GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai ta d’aga masa alamar eh, cikin sanyi murya tace ” uncle kayi hak’uri idan na b’ata maka ban kumawa, murmushi yayi had’i da jan hancinta yace ” ai baki laifin a wajen Uncle d’inki, dariya tayi tace ” ina godiya Uncle, haka dai sukayi ta hira cikin jin dad’i da annashu yayinda gaba d’aya hankalin Momy na kansu, tana satar kallan su.

BAYAN WATA D’AYA

Kwanci tashi asarar mai rai, rana bata k’arya sai dai uwar d’iya taji kunya, yau watan Zarah hud’u cif-cif a asibiti tana jinya yayinda cikinta ke da wata takwas, ta warke sumul babu abinda yake damunta, ko ciwon kai bata ji, tana cikin k’oshin tafiya sai dai d’an abinda ba’a rasa ba namai juna biyu musamman kuma mai tsohon cikin wata takwas yama shiga wata na tara, lafiya lau take tafiyarta kamar da bata ko d’ingishi, haka jikinta babu tabo ko kwarzane, ta dawo normal kamar da, yadda kasan ba itace tasha jinya har ta wata hud’u ba, cikin ikon Allah Zarah ta dawo kamar da, sai dai har lokacin tana cikin matsanancin bak’in ciki da damuwa gami da takaicin duniya musamman idan ta kalli cikin jikinta ta tuna yau ita ke d’auke da cikin shege kuma cikin shegen ma wanda ba’a san uban sa balle asalinsa ba, sai taji gaba d’aya ta tsani kanta da duniyar gaba d’aya.

Tun tana jin kunya tana b’oye-b’oyen cikin harta gaji ta daina ma, tunda shi ciki d’an duma ne da kansa yake bayyana kansa, ta d’auki damuwar duniya ta d’orawa kanta tayi mugun bak’i ta rame, har zuciyarta ma ta k’ek’ashe ta bushe rak’ayau ta daina kuka sai na zuci dan su kansu hawayen sun bushe, sun k’afe sun gaji da zubowa.

D’aukar da takardar sallama Doctor ya shigo yana fara’a ya mik’awa Naseer yace ” yau dai mun sallamar maka MATARKA mun huta da rigimarka sai kuma an dawo mana haihuwa, dan su ma’aikatan asibitin tsammanin su Naseer mijin Zarah ne, satar kallan Zarah Naseer yayi dan yaga reaction d’inta aka ci sa’a kuwa itama shi take kallo had’i da zaro ida waje kamar zasu fad’i k’asa.

Murmushi Naseer yayi had’i cewa ” ah wallahi kun huta fa, Doctor ya kalli Zara yace ” to maman biyu Allah ya raba lafiya, sai kinzo haihuwa murmushin yak’e Zarah batare datace komai ba, Dady, Momy, Mannir, Alhaji Abdullahi, Abban Zarah, Ikram duk suna wajen, gaba d’aya suka fito wajen harabar motoci Zarah tayi tsaye ta rasa wacce zata shiga dan tana tsoran karta yiwa Naseer laifi, dan tasan halinsa.

Kuma ma bata isa ta nufi motar Mannir batare da izinin Naseer ko Dady ba, su Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suna tsaye suna kallan ikon Allah, suna so suga hukuncin da Dady zai yanke, kallan Zarah Dady yayi yace ” ki shiga motar Naseer, ya kalli Naseer yace ” ka kawo ta gida na, da hanzari Mannir yace ” Dady na d’auka gida zan wuce dasu, wata muguwar harara Dady ya watsawa Mannir data hana shi k’ara cewa komai, da sauri Ikram tace ” Dady nima Zarah zanbi, “ok jeki shiga motar Naseer ku taho tare, cewar Dady yana shiga mota had’i da bawa driver umarnin tafiya.

Sosai hukuncin Dady yayiwa su Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dad’i har ran su, bare kuma oga Naseer da ji yayi kamar Dady ya mallaka masa duniyar gaba d’aya saboda tsananin farin ciki da jin dad’i, Naseer bai wuce dasu Zarah gida kai tsaye ba sai da ya biya dasu yawo sosai dan d’ebewa Zarah kewar zaman datayi a hospital, kuma yasanta da shegen san yawon tsiya, bai mayar dasu gida ba sai dare shima lura da yayi Zarah ta gaji kasancewarta mai tsohon ciki, sun tarar Momy da kanta tayi girki ta shirya dinning batare data saka ‘yan aiki sunyi mata ba, acwarta na tarar Zarah ne, bedroom d’aya Momy ta basu ita da Ikram dan tasan idan aka warewa Zarah bedroom ita kad’ai Naseer damunta zayyi ya hanata sakewa, amma idan yana ganin idan Ikram zai rink’a rage wani abun kodan ita badan su ba, tunda ta lura yana d’an jin kunyar Ikram d’in.

