GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannunsa da rik’e tana zabure-zabure can kusan tayi salati jikinsa ya saki……..

MOMYN ZARAH
[03/02, 20:53] Hassan Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

50

Da k’arfi Naseer ya kira sunanta yana jijjiga ta ZARAH!!!!!, a haukace yake kwalawa likita kira iya k’arfinsa yana ihuuuun hauka, a wajen Aunty Zainab ta zube a k’asa akan gwiwoyinta tana hawaye amma ta kasa kukan, a razane Mannir ya fita yana kwalawa Doctor kira a matuk’ar firgice, da sauri Doctor da Nursing suka shigo, gam Naseer ya rik’e tana ihuuu, sai da kyar aka b’amb’are daga jikinta aka shigar da ita emergency.

Shak’ar wuyan Mannir yayi yana ihuuu, kwata-kwata baya cikin hayyacinsa da nutsuwarsa ya gama fita daga hankalinsa, ya shak’e shi iya k’arfinsa yana cewa ” wallahi idan Zarah ta mutu kai ma sai ka bita, matuk’ar ina raye bazan bar makashin Zarah yaci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai dai nima a kashe ni, kakarin mutuwa Mannir ya shigayi yana kokawar kwace kansa amma ya kasa, Dady da Momy na zaune babu wanda yayi yunk’urin komai balle yayi magana, sai Abban Zarah ne yaje yana k’ok’arin kwace shi, amma ina ya kasa, wani gigitaccen mari Abba ya yarfawa Naseer, a kid’ime Naseer ya saki Mannir yayi kan Abban, ganin Abba ne yasa shi sakinsa da sauri yana yarfa hannu.

Ya durk’ushe a wajen yana kukan mutuwa, gaba d’aya wajen kowa tunanin wannan wanne irin ne Naseer yake yiwa Zarah, duk anyi jugum-jugum a k’ofar emergency room d’in, babu mai cewa k’ala, illa Naseer dake ta faman hawaye yana jin zuciyar sa kamar zata buga.

Iya wuya kam Zarah tasha kamar zata mutu dan sai da ta gwammaci mutuwarta akan ci gaba da rayuwarta, su kan su Doctors d’in sai da suka sha bak’ar wahala kafin su samu numfashinta ya dawo dai-dai, su kansu sun tausaya mata ganin irin bak’ar wuyar dataci, sai akayi 3hrs sannan aka fito da ita, da sauri Naseer ya mik’e ya nufi gadan da ake turata a ciki, yana binsu a baya har suka mayar da ita d’akinta, da sauri Naseer ya k’arasa bakin gadon ya zauna ya rik’o hannunta cikin nasa, kowa ya tsaya cak yana kallan ikon Allah, Doctor ya sauke ajiyar zuciya yace ” jininta ne ya hau sosai, kuma tana cikin matsananciyar damuwa ayi k’ok’ari arink’a kwantar mata da hanklinta da zuciyarta nagaf da tab’uwa.

A hankali Zainab taje bakin gadon ta shafa kan Zarah tana hawaye, zuciyarta nayi matuk’ar k’una da tafasa, tana jin k’irjinta kamar zai fashe saboda tsananin zafin dayake yi mata, ita kanta tasan tana tsannin k’aunar Zarah, amma dole tayi nisa da ita, mayar da kallanta tayi wajen Mannir tace ” muje, cikin muryar kuka ta kalli Ikram tace ” ki tsaya kiyi jinyar ‘yar uwarki har ranar za’a sallameta zan sa driver ya kawo miki kayanki da duk abinda kike buk’ata kinji, cikin sanyin jiki Ikram tace ” to Momy, dan tana tsananin san Zarah itama a ranta fiye da tunanin.

Harta kai bakin k’ofa ta juyo ta kuma kallan Ikram tace ” karki anyi haka kice zakiyiwa Zarah wani abu marar kyau, idan har naji kona gani nida kai na zan kashe ki wallahi, dan har yau har gobe Zarah tananan a zuciyata daram kamar da babu abinda ya ragu dan Zarah bata da uwa sama da ni Zainab ta fad’a kallan saitin Naseer, kuma har bada baza’a tab’a canjawa tuwo suna ba, murmushi Ikram tayi tace ” haba Momy yanzu har kina tunanin zan iya yiwa wani abu mummuna, duk duniya fa bani da ‘yar uwa ko d’an uwa kamar ta, tare muka taso kamar twice muka sha nono d’aya, Momy Duk duniya Zarah bata da kamar mu muna bamu da wanda yafita duk wanda yake tak’amar yana santa ko sanin ciwonta a bayan mu yake Momy dan munfi kowa sanin zafinta.

