GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Juyowa Dady yayi yana kallansa dan yasan dama za’a rina, fuska d’aure had’i cewa amma kasan dai bazai yiyu ka kwana nan ba ko? “ni fa Dady babu inda zani nabar Zarah, haba sai kace dai marar gata da galihu bayan wannan mahaucin dukan sannan atafi a barta babu wanda ya lura da halin datake ciki ga ciki a jikinta, a hasale Dady yace ” to idan ma za’ayi jinyar tata kasan dai baka d’aya daga cikin jerin wad’anda suka dace ko?

” please Dady kayi hak’uri amma babu inda zani, babu yadda Dady, Momy, Alhaji Abdullahi da Abban Zarah basuyi akan Naseer ya tashi ya tafi ba amma fafur yak’i ko motsi, dayaga an dame shi ma sai cewa yayi ” wai me kuke gudu ne bayan mai afkuwa ta afku duk abinda kuke tsoran karrya faru ya rigada ya faru, dan ni babu inda zani, sanin Naseer na kafiya tun yana yaro yasa Momy cewa ” shikenan kuje ni zan kwana dasu, sosai Abban Zarah da Alhaji Abdullahi sukaji dad’in karar da Momy tayi, dan haka suka shiga yi musu godiya ” lah bakomai an riga an zama d’aya, Momy tacewa Dady ” ka bawa driver barguna da pillows ya kawo min, Dady yace ” to muje mana ki d’auko duk abinda ya kamata inyaso sai na dawo dake, ba musu ta mik’e tabi bayansa.

Zarah najin k’arar rufe k’ofa ta bud’e idanta dan ta dad’e da farkawa kunya ce kawai ta hana ta bud’e idanta, duk budurin da akayi da Naseer akan kunanta, hawaye na zubo mata ta k’ura masa ido had’i da kiran sunansa a hankali ” Uncle!!, a hanzarce ya juya yana kanta shima hawaye na zubo masa, dakyar ta bud’i baki tace ” wallahi Allah Uncle ban san yadda akayi na samu ciki ba, please ka yarda dani, Allah yadda kuka ga cikin nan a jikina haka nima na ganshi, wallahi Allah Uncle ban tab’a sanin wani d’a namiji ba, ban tab’a aikata zina ba, har rantsewa su Momy da Dady da Qur’an nayi amma sunk’i yarda dani ta fashe da matsanancin kuka.

Shima kukan yake ya kasa cewa komai, “Uncle jibi irin dukan da Dady yayi min, Momy har kira na da MAZINACIYA (My up coming novel) tayi, kowa yak’i ya yarda dani, babu mai yi min uzuri, laifi na kowa yake dabuwa, nasan kai kowa yake zargi amma ni ban tab’a ji a raina ko sau d’aya zakayi min haka ba, na rasa mai yasa kwata-kwata zuciya ta tak’i zarginka, Uncle karka d’ai kawai a rage min a masu so na, na baya dan Allah Uncle karka guje ni, please ka yarda dani wannan ABU A DUHU (Next novel d’ina in sha Allah) yake, daga ni har kai babu wanda yasan MEKE B’OYE (shi kuma upper novel d’ina) har yanzu babu wanda yasan GASKIYAR AL’AMARI (Next upper novel d’ina) balle kuma duniya tasan SIRRIN B’OYE (My new novel).

A hankali yasa hannu yana share mata hawayen dake zubo mata yace ” karki damu Zarah, nima na rasa me yasa har yanzu zuciya tak’i ganin laifinki ko sau d’aya ba, wallahi na yarda dake 100% kuma ina tare dake d’ari bisa d’ari, cikin rawar murya tace ” thank you Uncle, thank you so much, duk duniya a halin yanzu bani da sama dakai, bani da masoyi na gaskiya mai k’aunata tsakani da Allah sama dakai.

Ni ko nace hmmmmm Zarah kenan baki daddara ba kenan har yanzu

Goshinsa ya d’ora akan nata suna kuka babu mai lallashin wani, Momy dake tsaye tana kallansu tun d’azu batare dasun sani ba, ta share hawayenta sai a lokacin ta samu sausauci a zuciyarta, d’an gyaran murya sannan tayi sallama, da sauri Zarah ta rufe idanta.

Cikin tausayawa Momy ta k’arasa inda suke ta zauna a kusa da had’i cewa ” ki bud’e idanki Fatima dan duk naji mai kuka ce, banbi Dady ba ganin dare yayi yace zai bawa driver ya kawo min, dan haka naji maganarki tun daga farko har k’arshe, a hankali Zarah ta bud’e idanta ta sauke su akan Momy yayinda hawaye keta faman ambaliya a fuskarta tace ” wallahi Allah Momy ban san yadda akayi cikin nan ya shiga jikina ba, ban san mafarin abun ba illa BAK’IN GANI (still my novel) danayi, hawayen Momy ta goge mata karki damu Zarah, na yarda dake kuma nayi miki alk’awarin ina tare dake akoyaushe ko’ina, murmushin yak’e wanda yafi kuka ciwo Zarah tayi, Momy tace ” karki sake ki damu karki saka komai a ranki balle ki jawowa kanki ciwo kinji, kiyi hak’uri kowanne d’an Adam da irin k’addararsa, sosai Momy ta kwantarwa da Zarah hankali sannan ta kira doctor ya dubata aka bata magungunanta.

