa ” au har mun zama Momy & Dady tun yanzu? ” ah ba dole na ba, ai ba jira da zafi-zafi kan bugi k’arfe, dariya Dady yayi dake tsaye a gefe tun d’azu yana kallansu cike da tausayin Naseer yace ” ai dole k’auwar nak’i, kuma idan da kara ai dole ace da mijin iya baba, haka dai suka sha hira da barkwanci.

Zainab kwance akan bed ta kasa runtsuw tunda suka bar gidan Mannir take cikin damuwa ta kasa skin ranta yaran ma har sun gane sun fahimci tana cikin damuwa, a hankali Mannir ya zauna kusa da ita yayinda idanunshi ke kanta k’uri baya ko k’iftasu, sai da ya rik’o hannunta cikin nashi sannan Zainab tasan ya shigo, firgigit tayi alamun tsorata, suna had’a ido ya sakar mata murmushi, martanin murmushin ta mayar masa, har a lokacin idanuwansu na sark’afe cikin na juna, “Zainab wai meyake damunki ne tunda muka dawo daga gida kika canja, kika shiga damuwa, idan akan auren Naseer da Zarah ne, ki kwantar da hanklinki matuk’ar baki so babu mayyi miki dole, idan baki san auren ko hanlinki bai kwanta, kawai a hak’ura, kar azo a jawo matsalar da muzuncin dake tsakanin iyayen mu shekara da shekaru ya lalace.

“Duk yadda zamu so Zarah ko muso mata alkhairi a bayanki muke, dan zan iya cewa duk duniya babu wanda ya kai ki san ta, Aunty Zainab batayi magana sai da ta bari ya kai aya sannan cikin sanyin jiki tace ” ko d’aya My dear, ni damuwata ba akan auren Naseer da Zarah bane, ni asalima naji dad’i yayi farin cikin auren nasu, dan ina gani addu’a ta dana dad’e inayi ta k’arb’u dan ina da yak’ini akan Naseer zai rik’e min ita, zai bata duk wani abu da mace ke da buk’atar samu daga wajen mijinta, “to akan me kika damuwa? Mannir ya tambaya.

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan tace ” ta yadda zan fuskanci Zarah na sanar da ita banice mahaifiyarta ba, ba nice na haife ta ita ba ‘ya ta ce ta ciki na ba, ta k’arasa maganar hawaye na zuba, “akan wannan kike damur min kanki, yayi maganar cikin dakewa, kai ta d’aga masa alamar eh, murmushi yayi sannan yace ” na riga da na gama tsara komai, da sauri ta kalle shi tace ” kamar ya? “eh yace, Family meeting zamuyi dan harna gama fad’uwa duk wad’anda suka dace, “su waye suka dacen, dawa-dawa ka gayyata? ” na sanar da mahaifin Zarah, nace yazo da iyayensa, kakanin Zarah’n sannan na sanar da Babanku nace yazo da su Momy kuma na sanar da su Dady da Momy sai Naseer, Zarah, Ikram, ni da ke, “yaushe za’ayi? Zainab ta tambaya, kai tsaye yace ” on 16/jan/2019 kinga jibi kenan, cikin sanyin jiki tace ” Allah ya kai mu, “Amin yace yana jan hancinta.

MEETING DAY

A babban parlor gidan Mannir kowa ya hallara yayinda gaban Zarah keta fad’uwa ta rasa dalili, kowa ya nutsu saboda kowa da manyansa a wajen, El-Mustapha ya kalli Naseer yace ” bud’e mana taro da addu’a, kai ya risina cikin girmamawa ya fara addu’a, sai ya kammala sannan El-Mustapha ya kalli Alhaji Abdullahi yace ” kai ya kamata kayi bayani, cikin sanyin jiki Alhaji Abdullahi ya kalli Zarah wacce gaba d’aya tausayinta ya gama kamashi yace ” Fatima a hankali ta d’ago kai ta kalle shi had’i da cewa ” na’am cikin sanyin jiki, yaci gaba ” wannan gaba d’aya naki ne danke akayi shi, ita dai kallansa kawai take batare data kuma cewa komai ba, ” saboda lokaci yayi daya kamata kesan ke wacece, kisan asalinki da kuma iyayenki da gaskiya domin komai daren da d’ewa wata rana dole sai kin sani, da k’arfi k’irjinta yayi muguwar bugawa cikin rashin fahinta ta kalli Zainab da tunda aka zauna take sharar hawaye, itama ita take kallo, cikin rawar baki Zarah ta bud’e baki zatayi magama amma ta kasa furta koda kalma d’ayace, yaci gaba Zarah, ZAINAB DA MANNIR!!! BA SUNE IYAYENKI NA GASKIYA BA, wata irin saukar aradu Zarah taji a ranta take kunnuwanta suka fara jiyo mata tsawa kamar ana ruwan sama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button