
Sosai ‘yan gidan su suka tausaya mata, an d’auki lokaci sosai kafin Malam ya shawo kan Ramlat dakyar da taimakon Yasmeen, sama-sama take kula shi, saboda gaba d’aya a tsorace take, cikin ikon Allah Malam ya gabatar da iyayen sa, had’i da neman alfarmar ayi auren kafin tayi Candy ta k’arasa a gidansa, babu musu su Abdul suka amince, ba’a saka lokaci mai tsayi ba, aka fara shirye-shiryen biki.
Ana saura sati d’aya biki aka tashi da mutuwar Malam, mutuwar data gigita hankulan jama’a, sosai hankalin su Abdul yayi masifar tashi,fad’ar tashin hankalin da Ramlat ta shiga ma b’ata lokaci ne, dan tayi masifar girgiza da razana, sosai ta firgita, ta zaman wata sukuku kamar marar hankali, ba taci bata sha, lokaci d’aya ta rame sosai, ta maida kanta zaman d’aki, koyaushe rana d’aki tana faman aikin kuka, sosai su Abdul suka tausaya mata, musamman Umar, dashi kusan koyaushe yana tare da ita yana lallashinta, da bata hak’uri had’i da nuna mata yarda da k’addara.
BAYAN WANI LOKACI
Bayan hakula sun d’an lafa komai ya fara zama normal, amma har a lokacin Ramlat tana cikin damuwa dan kallo d’aya zakayi mata kasan hakan, Abdul na d’aki Mama ta shigo ta samu guri ta zauna, daina abinda yakeyi yayi ya maida gaba d’aya hankalinsa kanta, Mama tace ” Abdul shawara ce nake san muyi akan yaran nan, ” cikin ladabi Abdul yace ” to Mama akan me kennan?
Umar dake shigowa ya tsaya cak yana sauraran su,da km abinda zasu tautauna akai Mama ta numfasa kana tace ” kaga yadda Allah ya nuna lamarinsa da ikonsa akan Ramlat ko, duk wanda ya fito da sunan neman aurenta sai rabo ya kashe shi, cikin rashin fahimta Abdul yace ” rabo kuma Mama rabon me?
Murmushi tayi irin Nasu Na manya sannan tace ” zai iyayuwa rabon a tsakanin su yake, duba da yadda duk wanda ya fito sai ya mutu, ina Allah ya riga ya tsara Ramlat matar Umar ce, Allah yayi shine mijinta, kasan wani baya auren matar wani haka kuma wani baya haihuwar d’an wani, dan haka nake ganin karmu matsa dayawa kawai mu barsu suyi aure tare da binsu da fatan alkhari .
Shiru Abdul yayi na wani lokaci yana tunani da saka da warwara akan zance mahaifiyarsa kafin Daga bisani can ya nisa yana sauke naunauyen ajiyar zuciya yace ” gaskiya Mama indai ina raye bazan tab’a bari Umar ya auri Ramlat ba, sai dai idan nima rabon ya kashe ni, idan na mutu sai suyi auren su, Mama ya za’ayi muna ganin kashi da rana mu taka, duk da Umar ya kasance dolen mu ne, amma gaskiya bazan iya bari Ramlat ta auri d’an fashi, da makami mazinaci, d’an maye ba, saboda komai yana iya faruwa,arayuwa duk ita ma Ramlat bata son auren nasu yanzu kuma bbu komai addini haramun auren d’an giya.
Shiru Mama tayi, Sosai cikin mutuwar jiki tace ” Allah ya zab’i abinda yafi alkhairi, ” Amin Mama addu’a ya kamata kiyi mana, “addu’a kam kullum akanta ake Abdullahi, murmushi Umar dake labb’e yayi ya girgiza kanshi kawai kwalla takaici na zubo masa a fili yace ” na cuci kaina, jin Mama na niyyar fitowa yasa shi saurin barin wajen.
Dayake Abdul Medicine yake karanta, cikin ikon Allah aka tura shi Practical a General hospital din dake Gombe, Allah yasa ya fara practical a sa’a tunda yake aiki bai tab’a samun wata matsala ba, har Allah yasa yayi wata biyu.
ranar wata Monday da wuri Abdul ya tashi ya shirya ya nufi hospital, yana zuwa yaga an kawo wata yarinya a matuk’ar galabaice, za’a shiga da ita Emergency, sai jini ke zuba ta k’asanta,yayinda numfashi ma da kyar take fitarwa tsabar tashin hankali datake ciki bata ko iya magana bata iyawa , da sauri Dr ya kira Abdul akan yazo ya taimaka masa , cikin rawar jini ya shiga,dakin aka kwantar da wannan yarinyar.
