GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin zafin rai Aunty Zainab tace “cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad’a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace ” wallahi Aunty ban sani ba, idan za’a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, dakyar Zarah ta yunk’ura ta mik’e, dakyar ta take taka k’afarta, tafiya tayi ta bud’e durowa ta d’auko Qur’an ta d’ora akan ta tace ” na rantse da wanda raina ke hannunsa na rantse da girman Qur’an dake kai na bansan wanda yayi min ciki nan ba, ban kuma tab’a aikata zina ba.

Jikin Aunty Zainab yayi mugu mugun yin sanyi, gaba d’aya jikinta ya saki, zuciyar ta daina yi mata zafi da tafarsa dake ji, tasan Zarah tana da cikekken ilimin addinin islama, tana kuma da nutuwa da hankali tasan bazata tab’a rantse mata da Qur’an akan k’arya ba, a harzuk’u Mannir ya k’arasa shigowa d’akin dan dama yana tsaye yana kallan duk abinda ke faruwa, bai jira wata-wata ba hau dukanta tak’o ina baji ba gani, ya zage yadda zai daki k’aton gardi namiji d’an uwansa yayi ta kai mata naushi da kutufo a ko’ina, cikin rashin imani da tausayawa.

Ya rink’a gwara kanta da bango, yana d’aga ta sama yana jefarwa har sai da ta daina numfashi da motsi amma bai dai na dukanta ba, wata irin razananniyar k’ara Ikram ta fasa had’i da fita da gudu tayi wajen wayar Zarah, da sauri dayi dialing number Naseer, da kamar bazai d’aga sai kuma yayi picking ganin number Zarah ce, a gigice tace ” Uncle kazo da sauri Momy da Dady zasu kashe Zarah, kayi sauri please karta mutu, a gigice ya fito da gudu yayi habar gidan dai-dai lokacin da Momy da Dadynsa ke yin parking sun dawo daga unguwa, ganin yadda Naseer ya fisgi motar a haukace sun san ba lafiya ba, dan haka suka rufa mishi baya.

Yana yin parking bai jira motar ta gama tsayawa ba ya fito yayi cikin gidan a haukace, a gefen motar sa su Dady sukayi parking suma suka fito suka nufi cikin gidan.

Naseer na shiga gidan ya jiyo ihun Ikram a bedroom d’in Zarah a hanzarce ya nufi can ya shaga kai tsaye dai-dai lokacin da Mannir ya shak’eta yana cewa ” mu zaki rainawa hankali, kin tab’a ganin inda akayi cikin haka nan ko a ruwa ake sha, idanuwanta suka firfitu waje gaba d’ayansu suka kakke numfashinta ya tsaya……….

MOMYN ZARAH

[03/02, 20:53] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

49

A haukace Naseer ya k’asa wajen yasa hannu ya fisge Zarah daga hannun Mannir ya kalle shi ido cikin ido yace ” wallahi duk abinda ya same ta bazan tab’a yarda ba sai nayi shari’a dakai, tsabar baka da imani ka zage iya k’arfinka da Allah ya baka a matsayinka na namiji kayiwa mutum wannan mummunan dukan sai kace ka samu dabba.

Murmushi Mannir had’i da cewa ” ai dole kaci haka tunda ka lallab’a ka d’urwa ‘yar mutane ciki, shege munafuki mazinaci, masik’i kawai, abinda dama damai bak’ar zuciya, gadan-gadan Naseer yayi kan Mannir dai-dai lokacin da iyayen nasu ke k’arasowa, tsawa Dady ya dakawa Naseer had’i cewa ” stop! Karka soma ina ruwanka da shiga tsakanin su ba tare ka gansu ba, yayi mata duk abinda zai iya, idan ma kashe ta zayyi gashi nan gata, tunda bashi da hankali yaga idan hukuma zata kyale shi, yayi maganar yana kallan Mannir dake ta faman huci.

Aunty Zainab dake tsaye tunda aka fara abin bata motsa ba sai taga Naseer ya sumgumi Zarah yana niyyar yin waje da ita, da sauri tasha gabansa tana jefansa da kallan tsana tace ” ina kuma zaka kaita? bayan ka riga da ka gama lalata, kallanta yayi ido cikin ido yace ” kamar yayafa?

