GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

MOMYN ZARAH
[02/02, 07:02] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

48

Dariya Aunty Zainab tayi had’i da cewa ” kai badai ciki ba, duba dai da kyau ka ganin, murmushi yayi had’i da cewa ” ciki ne da ita mana harna wata hud’u, tsaki tayi cikin fishi ta mik’e tana magana ” baka san aikinka ba wallahi, ban san mahaukacin daya baka aiki ba, a baya Doctor ya biyo ta yana mata magana amma ko kallansa bata yi ba, direct wajen Zarah ta wuce, da taimakon nursing suka saka ta a mota ta, tana driving tana mita ita kad’ai harta k’arasa k’ofar wani private hospital.

Da gudu nursing suka fito, cikin girmamawa suka gaida ita had’i da d’aukar Zarah suka wuce ciki da ita, nan ma gwajin farko Doctor ya shaidawa Aunty Zainab tana da shigar ciki na 4 months, nan ma tijara ta zazzagawa Doctor d’in sannan ta d’auki Zarah tayi ficewarta, wasa-wasa dai sai da Aunty Zainab taje hospital har biyar amma duk maganar d’aya ce shine ZARAH TANA DA CIKI, har government hospital taje amma duk haka ake ci mata, sosai jikin Zainab yayi mugun yin sanyi amma har a lokacin bata yarda Zarah nada ciki ba, zaune tayi a cikin mota ta kasa yin komai jikinta sai kerrrrrma, a hankali ta juya ta kalli Zarah, takai wajen 10 minutes bata d’auke idanta daga kanta, tana san gano wani abu amma ta kasa, rasa abinyi tayi, ta jima tana tunani kafin daga k’arshe ta yanke shawarar kiran Family doctor su, ajiyar zuciya ta sauke da k’arfi sannan ta ciro wayarta daga cikin jaka tayi dialing.

Ringing d’aya yayi picking cikin girmamawa, yace ” Hajiya ya gidan? bata samu damar amsa masa ba illa cewa da tayi ” kana ina yanzu? “ina asibiti ya bata amsa cikin kulawa, “ok ina san ganin ka right now, ok bani nan da 30 minutes zan zo in sha Allah, “no badamuwa bari nazo kawai ina kan hanya, cikin mamaki abinda take so da sauri haka yace ” ok sai kin k’araso, batayi magana ba ta kashe wayar had’i da yiwa motarta key, dayake ba tazara sosai in 15 minutes ta k’arasa, waya tayi masa ta sanar dashi ta k’araso, da saurin sa yazo yana murmushi, martanin murmushi ta mayar masa cikin yak’e, ganin yanayin datake ciki bak’aramin bashi mamaki yayi ba, yace ” Hajiya baki da lafiya ne?

” No Zarah ce bata d’an jin dad’i ta fad’a tana kallan cikin motar inda Zarah ke kwance, bin inda ta kalla yayi da kallo shima, da sauri yace ” subhanallah bari nayiwa nursing magana, yana tafiya yana magana a ransa “wanne irin so Zainab takeyiwa yarinyar nan ne haka, daga bata da lafiya duk ta rud’e ta canja gaba d’aya ta fita daga hayyacin ta, yana maganar harya k’arasa inda nursing suke ya shaida musu akwai mara lafiya a waje, tare da Aunty Zainab suka shigo, office d’insa ya kai ta yace ta zauna kafin su gama duba Zarah ba musu ta zauna.

Direct d’akin duba marasa lafiya aka wuce da ita, bayan ya gama yi mata duk abinda ya kamata ya bata taimakon gaggawa ta farfad’o, sai da yayi test yakai 5 tyms amma sakamakon dai d’aya ne, sai da yayi test kala-kala a k’alla shida amma duk dai ciki yake gani.

Yayi masifar mamaki da shiga mummunan tashin hankali dan shi a iya saninsa yasan Zarah bata da aure, jiya ma Naseer ke sanar dashi cewar jibi auran su, a tunanin ta yadda zai sanar da Zainab wannan maganar ya farayi dan yasan akwai babbar matsala, amma yasan ya zama dole ya sanar da ita gaskiya, dan haka cikin sanyin jikiya nufi office d’in, cikin rashin kuzari ya zauna a kujerar zaman sa yana fuskantar ta, a hankali ya kira real name d’inta abinda bai tab’a yi ba dan ta d’au magarsa mahimmnci ” Zainab!, gabanta ne yayi mummunar fad’uwa jin ya kira ainahin sunta, bata iya amsawa ba illa ido data zuba masa a matuk’ar tsorace.

