GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali Alhaji Abdullahi ya nuna mata Muhammad Daura yace ” wannan shine mahaifinki, sannan ya nuna mata iyayensa dake gefe yace ” wad’annan sune kakanninki na wajen uba, sunan mahaifiyarta FATIMA shine aka mayar miki dashi bayan rasuwarta, kuma Fatima ‘yata ce ta ciki na Yayar Momynki Zainab ce uwa d’aya uba d’aya itace ta rik’i Zainab tun daga yaye harta aurar da ita, ni da Mama ya nuna mahaifiyarsu Zainab yace ” mune kakaninki na wajen uwa, daga nan kwashe labarin komai tun daga zuwan Abbanta kano har Aurensa da FATIMA ‘yarsa da labarin Zuwairat da komai ya sanar da ita bai b’oye mata komai komai.

A hankali ya mik’a mata photo album k’ato yace ” gaba d’aya hotuman mahaifiyar ki ne aciki, tun tana yaririya, har zuwa girmanta harda wanda tayi da cikinki, tab tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, fad’ar halin bak’in ciki da damuwar da Zarah ta shiga ma b’ata lokaci ne, dan ta shiga mummunan tashin hankali hannunta na rawa ta k’arb’i photo album d’in, amma ta kasa bud’awa, ci gaba yayi da magana da magana “sannan mun bada AURENKI GA NASEER, mik’ewa Zarah tayi rungume da album d’in a k’irjinta, tana shirin fita dan ita bama tasan inda kanta yake ba, kwata-kwata bata cikin nutsuwarta da hayyacin ta.

Idanta babu ko d’igon hawaye saboda tsabar tashin hankali ita rok’on Allah ma take akan ta samu tayi kukan ko ta samu taji dad’in ranta, ganin bata cikin hayyacinta yasa Naseer yunk’urawa zai rik’o ta, da sauri Dadynsa ya rik’e masa hannu batare daya kalle shi ba, hakan yasashi komawa ya zauna dole, a firgice Aunty Zainab ta mik’e cikin matsanancin ta rungume ta a jikinta.

A hankali Zarah ta zame jikinta daga Zainab tana k’ok’arin barin parlor, k’ara rik’o ta Zainab ta yi cikin kuka tace ” please Zarah karki fishi dani na rashin k’in sanar dake gaskiya da wuri a baya baki kai ahekarun dazaki iya d’aukar bak’in cikin maraici ba shiyasa, a fili Zarah ta maimaita MARAICI!!!! sai lokacin taji wani irin kuka yazo mata aiko da k’arfi ta sake shi, wani irin mahaukaci kuma matsanancin kuka ta durk’ushe a wajen tanayi, duk wajen sai da akan tausaya mata harda masuyin kwalla da hawaye, cikin fitinan kuka tace ” yanzu ina 17yrs a duniya mahaifiyata tana da 17yrs da rasuwa amma ko sau d’aya ban tab’a yi mata wani addu’a ko wani abu da zai sanyata cikin farin ciki harya san tana da ‘ya ba, mai yasa baku sanar dani da wuri na k’araci rayuwata wajen yi mata addu’a ba, mai yasa zakuyi mana haka ni da ita ta k’arasa maganar cikin matsanancin kuka.

Cikin kuka Zainab ta k’arasa inda take ” wallahi Zarah banak’i sanar dake dan wani abu bane sai dan san da nake miki, Zarah ina sanki fiye da kowa da komai a rayuwa ta, dan Allah Zarah karki barni, da sauri Zarah ta rungume Zainab tana cewa ” Momy bakiyi min komai ba sai alkhairi, kin min gatan da kowacce take bawa ‘yarta, kuma kin shayar dani ke kikayi rainona, ke kikayi min komai Momy ya za’ayi na barki ko nayi fishi dake matuk’ar ina san ganin dai-dai a rayuwata, duk duniya bani da uwar data fi har yau har gobe, Momy bazan tab’a yin fishi dake ba duk girman laifin da zakiyi min, nasan kina so na Momy ni shaidace, ta fad’a tana k’ara shigewa Zainab d’in sosai ko zataji sanyi a ranta.

Cikin kuka Ikram ta taso itama ta rungume su, duk jama’ar dake wajen babu wanda bai zubar da hawaye ba saboda tsabar jin tausayinsu, cikin kuka Zainab tace ” na k’ara miki wani lafin dan nabada aurenki ga Naseer, murmushin k’arfin hali Zarah wanda yafi kuka ciwo tace ” bakomai Momy, nasiha mai ratsa jiki, jini, jijiya da duk wata gab’a dake jikin mutum El-Mustapha yayi musu, ya kuma k’ara bawa Zarah hak’uri akan ta rungume jarabawarta, ta godewa Allah ma ita tana da mahaifi da kuma dangi da ‘yan uwa masu tsananin k’aunarta, ga kuma uba Zainab da Allah ya bata, akwai wanda ake haihuwarsu ba uwa, ba uba, ba wa, ba k’ani, babu dangin uwa balle na uba, basu da kowa a duniya amma suke rayuwarsu cikin farin ciki da godiyar Allah, haka sukayi ta kawo mata musu da k’issoshi, suka nuna mata shi kanshi wanda akayi duniya da lahirar damunsa haka ya taso ba uwa ba uba cikin maraici, sosai jikinta yayi mugun yin sanyi ta kuma k’ara godewa Allah abisa ni’imomin dayayi mata, ta kuma rungumi K’ADDARAR TAH, had’i da guduwar niyyar yiwa mahaifiyata addu’a ba dare ba rana.

