GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

A razane Naseer ya shak’i wuyan Doctor yana cewa “ubanka ne yayi mata ciki?

Dakyar El-Mustapha ya k’ace Doctor daga hannun Naseer, ya kalli Doctor a firgice yace ” wake da cikin Zarah ko Zainab?

A tsorace Doctor yace ” Zarah ce keda cikin 4 months, ai Abban Zarah da Alhaji Abdullahi kasa motsawa sukayi jin maganar da Doctor ke fad’a, a razane Naseer yayi baya had’i da kurma mahaukaciyar k’ara da k’arfi wacce tayi sanadiyyar farkawar Aunty Zainab, cikin kuka ta fara magana ” Zarah kin cuce ni duk irin tarbiyyar danayi muku, da tsarewar danake yi muku, duk abinda kuke so shi nake yi muku dame har namiji zai rud’e ki, yanzu da wanne idan zan kalli Abbanki da mahaifiyarki da k’arasa cikin mahaukacin kuka.

Naseer ma kukan yake yi sosai kamar ransa zai fita, kamar k’aramin yaro, kai Abban Zarah ya dafe had’i da zaman dirshen a k’asa ya kasa cewa komai, El-Mustapha da Momy tsaye sukayi kamar an dasa su, a hankali idan Aunty Zainab ya sauka akan Naseer dake kuka tuburan yana yarfe hannu.

A zuciye ta mik’e ta nufe shi tana tangad’i, cakumar kwalar rigarsa taci cikin matsanancin kuka tace ” Naseer ka cuce ni, ka lalata min abinda na dad’e ina b’oyansa, cak ya tsaida kukansa jin abinda Aunty Zainab ke cewa, da wani irin kallan mamaki yake binta, dukan k’irjinsa ta farayi tana cewa ” Naseer meyasa, meyasa zakayi min haka, akan me, menayi maka, lokacin daka tsaya a gaba na kake min bayanin irin sanda kake yiwa Zarah da irin ingantacciyar kulawar dazaka bata, na yarda da kai sosai da zuciya d’aya, na aminta ko bana raye zaka rik’e min Zarah hannu bibbiyu bisa amana da gaskiya.

” Ashe ba haka bane, na yaudari kai na danayi saurin yarda dakai Naseer, ta k’ara fashewa da matsanancin kuka, idansa Naseer ya runtse da k’arfi yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, k’irjinsa nayi masa wanirin zafi, mak’ogwaronsa yayi masa mugun d’aci, gaba d’aya jikinsa rawa yake yana tsuma, shi kansa yasan babu abinda zai fitar dashi daga zargin yiwa Zarah ciki har sai idan ita Zarah ta farka ta fad’i wanda yayi mata cikin sannan zai fita daga zargi daga wajen kowa dan yasan a halin yanzu bashi da mafita ko abincewa, da gudu Zainab tayi hanyar fita cikin zafin nama Abba ya rik’o ta, kallo d’aya zakayi mata kasan kwata-kwata bata cikin hayyacin ta.

A firgice tace ” Abba ka kyale ni taje wajenta ta fad’a min wani tsinannan ne yayi mata ciki please Abba, tayi magana tana k’ok’arin kwacewa, kanta Abban ya shafa had’i da had’iye abinda yake ji yace ” a’a Zainab ki bari sai kin ji sauk’in jikinki tukunna, “Abba babu abinda yake damuwa na lafiya k’alau, kwanciyar hankali na d’aya ku kai ni wajen Zarah, kanta ya shafa ba tare daya ce komai ba, sai ya lallab’a ta Doctor yasa mata drip da yaya mata allurar bacci.

Ana ranar Dady ya kira Mannir yace duk abinda yake yi ya dawo gida, dan ba lafiya, washe gari jirginsu yayi landing a airport d’in AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT, hankalinsa a tashe yayi gidan inda ya tarar da Ikram kawai, ya tambaye ta abinda ke faruwa, kasancewar batasan abinda k’e faruwa ba tace masa Zarah ce ba lafiya dan iya abinda ta sani kenan, sai da yaje asibiti yaga Zainab ma ba lafiya.

Tunda Naseer ya koma gida ya shige bedroom d’in sa ya rufe yake ta rusa kuka, yak’i bud’ewa yak’i ci yak’i sha babu yadda Dady da Momy basuyi akan ya bud’e k’ofar ba amma yak’i, kuka kawai yake tuburan baji ba gani, babban bak’insa yadda aka lalatawa Zarah rayuwarta.

Duk budurin da akeyi Zarah batasa ni ba, dan bata san wainar da ake toyawa ba.

Sai da su Aunty Zainab sukayi sati d’aya a sabitin sannan aka sallame su, Zarah ta warke sumul babu abinda yake damunta , haka ma Zainab ta warke sai da batayiwa kowa magana tun da abin ya faru burinta kawai taga Zarah.