Sai da ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan yaci gaba ” Zainab ko wanne mutum da kika gani a rayuwa yana da k’addararsa da jabarwa dan Allah bazai tab’a barin mutum ba jarabawa abinda nake so dake kiyi k’ok’arin cinye taki jarabawar please, kuma ki fahince k’addara, kar hakan ya zame miki sanadiyyar kamuwa da ciwo, dan duniya tasan irin mugun san da kike wa Za….. hannu ta d’aga masa had’i da cewa ” what is going on? just go to straight to the point, cikin sanyin jiki yace ” Zainab ina so ne ki fara fahimta kafin na sanar dak……. katse shi tayi ta hanyar cewa ” go on Mr Doctor.

Cikin rawar murya yace ” she is pregnant, a zabure Aunty Zainab ta mik’e tana huci tace ” kai ma haka zakace kenan idan su sauran basu san Zarah kai ai kasanta tun kafin tasan kanta, amma kai ma mayar da kanka kamar sauran, murmushi had’i da mik’ewa yace ” zo muje abinda yace kenan ya wuce gaba ta bishi a baya, umarni ya bawa nursing dasu kai Zarah scanning room, a baya suka bi su da Zarah, suna shiga yacewa nursing su fita, bayan sun fita ya kwantar da Zarah, ya fara yi mata scanning ya kalli Zainab yace ” kalli kiga, baby Zainab ta gani yana ta wutsil-wutsil har an kusa gama masa halitta, Doctor yace ” idan test zayyi k’arya scanning bazayyi k’arya yanzu dai kin gani da idanki.

Ya k’arasa maganar yana juyawa gefenta gabansa ne yayi muguwar fad’uwa ganin halin da take ciki, tsaye take cak kamar mutum-mutumi, idanuwanta kan na’urar scanning d’in, ta kasa koda matsa hannunsa da sauri ya mik’e ya k’arasa inda take yana kiran sunanta cikin tashin hankali ” Zainab!!!!, bata ko matsa ba, hannu yakai ya tab’a ta yaga ta tafi luuuuuuu ta fad’i, cikin tashin hankali ya fara kwalawa nursing kira da k’arfi da gudu suka shiga.

Kai tsaye Emergency aka shigar da Aunty Zainab had’i da juna mata Oxygen, Doctors biyar ne akanta suna iya k’ok’arin su amma shiru har wajen 3hrs suna kanta amma babu ko alamar motsi gashi kuma zuciyar ta na bugawa, duk hunhunta yana motsi bare suce kota mutu, sun bata iyakar taimakon su amma babu wani ci gaba, haka suka hak’ura suka fito da ita suka kai ta d’aki had’i da saka mata na’urori kala-kala harda Oxygen d’in.

Itama Zarah an kwantar da ita asibitin kasancewar tana masifar jin jiki, sai bayan komai ya lafa Doctor ya kira El-Mustapha da Naseer ya nasar dasu halin da ake ciki, a rikice Naseer da Momy da Dady suka k’araso asibitin bayan sun sanar da familyn Zainab, kusan lokaci d’aya suka k’araso, a rud’e Naseer yake tambayar Doctor abinda ya faru, cikin in ina Doctor yace ” Zarah ce bata da lafiya shine Hajiya ta fad’i, kamar daga sama Doctor yaji Naseer yace ” meke damun Zarah!?

A tsorace Doctor ya d’ago ya kalli Naseer, yanayin yadda ya d’ago ya bawa kowa mamaki, kame-kame Doctor ya fara yi ya rasa abin cewa, a zafafe Naseer ya nufi shi yana cewa ” baka ji ana maka magana ne? Kayiwa mutane shiru, da sauri el-mustapha ya k’arasa wajen had’i da dakatar da Naseer ya kalli Doctor yace ” meke damun Zarah? yayi maganar yana kallansa ido cikin ido, ajiyar zuciya Doctor ya sauke dan yasan maganar kallan da Dadyn yake yi masa.

Cikin rawar baki yace ” she is pregnant, “wad’in cewar Naseer da k’arfi, kan Doctor a k’asa yace ” Zarah tana da shigar ciki na wata hud’u.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button