Tun daga wannan ranar Zarah ta shiga yiwa mahaifiyata addu’a sosai, kuma tsoran Allah ya k’ara shigarta, a d’ayan b’angaren kuma wata azababbiyar soyayya ce ta shiga tsakanin Zarah da Naseer, 24hrs suna tare a waya ko zahiri kullum yana gidan Aunty Zainab wajen Zarah, kwata-kwata bashi kowa da kansa sai nata, gaba d’aya rayuwa da lokacinsa ya sadaukar mata, sosai soyayya mai tsananin k’arfi ta shiga tsakanin su, ta yadda d’aya baya iya yin 2hra ba tare da yaji ko yaga d’ayan ba, kowannen su ji yake kamar bazai iya yin rayuwa babu d’ayan ba, ji suke numfashi suma yana fita ne da k’ara ruruwar so da k’aunar junansu.

Naseer da zaune a bedroom d’in su yayinda Ikram ke gefe bacci ya d’auke ta, suna tsaka da hira Zarah ta hango kenkeso (cockroach) ai bata san sanda ta fad’a jikin Naseer tana ihu ba shi kuma sai dariya yake, da ita ya mik’e a jikinsa ya kashe kenkeson yakai toilet, sannan ya dawo da bedroom, a lokacin hankalin Naseer ya dawo jikinsa, tana k’ok’arin sauka daga jikinsa yasa hannu ya k’ara matse ta gam, ya k’ura mata ido itama shi take kallo yanayin kallan da sukeyiwa junane yayi mugun kashe musu jiki had’i da saukar musu da sakala, a hankali Naseer ya tallafo hab’arta da hannusa yakai bakinsa saitin nata, kasa hana shi ta yi sakamakon muguwar da jikinta yayi, a hankali ya had’e bakin su waje d’aya ya shiga aika mata da hot kisses, yayinda hannunsa ke kai breast d’inta, dai-dai lokacin Aunty Zainab ta shigo, cak ta tsaya numfashinta yana k’ok’arin d’aukewa idanunwa take sukayi jajir suka firfito kamar zasu fad’o k’asa.

Da k’arfi tace ” NASEER!!! a zabure duk suka mik’e, cikin matsanancin tsoro suke kallanta, cikin kerrrmar jiki da rawar baki Naseer ya bud’e baki zayyi magana ta daka masa wata gigitacciyar tsawa a fusace had’i da cewa ” get loose 4rm here, da sauri yana kerrrrma ya fice, a hankali ta maida kallanta ga Zarah dake tsaye jikinta nata kerrrrma, takai wajen 5 minutes tsaye kawai tana kallanta, batare data ce mata komai ba, a hankali ta juya zata fita, har ta kai bakin k’ofa ta juyo tace ” karki sake ki bari yayi miki wayo ya karb’e abu mafi girma da daraja a wajen ki da rayuwarki (BUDURCI), ta juya ta k’arasa ficewa, kasancewar Mannir baya nan ya koma Paris tun bayan gama meeting ya koma dan bai gama course d’in da aka tura shi ba, yasa gari na wayewa ta kira Dadyn Naseer tace ” please Dady ina so matso da bikin Zarah da Naseer a mayar dashi nan da days, next Friday, jin yadda muryarta ke rawa yasa shi fuskarta akwai wani abu dan haka ba musu ya amince.

Sosai aka shiga shirye-shiryen biki haik’an, wanda shi Naseer hakan ma dad’i yayi masa, shidayake namiji ne dakewa yayi ya nuna kamar babu abinda ya faruwa, sab’anin Zarah da tunda Zainab ta kama su ta koma wasan b’uya da ita, kwata-kwata ta daina fituwa falo ta koma zaman d’aki, itako Zainab tayi banza da ita, ana saura kwana biyu d’aurin aure Zarah ta tashi da mugun zazzab’i da cewon kai ga yawan amai, kwata-kwata bata jin dad’in jikinta, sosai ta galabaita a cikin yini d’aya tak, Ikram ce tazo ta sanarwa da Zainab cewar Zarah bata da lafiya sosai, a firgice ta mik’e ta nufi bedroom d’in ganin halin da take ciki ne yayi masifar tada hankalin Zainab, da sauri ta koma parlor ta kira Naseer tace idan yana kusa please yazo gida yanzu yakai Zarah hospital, kasancewar basa baya kasa shima hankalin shi yayi masifar tashi yace” wallahi Aunty bana kusa, meke damunta bata jira bashi amsa ba ta mik’e ta zaki key d’in mota da hijab ta sumgumi Zarah tayi hospital, da sauri doctor suka karb’e ta sukayi ciki da ita gwajin farko likita ya gano Zarah nada shiyar ciki na wata hud’u, umarni yayiwa Zainab data biyo shi office, bayan ta zaune ne, cikin murmushi yace ” congratulations your daughter is pregnant, “ban gane ba doctor tace, murmushi yayi had’i da cewa Zarah tana da ciki harna wata hud’u…………..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button