“Ni zaka kalli ido na kace min kamar yayafa? sau nawa ina kama da ita, a zabure Dady ya juyo yana kallan ta yace ” Zainab mekike kice?

Hawayen fuskarta ta fara sharewa sannan tace ” eh Dady gashi nan ku tambaye shi idan k’arya nake masa, wallahi sau uku ina kamashi yana romancing d’inta, kafin Dady yayi magana Naseer yace ” da kika ganni ina romancing d’inta, kin ganni a kanta ne? ko kuma kin tab’a kamani akan ruwan cikinta ina sex da ita ya fad’a idansa cikin nata, dama Naseer akwai bak’ar zuciya, ganin ransa yayi masifar b’aci kuma sun san idan ransa ya b’aci haka idonsa rufewa yake yana iyayin komai yasa kuwa yin shiru, a hankali ya sunkuya ya sab’i Zarah a kafad’a yayi waje, Dady da Momy suka bi bayansa.

Amma kafin su iske shi ya figi motar a 360, da sauri suka shiga mota suka bi bayansa, a k’ofar wani had’add’e private hospital yayi parking, da hanzarinsa ya fito ya shiga cikin hospital d’in bai jima suka fito da Doctor da nursing, kai tsaye emergency aka wuce da Zarah, tsaye Naseer yayi a k’ofar emergency room d’in yana safa da marwa, a haka su Dady suka k’araso, da sauri suka nufe shi, Dady yace ” ya ake ciki ne?

Naseer ya bud’e baki zayyi magana Doctor ya fito a gigice da sauri Naseer ya tare shi, Doctor yace ” ina mijinta? batare da fargabar komai ba Naseer yace ” nine?

” accident d’in data samu gaskiya ya munana dan harda karaya biyu, a razane Naseer yace ” what!!! KARAYA!!! a d’an tsorace doctor yace ” eh k’afa da hannu, zaman dirshan Naseer yayi a wajen a k’asa ya fasa gigitaccen kuka, Kallan sa Doctor kawai yake yana mamakin namiji kamar Naseer amma da karyayyar.

Ni ko nace hmmmmm Doctor baka san so bane

Sosai zuciyar Dady da Momy ta karaya, a hankali Dady ya cewa Doctor ” kuyi duk abinda ya kamata kawai, ku d’orata, “ok doctor kawai yace ya juya ya koma cikin Emergency room, a hankali Dady ya durk’usa a gaban Naseer ya rungumo shi jikinsa yana lallashi yayinda Momy ke shafa kansa, a zuciyar Dady yana jinjina tsantsan rashin imani irin na Mannir, cikin kuka Naseer yace ” Dady kana jin Doctor ma cewa had’ari ta samu dan shi a tunanin sa accident ne, babu wanda zayyi tsammanin wannan duka ne, Dady Mannir kwata-kwata bashi da imani, baya ganin akwai ciki a jikinta idan wani abu ya same ta fa, wallahi Momy bazan yarda ba sai nayi shari’a dashi kona rama mata, daga Momy har Dady babu wanda yace k’ala.

Wayar Dady ya ciro daga aljihu ya kira Alhaji Abdullahi da Abban Zarah ya sanar dasu halin da ake ciki, basu jima ba suka k’araso tare, cikin mummunan tashin hankali, anan Dadyn Naseer yayi musu bayanin duk abinda ya faru batare daya b’oye musu komai ba, sosai zuciyar Abban Zarah ta sosu, amman ya daure ya b’oye bai bari ko fuskarsa ta nuna ba, balle a gane yaji zafin abin, Alhaji Abdullahi ne ya harzuk’a ya rufe idonsa yayi ta zazzaga ruwan bala’i san ransa.

Sai da akayi a k’alla 5 hrs sannan aka fito da Zarah jiki duk nad’e da bandeji, da hanzari su Naseer suka mik’e suka bayan su, wani shegen d’aki aka kaita mai shegen kyau da k’ayatuwa babu abinda babu harda kitchen da bathroom & toilet, a bakin gadon kusa da ita Naseer ya zauna had’i da k’ura mata ido hawaye na zuba, sosai al’amarin ya bawa duk jama’ar dake wajen tausayi, wajen 11:00pm na dare Dady ya kalli Momy da Naseer yace su fito su tafi, amma bud’ar bakin Naseer yace ” in tafi ina?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button