Sai da sukayi wanda da sallah sannan suka fito falo suka tarar da Momy, Naseer, Dady gaba d’aya su ake jira aci abinci Momy tace bamai ci sai Zarah tazo dan ita tayi girkin,cikin shagwab’a Naseer yace ” kai Momy ni da Dady ba duk yunwa muke ji, murmushi tayi had’i da cewa ” to sai ka tashi ai gata nan ta fito, dariya yayi yana kallan Zarah yace ” yau Momy tayi mana horan yunwa saboda ke, ta hana mu cin abinci wai sai kin zo, murmushi kawai tayi batare datace komai ba, Momy tace ” to Bissimillah, gaba d’aya suka nufi dining table, cikin kwanciyar hankali suke cin abincin su yayinda Naseer keta aikin tsokanar Zarah yana janta da hira, tana bashi amsa sama-sama.

Mannir na komawa gida Aunty Zainab ta tare shi da sauri dan ta k’agu taji yadda takaya, murmushi had’i da tallabo fuskarta ya zaunar da ita akan sofa shima ya zauna a kusa da ita, idansa cikin nata yake kallan ta, cikin mutuwar jiki ya girgiza mata kai, da sauri tace ” ban fahimta ba please ka bud’e baki kayi min bayani yadda zan gane, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace ” an sallami Zarah yau daga hospital kuma ta warke sumul kamar bata tab’a yin ciwo ba, da hanzari tace ” tana ina ya ban gan ku tare ba?

Cikin mutuwar jiki yace ” Dady ya hana ta biyo ni, dan ko kallanta bayyi ba balle ya saurari ni, daga nan ya kwashe duk yadda sukayi da Dady ya fad’a mata, a hankali tace ” cikin ya zube ko yana jikinta har yanzu? sai da yayi d’an jimmmmm kafin yace ” Zainab ina cikin zashi, yanan mana a jikinta sai ma girma dayayi sosai, dan ina tunanin ma ta kusa haihuwa, dak’arfi da runtse idanuwanta tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa da k’arfi yayinda k’irjinta yayi mata mugun nauyi, Mannir zai sake magana tayi saurin dakatar dashi ta hanyar d’aga masa hannu.

Ita kanta tasan yanzu kwata-kwata bata k’aunar ganin Zarah, ta rasa meyasa take jin ta tsane ta a ranta, saboda bazata iya ganinta d’auke da cikin shege ba yasa har Zarah ta gama zamanta a hospital bata tab’a zuwa dan zuciyarta bazata iya jurewa hakan ba.

Kullum kuma koyaushe Naseer na tare da Zarah 24hrs yana tare da ita baya matsawa konan dacan musamman ma yanzu da cikinta ya shiga watan haihuwa, dan yanzu jiran haihuwa suke ko yaushe, cikinta ya tsufa sosai ta zama, zama dakyar tashi dakyar, kullum Naseer yana kusa da ita baya matsawa konan da can, dan ko fita zayyi tare dasu yake fita, kuma kullum sai ya raba dare a d’akin su kafin ya tafi, haka da asubar fari yake zuwa duba su, sosai Momy da Dady ke bata kulawa tamkar ‘yar cikin su da suka tsugunna suka haifa, a b’angaren Mannir ma kullum sai yazo gidan sau biyu ganin Zarah, sosai Zarah kejin dad’in zuwansa, dan ta saki jiki dashi sosai kamar da, bata tab’a nuna masa wani abu ko fuska na cewar yayi mata laifi ba, asalima itake bala’in jin kunyar sa, idan bai zo ba har waya take masa ta tambaye dalili.

Kullum yazo sai ta tambaye shi Momyn ta, dan sosai take kewar Zainab, tana san ganinta dan dai babu yadda zatayi ne, tasan duk ranar data furta haka rai ran Naseer da Dady yayi masifar b’aci, sosai take yiwa Mannir kukan tana san ganin Momynta, duk sanda yazo sai rok’e shi akan ya bawa Zainab hak’uri dan tasan har yanzu fishi take da ita, babu yadda Mannir bayyi akan Zainab taje taga Zarah ko sau d’aya ne ba amma tak’i.

Yau ma kamar kullum Mannir ya gama shirinsa tsaf zai je duba Zarah, yazo zai wuce ta parlor Zainab tace ” ina zaka haka kake ta sauri? “zani duba ‘ya ta ne, ga mamakinsa sai yaji tace ” zani da sauri ya kalli inda take, bata saurare shi ba, taje ta sako hijab ta iske shi a parlor tace ” muje ko?, batare daya ce komai ba ya wuce tana binshi a waya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button