Suna shiga gidan ita da Mannir suka tarar da Zarah da Ikram a parlor da gudu Zarah ta nufu Aunty Zainab tana” Momy I really misses you so much, Mannir shima dabe san meke faruwa ba yayi tsaye yana murmushi, a zabure Aunty Zainab tayi kan Zarah ta shak’e ta, wani irin mugun duka ta ko’ina ta shiga yi mata tana kuka, da sauri Mannir ya k’arasa inda take ya kwace Zarah.

“Lafiyarki kuwa Zainab kike mata irin wannan dukan me tayi miki?

Cikin kuka tace ” Mannir ka bani ita ta sanar dani uban da yayi mata cikin jikinta, a kid’ime Mannir yace ” what! Ciki Zarahn? “Eh mannir Zarah CIKIN SHEGE TAYI ta d’auko mana magana da abin kunya.

“Kin san abinda kike cewa kuwa?

Jakarta ta bud’e ta ciro d’auko gaba d’aya test d’in asibitin dataje, ta had’a da scanning duka ta mik’a masa hannunsa na rawa ya karb’a ya zauna akan kujera yana dubawa, “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un yake ta maimaitawa bai san sanda takardun suka zube k’asa ba, Zarah da tunda taji maganar ciki jikinta ke kerrrrrrma ta durk’usa had’i da d’aukar takardun tana dubawa, wani irin mahaukacin ihu ta saki had’i da zubewa k’asa a sume, a matuk’ar zuciye Mannir ya mik’e ya zage iyakar k’arfinsa ya shiga kasar mata mahaukatan naushi da duka tako’ina, take ya had’a mahangurb’a, dukan dayake mata ne ya farfad’o da ita daga suman datayi.

Sosai Mannir ke dukan Zarah, amma Zainab na tsaye ko gezau batayi, ita Zarah tama kasa kuka saboda gaba d’aya ba’a cikin hayyacinta take ba, ba zafin dukan tafi ji ba, zafin da zuciyar ta take yi mata shi tafi ji, kanta Mannir ya kama ya gwara da bango wanda sai da yayi sanadiyyar d’aukewa numfashinta.

Fad’uwa a k’asa a sume jini na zuba ta bakinta da hanvinta, fuskarta ta kumbura sumtum, gaba d’aya Mannir ya gaba sab’a mata kamanni, duk da suman datayi amma hakan baisa Mannir tausaya mata ya kyaleta ba, dukan nata yaci gaba dayi kamar mahaukacin zaki, dukan daya sumar da Zarah haka dukan ne ya farfad’o da ita.

Sai ya gaji dan kansa sannan ya kyale ta, anan ta zube tana mayar da numfashi sama-sama saboda wahala ta kasa tashi, jikinta duk a fashe, cikin kuka Ikram tazo ta ja ta bedroom taKaita kan bed ta kwantar ta sata gaba tana kuka.

A hankali Zarah ta d’ago kumburar kanta ta da jajayen idanta ta kalli Ikram dakyar ta iya bud’e bakin tace ” Ikram da gaske ciki ne dani?

Kai Ikram ta d’aga mata hawaye na zubo mata alamar “eh, ido Zarah ta lumshe tana ambaton ” innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, had’i da shafo cikin ta, aiko wutsil taji ya motsa, a hankali ta bud’e idanta tana sauraran yadda Babyn ke motsawa sosai a cikinta, hakan ne ya k’ara tabbatar mata akwai d’a acikin cikinta, ita dai tasan ba’a tab’a samun ciki sai an kwanta da d’a namiji (sex) dan ta karanta a addini da kuma biology, ita kuma a iya saninta babu wani namiji daya tab’a saninta ‘ya mace ko ya kusance ta, balle harta samu ciki, sai dai idan saka mata akayi dan ta tabbatar bata tab’a samun ciki haka nan ba, haka Zarah ya kwana cur bako gyangyad’i balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare, har gari waye, haka ma Aunty Zainab da Mannir babu wanda ya iya runtsa, balle kuma Oga Naseer.

Da sassafe Aunty Zainab ta shiga d’akin Zarah ta tarar da kwance cikin bargo tana ta kakkarwar sanyi, Ikram na gefenta, tsaye tayi a kanta tana kallanta cike da muguwar tsana dan yanzu kwata-kwata bata k’aunar ganin Zarah tace ” Zarah ki sanar dani uban da yayi miki cikin nan, cikin kusa Zarah tace ” wallahi Allah Momy ban san waye ba, nima ganin cikin kawai nayi a jiki na, wasu fitunannun marika ta watsawa Zarah wanda yasata hantsilawa cikin fushi tace ” karki k’ara kirana Momy ni ban haifi MAZINACIYA ba, tsayar da kukanta Zarah tayi ta k’ura mata ido kawai, had’i da maimaita sunan da Momy ta kira ta MAZINACIYA!!! , a hankali tace ” Momy wallahi nima ba mazinaciya bace, na rantse da girman Allah ban tab’a aikata laifin ZINA ba, K’ADDARA TAH ce haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button