Sannan Momy ta bata light food tad’anci d’an mitsitsi shima ba’a san ranta sai da Momy da Naseer suka matsa mata dakyar taci, , a b’angaren Aunty Zainab kuwa kwata-kwata bata runtsa ba, yadda taga rana haka taga dare dan bacci k’aurace mata yayi, haka ma Mannir dan shi safa da marwa ma yayi tayi a d’akin har gari ya waye.

Washe gari da sassafe Zainab da Mannir, Ikram suka tafi gidan su Momy dan jin yadda Zarah ta kwana, dan ita Zainab tun da Zarah ta rantse mata da Qur’an kwata-kwata ta daina ganin laifinta ta karkata gaba d’aya laifin ta d’orawa Naseer dan tasan idan ba shi babu mai d’urkawa Zarah ciki, shine suke kullum kuma koyaushe, Mannir dai baya nan balle ta zarge shi dan yanzu 4 months 2 weeks kenan baya k’asar.

Suna isa harabar gidan Dady na fitowa d’auke da kwandon breakfast, ya gansu sarai amma ya d’auke kansa ya shiga mota had’i da yiwa driver alamar ya taho, da sauri Mannir ya nufe shi yana yi masa magana amma Dady ko kallan inda suke bayyi ba balle ya amsa masa ya bawa driver umarni daja motar.

Da hanzari Mannir ya koma cikin motar yana yiwa Zainab alama data shiga, ya figi motar ya rufawa Dady baya, acan Dady ya iske Alhaji Abdullahi da Abban Zarah ana ta drama da Naseer ya tafi gida yayi wanka ya shirya ya dawo amman yak’i, su Dady suna gaisawa Mannir da Zainab shigo d’akin, a hasale Naseer ya mik’e zai zuba tijara Dady yayi saurin hanashi, Mannir na niyyar nufar gadan Zarah Dady yayi saurin dakatar dashi ta hanyar d’aga masa hannu, Zainab tsaye tayi k’em ganin mummunan halin da Zarah ke ciki duk jikinta nad’e da bandeji har fuskarta ga k’afarta da hannunta d’aya a sak’ale duk da k’arafa alamar d’ori , sosai Zainab ke kuka cike da tsananin tausayin Zarah.

Mannir yace ” please Dady ka barni na ganta wallahi tun jiya muke neman asubitin da kuke, daga ni har Zainab hankalin mu a matuk’ar tashi yake dukkan mu babu wanda ya runtsa.

A hasale Dady yace ” kuna san nata ne kai da matarka zaku had’a kai kuyi mata wannan mugun dukan da har Doctors suna tsammanin accident ne, babu wanda yayi tunanin wannan duka ne harda karaya biyu.

“Karaya fa Dady Mannir ya fad’a a razane yana zaro ido, ” baka da gani ne ko baka da ido ne ko dazaka shiko part d’in bakaga an saka Orthopedic ba, ” dan Allah kayi hak’uri wallahi ban…. bai kai ga k’arasa maganar ba suka jiyo ihun Naseer, duk suka kalle shi,, da gudu ya nufi gadan Zarah yana kwala mata kira Zarah!!! gaba d’ayan suka kalli wajen, jini ne fitowa Zarah ta baki ta hanci data kunnenta, idanuwanta gaba d’aya sun kakkafe bak’in ya d’auke sai iya farin kawai, jikinta ya sandare, sai kaf-kaf datake kamar mai farfad’iya.

A haukace Naseer ya shiga jijjiga ta yana kiran sunan Doctor da k’arfi duk ya fita daga cikin hayyacinsa, nutsuwarsa ta gushi ihuuuu kawai yake yana kuka, hannunsa Zarah ta rik’o da d’ayan hannunta mai lafiya dakyar tace ” Naseer, yau ne rana ta farko data ambaci real name d’insa a razane ya d’ago yana kallanta ido cikin ido yana kuka kamar ransa zai fita, murmushin k’arfin hali tayi masa tace ” nagode sosai da soyyayyar daka nuna min, dazan rayu dana yi maka….. bata k’arasa ba ta fara aman jini gunduwa-gunduwa dakyar ta tallafo fuskarsa tana murmushi tace ” uncle mutuwa zanyi, please ka daina kuka, na baka amanar Momy na Ikram ka kular min dasu yadda zaka kula da kanka, ka yafewa Dady na please karka rik’e shi a ransa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button