Abdul na shiga Dr ya d’age gaban yarinyar, ” Innalillaihi wa’inna ilaihirraji’un abinda Abdul ya shiga furtawa kenan yana dauke idanunsa da sauri .
Saboda ganin yadda gaban yarinyar yayi da sauri ya runtse idanushi tare da kansa gefe, sai ji yayi caraf an rik’o masa hannu a d’an tsorace ya bud’e idonsa, yarinyar ya gani rik’e da hannunsa, hawaye na zubo mata,tana dubansa agalabaice bakin da k’asanta jini sai zuba yake, da kyar ta iya bud’e baki tace ” sunana Aisha, ina karatu a Government Girls ina SS1, d’an gidan Sanata Sambo ya ganni yace yana sona, nak’i amince masa ballanantana Na kulashi to shine dan nak’i kula shi, suka yi min fyad’e shi da abokan sa, ni ‘yar talakawa ce iyaye na basu da wani k’arfi dasu daukar min mataki akan abinda aka min .
dan Allah , ina neman taimako d’aya a wajen ka, ta rik’o hannayan sa duka ta yunk’ura alamun tana son tashi amma ta kasa tashi sai uban jini ne kawai ke fita daga jikinta,.
hannayen damke cikin nasa tace ” ka duba School Bag dina nayi video nayi recording komai, dan girman Allah ka yad’a labari nan karka b’oye shi sannan ta fashe da wani irin matsanancin kuka,me ban tausayi da cin rai numfashinta Na sauka ahankali tace ” ka d’auke ni tamkar k’anwar pls kayi min alk’awarin zakayi min abinda nasaka tallafa kamin gata , ka tona masa asiri, ta yadda mahaifinsa bazai samu nasarar ci zab’en takarar governor daya tsaya ba, pls kayi min alk’awari tana ta maimaita pls kayi min alk’awari zakayi har numashinta ya tsaya cak alamun mutuwa tayi hannunta still damke cikin nasa.
Mutuwar tsaye Abdul yayi ya kasa koda kwakwkwaran motsi balle yayi magana saboda rik’on datayi masa dakyar likitoci suka kwace hannunta daga ‘cikin nasa, shi kansa hawayen tausayin yarinya ke bin kuncinsa yana fitowa daga Emergency yaga iyayenta suna kuka kamar ransu zai fita.
, direct School Bag d’inta ya d’auka ya wuce gida, shi bai ma san me yake yi ba, koda yake tafiya babu abinda yake tunawa sai yarinyar yaddda take kuka
tare da nacewa ka taimake ni kayi min alk’awari zakayi.
Yana k’arasawa gida ya zube agaban mahaifiyar sa, sai daya kusan 30 minutes baice mata komai,ba Mama sai tambayarsa take lafiya, Abdul ?
Meyye faru da kai hk ?
amma ina ya kasa magana sai kuka yake yana tuno da yarinyar da irin illar dakayiwa rayuwa hakika maci amana irinsu basu cancin rayuwa a doron kasa ba .kuka yake sosai har shesheka , sai can iya bud’e baki ya fara magana bai b’oyewa Mama komai ba ya kwashe duk abinda ya faru ya zaiyane mata,d dangane da wannan yarinyar .
sosai Mama ta firgita,d a jin lamarin sai da saita kanta sannan tace ” kai yanzu meye shawararka? Sannan km meyye abinyi Abdul ?
Kallon Mama yayi sosai kana muryarsa cike da kuka yace ” ni bani da wata shawara ko abinyi, Mama ta kalle shi tace ” kamar ya?
“Mama nima ban san me zanyi ba, ban san ya’ya zan taimakawa wannan yarinyar da,akazalinta aka yanke mata farinciki rayuwa ta hanyar yi mata fyade murmushi me cin rai da zuciya Mama tayi tare da cewa ” karkayi haka Abdul ka tuna hannunta cikin naka ta mutu tana zubd hawayen takaicin abinda akayi mata tana k’ara nanata maka kalmar, bata sanka ba amma tasamu yak’i ni akanka harta yarda dakai ta dank’a maka amana, a hafin hannunka ta mutu tana zubar da hawaye, yanzu idan Ramlat akayiwa haka, kuma fa .
Nasan ita bazakace bakasan abinda zakayi ba nasan kana da hujja yadda zakayi, …..da wani irin mugun sauri Abdul ya d’ago kanshi ya xubawa mama idanunshi yana kallonta cike da jin tsoron kalmar data fito bakinta , .