Tun daga ranar Momy, Ikram da Naseer ke jinyar Zarah, sai dai ita Momy bata kwana anan da dare take tafiya tabar Ikram da Naseer su kwana da ita, sai da Dady da Abban Zarah suka matsawa Naseer sannan yake tafiya da safe ya dawo da yamma, amma dole ce ta sashi hakan badan yaso ba, tun daga ranar Zainab bata kuma zuwa ba, sai dai kullum sai ta kira wajen sau 10 ta tambayi jikin Zarah, shiko Mannir dama ya gama course d’in daya kai shi Paris dan haka tunda ya dawo bai koma ba, shi Mannir kullum sai yaje asibitin sau biyu da safe idan ya fito zai tafi office sai biya yaga jikin nata haka ma da daddare, amma ko kallansa Naseer bayayi, har gwara Momy da Dady suna amsa masa gaisuwarsa sama-sama, haka kullum Alhaji Abdullahi da Abban Zarah sai sun zo.

Iya bak’ar wahala kam Zarah na shantashanta dan sau biyu ana fasa kukan mutuwarta, Allah sarki yarinya k’arama amma ta had’u da k’addara mai girman gaske, kullum cikin matsanancin kukan bak’in ciki take da takaicin rayuwarta, duk tayi bak’i ta rame ta lalace kamar ba Zarah ba, kwata-kwata tak’i sausautawa zuciyar ta, Naseer da Ikram na iya bakin k’ok’arin su wajen d’ebe mata kewa da gusar mata da damuwa, yayinda a hankali cikinta keci gaba da girma yana k’ara fituwa kullum yana yawan yi mata motsi wani lokacin ma ko bacci take idan ya motsa sai ta farka.

A haka har akayi wata biyu, jikinta kam yanzu sai dai muce Alhamdulillah, kasancewar akwa ingantacciyar kulawa ta warke, dan har an cire mata d’aurin k’afarta dana hannunta, hannun ya warke sumul sosai, duk inda Mannir yaji mata ciwo ta ya warke babu taso ko d’aya illa k’afarta da har yanzu da saura dan kwata-kwata bata iya taka ta, doctor yace next week za’a fara koya mata tafiya da abin koya tafiya, sab’anin hannun daya warke sosai kamar bata tab’a karyewa a hannun ba dan ko tabo babu babu abinda bata iyawa da hannunta kamar dai yadda ta saba a baya.

Haka ma a b’angaren damuwa ta d’an rage kad’an dan zamu iya cewa ba laifin tunda yanzu tana samu tayi hira dasu Momy, Ikram, musamman kuma Naseer data sawa ranta duk duniya babu mai santa kamar shi, ta rage kukan da take yawan yi sab’anin da, da’indai bacci ba bacci takeyi ba to tana cikin aikin kuka 24hrs, amma yanzu har murmushi take yi sosai.

A hankali jikin Zarah yaci gaba da samun sauk’i sosai, yayinda Naseer ke koya mata tafiya, hankali cikin ikon Allah yanzu tana iya tafiya da sandar ita kad’ai batare da an rik’e ta ba, tana iya yin komai da kanta har zuwa tailed da bathroom tayi wanka ko kashi tayi sallah, yanzu babu abinda akeyi mata da kanta take komai, haka ma abinci tana ci sosai kasancewar cikin jikinta mai sa cin abinci sosai ne, dan yanzu cikin Zarah yana da wata bakwai.

Yau ma kamar kullum Naseer na zaune a gefen Zarah, Momy nakan sallaya, Ikram na kallan wani a MBC Bollywood ta tattara hankalinta gaba d’aya wajen kallanta, Naseer ya kalli Zarah yana murmushi yace ” yanzu kina da 3 months a asibitin nan, gashi doctor yace ” zaki kai har nan da next month, anya bazaki gaji bakuwa, da naso na matsa masa dole sai ya sallame ki, saboda na fuskanci kun k’usa da zaman hospital, martanin murmushin ta mayar masa had’i da cewa ” ku baku gani da d’awainiya dani ba sai ni zan gaji da zaman asibitin, zune ya kamata ku gaji da wahala dani ai, da sauri ya d’ora hannunshi akan lips d’inta had’i cewa ” shhhhhhhhhh karna kuma jin kince muna zamu gaji dake ko muna wahala dake kinji ko?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button